Jump to content

Danladi Mohammed

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Danladi Mohammed
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Hon-Danladi Mohammed yana gabatar da jawabi a Jami'ar Jihar Bowie- 2014-06-08 17-57

Hon. Danladi Mohammed shine kwamishinan tsare-tsaren tattalin arziki na jihar Gombe ta Najeriya .

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Danladi Mohammed da ga Muhammad Pantami da Amina Pantami a ranar 29 ga watan Satumba shekara ta alif ɗari tara da sittin da takwas (1968). Ya fara karatun sa a makarantar firamare ta Jan-Kai da ke jihar Gombe. Ya sami digiri a kan ilimin tattalin arziki a Jami'ar Maiduguri. Ya sami MBA a harkar kudi, daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa. Ya kuma halarci kwas a kan nazarin siyasa da aiwatar da manufofi a cikin shekara ta 2011 a Global Training Consultation London, an gudanar da jagoranci a cikin shekara ta 2014 a Howard, Washington, DC, Amurka, da kuma kwas ɗin kan kasafin kuɗi don samar da daidaito tsakanin maza da mata a Jami'ar Jihar Bowie a cikin shekara ta 2014.

Hanyoyin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]