Hamza Abu Faris
Hamza Abu Faris | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Msallata, 13 ga Janairu, 1946 (78 shekaru) |
ƙasa | Libya |
Karatu | |
Makaranta |
University of Libya (en) Ez-Zitouna University (en) Jami'ar Tripoli |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Employers | Jami'ar Benghazi |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | no value |
Hamza Abu Faris ,(Larabci: حمزة أبوفارس), malami ne kuma ɗan siyasa ɗan ƙasar Libya 'wanda aka haife shi a Msallata a ranar 13 ga watan Janairu ,1946.[1] Abdurrahim El-Keib ,ne aka naɗa shi Awqaf & Islamic Affairs ,Minister a ranar 22 ga watan Nuwamba 2011.[2]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An baiwa Hamza Abu Faris takardar shedar koyarwa a harshen Larabci da koyar da addini daga birnin Tripoli a shekarar 1967. A cikin shekarar 1971 ya sami takardar shaidar sakandare a Sashen Adabi sannan ya ci gaba da karatu a Kwalejin Malamai da Ilimi mai zurfi a Tripoli.[3]
Abu Faris ya samu digirinsa na farko a fannin Harshen Faransanci da adabi bayan ya yi karatu a Sashen Harsuna.
Ya yi karatun digirinsa na biyu a jami'ar Al Fateh a fannin ilimin addinin musulunci ƙarƙashin kulawar Dr. Abd'al-Salaam Abu Naji a shekarar 1984.
A shekara ta 2000 Hamza Abu Faris ya sami digirin digirgir (Ph.D) a fannin Kimiyyar Musulunci, tare da ba da fifiko a fannin Fiqhu (Comparative Fiqh) daga Jami'ar Zaytuna da ke Tunisiya; Kundin karatunsa na digirin digirgir yana da taken "Alkali Abdul Wahab al-Baghdadi da tsarinsa na tafsirin sakon manzon Allah."[4]
Horon Addini
[gyara sashe | gyara masomin]Dangantakar Hamza Abu Faris da ilimin Shari’a (ilimi da horar da hadisai na shari’a) ta fara ne, a hannun Shaikh wani kauye; ya kammala haddar Alkur'ani a shekarar 1982.
Musamman:
- Fikihun Malikiyya daga shahararrun ayyukan (al Malik).
- Tauhid (ka'idar kadaita Allah)
- Ilimin Hadisi (hadisai dangane da rayuwar Annabi Muhammad)
- Tafsirin Alqur'ani
- Muwatta (nassi na asali a mazhabar Malikiyya na fikihu)
- tafsirinsa al-Zurqani
- Sahihul Bukhari (Hadisin Hadisai)
- Sahih Muslim (Tarin Hadithin Canonical)
Kwarewa ta musamman a fagen gado da ilimin fikihu.
Aikin koyarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Hamza Abu Faris ya koyar a matakin sakandire na shekaru da dama kafin ya koyar a tsangayar shari'a a jami'ar Benghazi daga baya kuma ya karantar a bangaren shari'a na jami'ar Nasser ta Tarhuna. Daga baya an naɗa Abu Faris a bangaren shari'a a jami'ar Al Fateh dake birnin Tripoli.
Sauran Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Ya yi aiki a matsayin mai bincike na Majalisar Fiqhu na Kungiyar Ƙasashen Musulmi a Makka da Majalisar Fatawa da Bincike ta Turai.
Ya halarci wani shirin talabijin mai suna Musulunci da salon rayuwa a gidan talabijin na Libya, wanda ake watsa shi kai tsaye a ranakun Juma'a da Asabar.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Abu Faris, Hamza. "Hamza Abu Faris' Official CV". Archived from the original on 26 April 2012. Retrieved 12 December 2011.
- ↑ "Libya's NTC unveils new government line-up". Reuters. 22 November 2011. Retrieved 23 November 2011.
- ↑ "Libya's NTC unveils new government line-up". Reuters. 22 November 2011. Retrieved 23 November 2011.
- ↑ Abu Faris, Hamza. "Hamza Abu Faris' Official CV". Archived from the original on 26 April 2012. Retrieved 12 December 2011.