Gidan Gallery na Fasahar Zamani, Legas (NGMA)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gidan Gallery na Fasahar Zamani, Legas

Bayanai
Iri art museum (en) Fassara, museum of modern art (en) Fassara da tourist attraction (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Mulki
Hedkwata Lagos
nga.gov.ng

Gidan kayan gargajiya na Fasahar Zamani, Legas (NGMA) babban gidan kayan gargajiya ne a Legas, birni mafi girma a Najeriya. Na nuni ne na dindindin na Gidan kayan gargajiya na Fasaha, wani yanki na ma'aikatar yawon shakatawa, al'adu da wayar da kan jama'a ta Tarayya. Gidan kayan gargajiyan yana cikin gidan wasan kwaikwayo na 'National Arts Theatre, a Entrance B'.[1]

Wuri[gyara sashe | gyara masomin]

Gidan kayan tarihi na fasahar zamani na ƙasa yana kan benaye biyu ne a ƙasan katafaren dakin taro na gidan wasan kwaikwayo na 'National Arts Theatre'. Babban gidan yana da nunin zane-zane na zamani, gami da zane-zane masu launi na 'Bruce Onobrakpeya' da kuma tagulla na (Ben Osawe). Akwai kuma kantin sayar da littattafai da kuma ɗakin karatu.[2]

Gidan Tarihi na Fasahar Zamani, Legas

Nunawa[gyara sashe | gyara masomin]

Sashen Hoton zane-zane ya ƙunshi dukka hotuna na zamani da na farko na fitattu, game da duk shugabannin ƙasa. Ya haɗa da hotunan masu fasaha irin su (Aina Onabolu) (Cif Hubert Ogunde), 'Chinua Achebe' 'Wole Soyinka' da Farfesa Ben Enwonwu. Sashen da ke dauke da ayyukan mashahurai da sauran masu fasahar Najeriya. Wadanda suka hada da aikin Akinola Lasekan da Erhabor Emokpae da Farfesa Solomon Wangboje da Bruce Onobrakpeya da kuma Haig David West da Gani Odutokun.[3]

Sashen sassaƙaƙa na zamani yana gabatar da Najeriya na baya-bayan nan, yana nuna cigaba da siffofi na farko kamar al'adun Nok, to amma yanzu ba al'ada ba ce da kuma halin su. Sauran sassan sun hada da tukwane da zane-zane daga ƙasashen abokantaka, kwatancen kafofin watsa labarai da salo, zanen gilashi da kayan sakawa. Fasahar masaku na zamani ne a Najeriya ta samo asali ne daga al'adun Yarabawa, da Hausawa, Igbo da sauran al'ummomin Najeriya. Hatta fasahar masaku na zamani na iya zana tatsuniyoyi da amfani da alamomin gargajiya da launuka da alamu.[4]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Gidan kayan tarihi na zamani na fasahar zamani na Najeriya

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Welcome". National Gallery of Art. Archived from the original on 2011-05-08. Retrieved 2011-05-22.
  2. "National Gallery of Modern Art Lagos". Nigeria Vacation. Archived from the original on 2010-11-26. Retrieved 2011-05-22.
  3. National Gallery of Modern Art (NGMA), Lagos". Nigeria: National Gallery of Art. Archived from the original on 2011-06-13. Retrieved 2011-05-22.
  4. National Gallery of Modern Art (NGMA), Lagos". Nigeria: National Gallery of Art. Archived from the original on 2011-06-13. Retrieved 2011-05-22.