Damilola Adegbite
Damilola Adegbite | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Lagos,, 18 Mayu 1985 (39 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Mazauni | Lagos, |
Harshen uwa | Yarbanci |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Chris Attoh (2015 - 2017) |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Bowen Queen's College, Lagos |
Matakin karatu | Digiri |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da model (en) |
IMDb | nm5270569 |
Damilola Adegbite (an haife ta a Oluwadamilola Adegbite; 18 Mayu, 1985) 'yar wasan kwaikwayo ce ta Nijeriya, Tauraruwa, kuma sananna a shirye-shiryen Talabijin.[1] Ta taka rawa a matsayin Thelema Duke a shirin Tinsel, ta kuma fito a matsayin Kemi Williams a fim din Flower girl.[2] Ta lashe kyautar Gwarzuwar Jaruma (Best Actress) a shirin Talabijin a shekara ta 2011 a gasar Nigerian Entertainment Award.[3]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifeta a garin Surulere, jihar Legas. Ta halarci makarantar Queens College dake Yaba, Legas sannan ta karanci harkokin kasuwanci (Business Administration) a Jami’ar Bowen da ke Iwo, Jihar Osun. Tinsel shine shirinta na farko a wasan kwaikwayo.[4] Ta kuma bayyana a cikin tallan TV da shirye-shiryen da aka gabatar a talabijin.[5]
Rayuwar mutum
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Agusta 2014, Adegbite tayi aure da Chris Attoh, wani dan wasan fim din da ta hadu da shi a fim din Tinsel na opera.[6] A watan Satumba na 2014, ma'auratan sun samu ḱaruwa ɗa namiji Brian.[7] Adegbite da Attoh sun yi aure na sirri a Accra, Ghana a ranar 14 ga Fabrairu, 2015.[8] A watan Satumba na 2017, labari ya bazu cewa auren Adegbite da mijinta Chris Attoh ya lalace. Adegbite ta haifar da yaduwar jita-jitan bayan ta goge sunan Chris Attoh daga jikin sunanta a asusun ta na sada zumunta. Sannan ta dena biy-biyanshi a shafinta na Instagram, ta goge duk hotunan sa daga asusun ta na sada zumunta.[9] Sa’o’i bayan haka, a zantawa da akayi da Chris Attoh ya tabbatar da cewa aurensa da Damilola Adegbite ya mutu.[10][11]
Fim
[gyara sashe | gyara masomin]Fina-finai
[gyara sashe | gyara masomin]- 6 hours to Christmas (2010)
- Flower Girl (2013)
- The missing a (2017) a matsayin Alero
- Heaven's Hell (2015)
- Isoken (2017)
- Banana Island Ghost (2017)
- Bace (2017)
- From Lagos with Love (2018) a matsayin Samantha
- Merry Men: The real Yoruba Demons (2018) a matsayin Dera Chukwu
- Merry Men: The real Yoruba Demons (2019) a matsayin Dera Chukwu
- Coming from Insanity (2019)
- Cross roads Siwoku (2020)[12]
Shirin Talabijan
[gyara sashe | gyara masomin]- Kafin 30 (2015 – present) a matsayin Temilola Coker
- Tinsel (2008–2012) a matsayin Telema Duke[13]
Gidan wasan kwaikwayo
[gyara sashe | gyara masomin]- V Monologues
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.pmnewsnigeria.com/2020/01/31/lolo-1-produces-new-movie-when-love-is-not-enough/
- ↑ https://uzomediangr.com/tag/banana-island-ghost[permanent dead link]
- ↑ Yemisi Suleiman (February 12, 2013). "Why I left Tinsel". Vanguard News. Retrieved November 14, 2021.
- ↑ https://web.archive.org/web/20170926041245/http://www.lailasblog.com/damilola-adegbite-removes-husbands-name-from-ig-deletes-all-photos-with-him/
- ↑ VMZ Interviews Damilola Adegbite". November 13, 2012. Archived from the original on 23 February 2014. Retrieved 14 November 2021."
- ↑ "PHOTOS: How Chris Attoh Proposed To Damilola On A Yacht". Peace FM Online. 12 August 2014. Archived from the original on 14 August 2014. Retrieved 14 November 2021.
- ↑ "Aww…Chris Attoh and Damilola Adegbite Christen Their New Son Brian". bellanaija. 23 November 2014. Retrieved 14 November 2021.
- ↑ "Chris Attoh & Damilola Adegbite's Val's Day Wedding". Channels Television. 16 February 2015. Retrieved 14 November 2021.
- ↑ "Damilola Adegbite removes husband's name, unfollows him, and deletes all his photos from IG". Laila's Blog. 25 September 2017. Archived from the original on 26 September 2017. Retrieved 14 November 2021.
- ↑ "Exclusive: Chris Attoh opens up to BellaNaija about New Projects, Divorce from Damilola Adegbite & 'The Kindness Foundation'". bellanaija. 25 September 2017. Retrieved 14 November 2021.
- ↑ https://www.bellanaija.com/2017/09/exclusive-chris-attoh-divorce-damilola-adegbite-kindness-foundation/
- ↑ https://www.sunnewsonline.com/life-as-a-single-mother-of-four-omotunde-david-lolo-1-broadcaster/
- ↑ http://www.channelstv.com/2015/02/16/chris-attoh-damilola-adegbites-vals-day-wedding/
Hanyoyin haɗin waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Damilola Adegbite on IMDb