Jump to content

Hari a Ma'aikatar DSS, Abuja

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHari a Ma'aikatar DSS, Abuja
Iri aukuwa
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 31 ga Maris, 2014
Wuri Abuja
Adadin waɗanda suka rasu 21
Adadin waɗanda suka samu raunuka 2
maganar Boko haram

Hari a Abuja dai, wani harin ta'addanci ne da ƙungiyar Boko Haram ta hada kai ta kai a ma'aikatar tsaron kasar ta Abuja a ranar 31 ga watan Maris, 2014 a ƙoƙarin su na tserewa daga inda ake tsare dasu.[1] Hakan ya yi sanadiyar mutuwar maharan 21 da suka yi yunƙurin tserewa inda jami'an tsaro 2 suka samu munanan raunuka.[2]

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 31 ga Maris, 2014 da safe, lokacin da ɗaya daga cikin Jami'in tsaro na ma'aikatar ake zargin ya je gidan yarin don yin karin kumallo.[3] A ƙoƙarinsa na komawa ofishin sa, ɗaya daga cikin ƴan ta’addan ne ya kwace masa makami, inda ya buge shi a kai duk da hannunsa a ɗaure yake-(hannun akwai ankwa) a ƙoƙarinsa na tserewa.[4] Wannan lamari ya jawo hankalin masu gadin da ke ɗauke da makamai da suka yi harbi a sama, don dakatar da su.[2] Wannan yunƙuri ya ci tura har sai da jami'an soji suka shigo domin murƙushe tashe tashen hankula.[5] Fursunoni 21 ne sojoji suka kashe sannan wasu jami’an gwamnati biyu sun samu munanan raunuka.[6]

Bayan harin, an yi ta cece-kuce kan mutuwar fursunonin 21 da suka mutu a yayin harin,[7] saboda wataƙila sojojin da suka yi musu lakabi/suna da ƴan Boko Haram sun kashe wasu fursunonin da ba su ji ba ba su gani ba.[8] Wannan zato ya samo asali ne daga wasu wallafe-wallafen jaridar New York Times na rahoton ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta duniya, wanda ta yi zargin cewa an kashe mutane kusan 600 ba tare da suna riƙe da makami ba,[9] a lokacin da aka sake kama waɗanda suka tsere a baya lokacin da ƴan ƙungiyar Boko Haram suka kai hari a barikin sojoji na Giwa a Maiduguri.[10] Rahoton na Amnesty International ya samo asali ne daga wani shaidar gani da ido na kisan da sojojin Najeriya suka yi wa fursunonin da ƴan ƙungiyar mayaƙan Boko Haram suka sako waɗanda ba su ji ba ba su gani ba a harin da suka kai barikin sojin na Giwa.[11] Wani ganau ya ce: “Tsoffin wadanda ake tsare da su suna cikin aji. Sai suka fara kururuwa 'mu ba Boko Haram ba ne. Mu tsararru ne!' Ni da makwabta mun ga sojoji sun kwashe mutanen zuwa wani wuri da ake kira (‘no man's land,’ ) a bayan jami’ar Maiduguri. Mun kalli yadda sojoji suka buɗe wuta inda suka kashe mutane 56. An kashe su a gabanmu. Dukkansu", in ji jaridar New York Times.[12]

  1. "DSS foils attempted jail break at its headquarter in Abuja". Vanguard News. 20 February 2016. Retrieved 20 February 2016.
  2. 2.0 2.1 "Abuja Boko Haram Jailbreak: SSS Confirms 21 Casualties". Sahara Reporters. Retrieved 20 February 2016.
  3. "DSS foils attempted jail break at its headquarter in Abuja". Vanguard News. 20 February 2016. Retrieved 20 February 2016.
  4. "20 Boko Haram suspects killed in Abuja DSS attack". Vanguard News. 20 February 2016. Retrieved 20 February 2016.
  5. "21 die in Abuja attempted jailbreak - DSS". Nigeria. Retrieved 20 February 2016.
  6. Mikail Mumuni; Cyril Mbah; Kola Olawoyin. "21 die as SSS foils Boko Haram Abuja jailbreak". Newswatch Times. Archived from the original on 3 March 2016. Retrieved 20 February 2016.
  7. "Boko Haram Giwa barracks attack: Nigerian army 'killed hundreds'". BBC News. Retrieved 20 February 2016.
  8. "Amnesty International Accuses Nigerian Military of Committing War Crimes, Claims Videos Show Abuses (GRAPHIC VIDEO)". HuffPost. 5 August 2014. Archived from the original on 28 December 2014. Retrieved 20 February 2016.
  9. "Abuja DSS Jailbreak: The Truth Behind It Exposed By New York Times". OsunDefender. Archived from the original on 28 December 2014. Retrieved 20 February 2016.
  10. "Amnesty International: 1,500 Nigerians Killed in Boko Haram Violence in 2014". VOA. Retrieved 20 February 2016.
  11. Jack Moore. "Nigeria Army 'Killed Hundreds' After Boko Haram Barracks Attack - Amnesty International". International Business Times UK. Retrieved 20 February 2016.
  12. "16 men arrested by Nigeria soldiers 'found dead with bullet wounds'". Times LIVE. Agence France-Presse. Retrieved 20 February 2016.