George Akume

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
George Akume
Minister of Special Duties and Inter-Governmental Affairs (en) Fassara

23 ga Yuli, 2019 - 29 Mayu 2023
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 - 29 Mayu 2019
District: Benue North-West
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: Benue North-West
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
Gwamnan jahar benue

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Dominic Oneya - Gabriel Suswam
Rayuwa
Haihuwa 27 Disamba 1953 (70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Tiv
Harshen uwa Harshen Tiv
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Harsuna Turanci
Harshen Tiv
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Peoples Democratic Party

George Akume (An haife shi ne a ranar 27 ga watan Disamban shekara ta 1953), ya kasance ɗan siyasan Nijeriya ne, wanda ke Minista na Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati. Ya kasance Sanata na Tarayyar Najeriya. Ya kasance Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa daga watan Yuni shekarata 2011 zuwa watan Yuni shekarata 2015. Ya kuma kasance Gwamnan Jihar Benuwai daga 29 ga watan Mayu a shekara ta 1999 zuwa 29 ga watan Mayu a shekara ta 2007. Shi ne Gwamna na farko a Jihar Benuwai da ya kammala wa’adin mulki biyu. An zabe shi gwamnan jihar Benuwai a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sannan kuma aka zabe shi ya zama dan majalisar dattawa.[1]

An sake zabar Akume a matsayin Sanata mai wakiltar Benuwe ta Arewa Maso Yamma na zaben Afrilu na shekarata 2011, a karkashin inuwar jam’iyyar 'Action Congress of Nigeria' (ACN). Ya sake cin zabe a shekarata 2015 amma ya sha kaye a hannun Sanata Orke Jev na PDP a shekarata 2019. A ranar 23 ga watan Yulin, a shekarata 2019, Shugaba Buhari ya zabi Akume ya zama minista.[2]

Bayan Fage[gyara sashe | gyara masomin]

Akume ya samu digiri na farko a fannin ilimin zamantakewar dan Adam da kuma digiri na biyu a kan Harkokin Kwadago daga Jami’ar Ibadan. Yanzu yana zaune ne a Abuja, Nijeriya.[3]

Harkar siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 1999, ya zama gwamnan jihar Benuwai kuma ya yi wa'adi biyu na shekaru hurhudu. Ya ci zabe don wakiltar mutanen Benuwai a matsayin Sanata mai wakiltar Benuwai ta Arewa Maso Yamma a Majalisar Dattijan Najeriya. An sake zabar Akume a matsayin Sanata mai wakiltar Binuwai ta Arewa Maso Yamma a zaben watan Afrilun a shekarata 2011, yana kan kujerar Action Congress of Nigeria (ACN) Ya samu kuri’u 261,726, ya doke Terngu Tsegba na PDP wanda ya samu kuri’u 143,354. An sake zabarsa a majalisar dattijai karkashin inuwar jam'iyyar 'All Progressives Congress' (APC) a shekarata 2015. Ya kasance shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan sojoji kuma babban dan majalisar dattijai. An gabatar da shi kuma ya tabbatar da Ministan Tarayyar Najeriya ta Muhammadu Buhari.[4][5]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Jerin gwamnonin jihar Benuwe

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.nigeriainfo.fm/news/homepagelagos/tinubu-swears-in-george-akume-as-sgf/
  2. https://www.vanguardngr.com/2022/02/apc-national-convention-ive-no-running-battle-with-efcc-says-sen-akume/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-12-19. Retrieved 2023-10-03.
  4. https://web.archive.org/web/20160303202454/http://www.nassnig.org/senate/member.php?senator=36&page=1&state=9
  5. https://web.archive.org/web/20110502015602/http://www.thenationonlineng.net/2011/index.php/news/4383-benue-youths-protest-governorship-poll-result.html