Chimezie Imo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Chimezie Imo
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 7 ga Janairu, 1992 (32 shekaru)
ƙasa Najeriya
Imo
Karatu
Makaranta Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa
Matakin karatu Digiri
Harsuna Harshen Ibo
Turanci
Sana'a
Sana'a Jarumi, model (en) Fassara, narrator (en) Fassara, mawaƙi da mai tsara fim
Kyaututtuka
IMDb nm8560414

Chimezie Imo ɗan wasan kwaikwayo ne na Najeriya kuma abin koyi. An fi saninsa dalilin irin rawar da ya taka a fina-finan: Nimbe, Kasala da MTV Shuga Naija series.

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Chimezie a ranar 7 ga Janairu, 1992, a jihar Legas, amma ya fito daga ƙaramar hukumar Orsu ta jihar Imo da ke a kudu maso gabashin Najeriya. Yana da shekaru 7, ya kasance cikin ƴan ƙungiyar mawaƙa na cocinsa da ƙungiyoyin wasan kwaikwayo.[1]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Aikin fim da talabijin na Chimezie ya fara ne a cikin shekarar 2014, lokacin da aka naɗa shi a matsayin wanda ya zo na biyu a cikin shirin baiwa na Najeriya, 'The Next Movie Star Reality Show'. Ya fara fitowa wani shirin fim mai suna ‘Learning Curves’ kuma tun daga nan ya fito a wasu shirye-shiryen talabijin kamar ‘Origin’ da kuma wasan barkwanci na ‘90 Gogoro’.

A cikin 2018, Chimezie ya taka rawar a matsayin saurayi mai ruɗewa, yana mai sunkuyar da matsa lamba a Shuga Naija.[2] A wannan shekarar, ya taka rawa cikin ɗaya daga cikin yara maza huɗu a wani wasan barkwanci mai suna Kasala (fim).

A cikin 2019, Chimezie shine wani matashi mai shaye-shayen ƙwayoyi a cikin shirin fim mai suna Nimbe. Ya sami goyon baya dalilin rawar da ya taka a fim ɗin kuma an zaɓe shi acikin jerin wadanda ka iya lashe kyautar; Mafi kyawun ɗan wasan na kyautar Future Awards 2020 da kuma Most Promising Yong Actor a wajen bikin kyautar; Awards Academy Awards (AMAA) 2020.

A cikin 2022, Chimezie ya fito a cikin psychodrama "Choke"[3][4] kuma ya sami yabo saboda aikin da ya yi a ciki a matsayin majinyacin wani mai fama da cutar sikila.[5][6]

A cikin 2023, an zabe shi a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za'a bawa lambar yabo ta Masu Kallon Fina-Finai ta Afirka na kyautar Best Actor in a Leading role for Choke.[7]

Kyaututtuka da zaɓe[gyara sashe | gyara masomin]

Shekara Kyauta Iri Sakamako Madogara
2020 Africa Movie Academy Award Best Promising Young Actor Ayyanawa [8]
2020 Future Awards The Future Awards Africa Prize for Acting Ayyanawa [9]
2023 Africa Magic Viewers Choice Award Best Actor In A Drama Ayyanawa [10]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "INTERVIEW WITH ACTOR CHIMEZIE IMO". thedvfstylecollective. Archived from the original on 21 April 2023. Retrieved 8 December 2018.
  2. "Eight Reasons Why We Love Chimezie Imo". thenet. Retrieved 1 December 2020.
  3. "Chimezie Imo, Kanayo O. Kanayo, Nkem Marchie to star in 'Choke' movie". pulse.ng. Retrieved 5 May 2022.
  4. "Choke: Synopsis, Theatrical Release Date and What We Know So Far". shockng. Retrieved 16 July 2022.
  5. "'Choke' Review: Chimezie Imo Stars in Thought-stirring and Pulsating Psychological Thriller". Whatkeptmeup. Retrieved 10 October 2022.
  6. "Chimezie Imo Discusses His Acting Roots, Importance of Critics and Recent Roles in Gritty 'Afrocity' and "Challenging" 'Choke'". Whatkeptmeup. Retrieved 28 September 2022.
  7. "AMVCA Releases Nomination List For 9th Edition". Daily Trust. Retrieved 17 April 2023.
  8. "'Knuckle City', 'The Milkmaid' lead AMAA 2020 nominations [Full List]". pulse.ng. Retrieved 30 November 2020.
  9. "The Future Awards". thefutureawards. Retrieved 8 November 2020.
  10. "Full List: Here are all our AMVCA 9 Nominees". DSTV. Retrieved 16 April 2023.

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]