Jump to content

Fatima bint Asad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fatima bint Asad
Rayuwa
Haihuwa Hijaz, 568
Mutuwa Madinah, 625 (Gregorian)
Makwanci Madinah
Ƴan uwa
Mahaifi Asad ibn Hashim
Mahaifiya Fatima bint Qays
Abokiyar zama Abu Talib ibn ‘Abd al-Muttalib (en) Fassara
Yara
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a

Fatima Bin Asad bin Hashim Bint Abd Manāf (Da Larabci: فاطمة بنت أسد بن هاشم بن عبدمناف ) Ita ce mahaifiyar Imam 'Ali (AS) kuma matar Abu Talib. Fatima Bin Asad ita ce mace ta biyu, da ta musulunta. Akwai ruwayoyi daga Annabi (SAW) ga me da ita wadanda su ke nuna girman matsayin ta, Fatima Bin Asad. Kabarinta ya na cikin maƙabartar Baƙi'.

Fatima Bint Asad Ƴar ƙabilar Bani Hashim ce. Masana tarihin rayuwarta sun rubuta zuriyarta a matsayin Fatima Bint Asad Bn Hashim Bn Abd Manaf. Ta girma a Makka kuma ta auri Abu Talib. Bayan bayyanar Musulunci ta yi hijira zuwa Madina, in da ta rasu. ita ce mace Bahashimiya ta farko da ɗanta ya zama halifan musulmi.

Wasu Ruwayoyi da hadisai da dama da ba su da inganci sun nuna cewa Fatima Bint Asad ba ta musulunta ba a lokacin rayuwarta, Yawancin Ruwayoyin Tarihin Musulunci sun yi watsi da Wannan da'awar.  ta musulunta a Makka, sannan ta yi hijira zuwa Madina.

Fatima Bin Asad ita ce mahaifiyar ƴaƴ takwas: Talib, 'Aƙil, Ja'afar, 'Ali (AS), Hind (Ko Umm Hani ), Jumana, Rayta (Ko Umm Talib), da Asma'. Sai kuma Muhammad (SAWW) Ɗanta da ta karɓa.

Kula da Annabi Muhammad (SAWW)

[gyara sashe | gyara masomin]

Sakamakon rasuwar mahaifinsa da mahaifiyarsa da kakansa da suka yi a jere, Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam Ya koma gidan Abu Talib (Baffansa) yana da shekara takwas. Fatima Bin Asad kasancewarsa matar Abu Talib ta taka muhimmiyar rawa wajen kula da shi.

Soyayyarta ga Manzon Allah (SAWW) A bayyane ta ke daga yadda ya yi a lokacin rasuwarta: Yace “Yau mahaifiyata ta rasu”, Sannan ya lulluɓe ta cikin rigarsa ya kwanta a cikin kabarinta (ya yi mata addu'a).

Ita ce Kaɗai ce macen da ta haihu a cikin Ka'aba. Yayin da Fatima ta ji zafin naƙudar haihuwar Ali (AS) sai ta shaida wa Allah a bayan Ka’aba tare da addu’ar samun sauƙi. Nan take bangon ɗakin Ka’aba ya Buɗe a gabanta, ta shiga harabarta. Da shigarta sai Ka'aba ta sake rufewa cikin mu'ujiza. Ta zauna a ciki na tsawon kwanaki uku a rana ta huɗu (13 Ga Watan Rajab shekara talatin bayan shekarar giwaye /600 miladiyya) sai bango ya bude mata, ta fito ɗauke da jaririnta Ali (AS) a hannunta.

Haihuwa Imam Ali (AS) a ɗakin Allah al’amari ne da kusan dukkan malaman Musulunci sun ruwaito shi da kuma tabbatar da ingancinsa, in banda Ƴan tsiraru daga cikinsu masu ƙoƙarin kore duk wata falala da darajan Amirul Muminin (AS) da kuma Ahlul-bayt (AS).

Ita ce mutum ta goma sha ɗaya kuma mace ta biyu (Ta farko ita ce Khadija (AS) da ta musulunta.

An ce Fatima bn Asad ta rasu a shekara ta 4/625-6 a Madina

Bayan rasuwarta, Manzon Allah (SAWW) ya lulluɓe ta cikin rigarsa ya ce: " Jibrilu ya ba ni labari cewa ita daga mutanen Aljanna ce, sai Allah ya umarci mala'iku dubu saba'in da su yi addu'a a jikinta". Sannan ya karanta mata sallar jana'iza, ya kuma halarci jana'izarta har suka isa maƙabartar Baƙi'. Manzon Allah (SAWW) ya shiga kabarinsa ya kwanta a cikinsa, sannan ya miƙe ya rike gawarta ya kwantar da ita a cikin kabari.

Fadin Muhammad (SAWW) dangane da Fatima Bint Asad:

"Allah ya jiƙanki mai daraja, kin kasance a gareni kamar mahaifiyata, kin ciyar da ni a lokacin da ke da kanki ki ke jin yunwa, burinki na yin haka shi ne don faranta wa Allah da ayyukanki." Yakan ce: Ni maraya ce ta sanya ni Ɗan ta, ita ce mafi alheri a gare ni bayan Abu Talib.

"Ya Allah! Rayuwa da mutuwa a hannunka su ke, kai kadai ba za ka mutu ba, ka albarkaci mahaifiyata Fatima bint Asad, ka ba ta wani gida a cikin Aljannah, Kai ne Mai rahama."

Uwata Allah Ya kiyaye ki a karƙashinsa, sau tari kina barin kanki da yunwa don ciyar da ni da kyau, kin ciyar da ni, kin kuma tufatar da ni da kayan masu kyau da kika yi ki kanki, tabbas Allah zai ji daɗi da waɗannan ayyukan naki. Kuma Lallai an yi nufin ku ne don samun yardar Allah da rabauta a Lahira. "Ta san ƴaƴanta su na jin yunwa amma ta tabbatar da na ci abinci, ba za ta tsefe gashin ta ba sai ta shafa mai a kai ta tsefe min gashi".