Jump to content

Haɗin kai na Duniya don Ilimi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Haɗin kai na Duniya don Ilimi (Global Partnership for Education) haɗin gwiwa ne na masu ruwa da tsaki wanda ke nufin ƙarfafa ilimi a faɗin duniya.[1]  Wanda Babban Bankin Duniya ya shirya shi,[2]GPE ita ce haɗin gwiwa ɗaya tilo na duniya da aka keɓe don ba da tallafin ilimi a cikin ƙasashe masu tasowa.[3]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An ƙaddamar da haɗin gwiwa a shekara ta 2002, Haɗin kai na Duniya don Ilimi.  An ƙaddamar da shi don haɓaka ci na ilimin firamare na duniya. A cikin 2013, Alice P. Albright ta shiga a matsayin mai gudanarwa, wanda kuma Julia Gillard, tsohuwar Firayim Ministan ƙasar Australiya, aka naɗa ta a matsayin shugabar Hukumar GPE.[4] A cikin 2016, Rihanna  ta zama Jakadiya ta farko na hukuman GPE.[5] 

Membobin ƙungiya[gyara sashe | gyara masomin]

Ƙasashen da ke cikin wannan shirin sun haɗa da Afghanistan, Albaniya, Aljeriya, Angola, Bangladesh, Belize, Benin, Bhutan, Boliviya, Burkina Faso, Burundi, Cabo Verde, Cambodiya, Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Chadi, Comoros, Kongo, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, Cote d'Ivoire, Djibouti, Dominika, Masar, El Salvador, Eritriya, Eswatini, Habasha, Fiji, Gambiya, Georgiya, Ghana, Grenada, Guatemala, Guinea, Guinea-Bissau, Guyana, Haiti, Honduras, India, Indonesia, Jordan, Kenya, Kiribati, Jamhuriyar Kyrgyzstan, Lao PDR, Lebanon, Lesotho, Laberiya, Madagascar, Malawi, Maldives, Mali, Marshall Islands, Mauritania, FS Micronesia, Moldova, Mongoliya, Moroko, Mozambique, Myanmar, Nepal, Nicaragua, Niger, Nijeriya, Pakistan, Papua New Guinea, Philippines, Rwanda, Saint Lucia, Saint Vincent da Grenadines, Samoa, Sao Tome and Principe, Senegal, Saliyo, Solomon Islands, Somalia, Sudan ta Kudu, Sri Lanka, Sudan, Syria, Tajikistan, Tanzania, Timor-Leste, Togo, Tonga, Tunisiya, Tuvalu, Uganda, Ukraine, Uzbekistan, Vanuatu, Vietnam, West Bank da Gaza, Yemen, Zambiya, da Zimbabwe.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]