DJ AB

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
DJ AB
Kasar asali Nijeriya
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello


Haruna Abdullahi (wanda aka fi sani da DJ AB) mawaƙin gambarar Hausa ne ta zamani ne, dake zaune a jihar Kaduna.

Farkon rayuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifeshi a kabala, cikin garin Kaduna dake jihar jihar Kaduna a watan Disamba na shekarar 1993.28 Years

Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Ya yi makarantar firamare da sakandare a kwalejin gwamnatin tarayya Federal Government College Kaduna da ke Malali a Kaduna, kuma yana kan karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke garin Zariya.

Waka[gyara sashe | Gyara masomin]

Abba yafara wakokin gambarar Hausa ta zamani Hausa HipHop a cikin kungiyarsu ta Yaran North Side kafin ya fara hadin gwuiwa da wasu mawakan na Arewa kamar irin su BOC Madaki, Deezel, Classiq Morell da sauran fitattun mawakan Hausa Hip Hop a Arewacin Nijeriya. Ya haura har wasu jihohin in da ya hada guiwa da wasu mawakan na Nijeriya a kudancin kasar don wakoki daban-daban.[1]

DJ Abba ya yi wakoki masu dimbin yawa da suka yi tashe a fadin Arewacin Nijeriya da ma gefenta a wasu kasashen kamar Nijar, Kamaru da Ghana. Yana da masu saurare da yawa musamman a kafafen Intanet daga kasashen turai da ma Amurika. A shekarar 2019 Mr. Eazi Empawa suka zabe shi cikin mutane 100 da suka can-canci a tallaba masu da kudi ko wanne da dala dubu uku wanda za’ayi amfani da kudin wajen yi ma wa’annan mawaka guda 100 bidiyo a fadin Afrika. [2]

A 2020, Dj Ab, ya hada kai da Deezell, BOC Madaki, Kheengz Su ka sake albam mai suna THE FOUR HORSEMEN ALBUM.[3]

Albam[gyara sashe | Gyara masomin]

S/N Waka Shekara Albam
1 Girma : tare da Deezel da Classiq
2 Ga ni
3 Kumatu
4 Yi Rawa : tare da Young6ix
5 Yar boko
6 Babarsa
7 Totally
8 Gan gan
9 Babban yay
10 My woman
11 Soyayya
12 Su baba ne
13 Tell Me : tare Sals Fateetee
14 A Zuba shi
15 An zo wajen
16 Bomba man
17 Da ban ne

Duba nan[gyara sashe | Gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. "Fitattun mawakan ingausa guda 10". Leadership Hausa. Retrieved 4 May 2019.
  2. "Burina Arewa Ta Shiga Taswirar Duniya A Fagen Waka: Haruna Abdullahi". Muryar Amurka (VOA Hausa). Retrieved 4 May 2019.
  3. zadok, Zoreno (2020-12-27). "ALBUM: THE FOUR HORSEMEN EP – DJ AB x Kheengz x Deezell x B.O.C Madaki". tripplejam.com.