Jump to content

Harin bam akan masu taron Mauludi a Kaduna

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHarin bam akan masu taron Mauludi a Kaduna
Iri bombardment (en) Fassara
attack (en) Fassara
incident (en) Fassara
aukuwa
Kwanan watan 3 Disamba 2023
Wuri Jihar Kaduna
Adadin waɗanda suka rasu 85
Adadin waɗanda suka samu raunuka 30

Harin Bam ɗin da aka kai da jirgi maras matuki [1] ya faru a daren ranar 3 ga watan Disamban shekarar 2023, inda rahotanni farko suka tabbatar da rasa rayukan mahalarta maulidin su 30,[2][3][4], amman daga baya hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar farar hula aƙalla 85[5][6][7][8] sakamakon jefa musu bam da ake zargin sojojin Najeriya da yi. An kai waɗanda suka jikkata a asibitin garin Buruku

Rundunar sojin saman Najeriya ta yi martani game da zargin harin bam kan masu Maulidi. Inda ta ce wannan labarin kanzon kurege ne babu inda su ka harba bam cikin kuskure kan masu Maulidin.[9] Rundunar sun kara da cewar, ba rundunar sojin saman ce kaɗai take kai hari da jirage marasa matuka ba a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya[10][11]

Sai de daga baya rundunar sojin ta ɗauki alhakin kai harin.[12][13][14][15]

Kafin nan[gyara sashe | gyara masomin]

Mutane na gudanar da maulidin a garin TUDUN-BIRI dake karamar hukumar Igabi, Jihar Kaduna.

Ya ce suna Mauludin-ne da sunan makarantar Madrasatul Madinatul Ahbab wa Talamiz da ke Ugara.

Duk shekara sukan yi wannan taron Mauludi, kuma ko a kwanan baya sun yi wani makamancinsa, amma suka sake tsara gudanar da wani a daren Litinin din jiya.

Harin[gyara sashe | gyara masomin]

A cewar wani ganau da BBC Hausa ta bayar da rahoto Jirgin ya yi ta shawagi a kan mahalarta Mauludin kafin ya jefa musu bam a karon farko da misalin karfe 10 na dare.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar luguden bam din a kan "mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba". Ta kuma bayyana shi da cewa abin takaici ne matuka.[16]

Cikin wanda lamarin ya rutsa da su akwai mata da kananan yara har ma da jarirai.

Martani[gyara sashe | gyara masomin]

Rundunar sojin Sama[gyara sashe | gyara masomin]

Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce akwai bukatar a san cewa ba ita kadai ke amfani da jiragen yaki a Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba.[17]

Alhakin kai harin[gyara sashe | gyara masomin]

Daga baya rundunar sojin Najeriya ta ce ita ce ta kai harin bam da aka kai kan mutanen ƙauyen a yayin bikin Maulud Nabiy a Tudun Biriin da ke karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.[15][13][12]

Rundunar sojin ta ƙara da cewar harin da aka kai ta sama ba bisa ka'ida ba ne, inda ta ce jami'an na kai hare-haren ne kan 'yan ta'adda.[14]

Shugaban ƙasa[gyara sashe | gyara masomin]

Shugaba, Bola Tinubu [7] da Gamnan Jihar Kaduna Uba Sani[18][19] sun bayar da umarni ayi bincike akan lamarin.

Wai-wa-ye[gyara sashe | gyara masomin]

Iri-iren waɗanda hare-haren sun faru a Najeriya, inda akasari ake alaƙanta hakan da rashin sanin makamar aiki gami da rashin hukunta masu laifi a lamarin. Kungiyoyi da dama, ciki har da; Jama’atu Nasril Islam, da Ƙungiyar Dattawan Arewa-(NEF), sunyi kira ayi sahihin bincike game da wannan hari.[20][21]

Ko a shekara ta 2017 an kai makamancin wannan hari a garin Rann, da rundunar sojin saman Nijeriya, tace shima bisa kuskure ne.

Diyya[gyara sashe | gyara masomin]

Gwamnatin kasar ta ce zata biya diyyar rayukan da aka rasa sakamakon harin.

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima ya fadi hakan yayin wata ziyara daya kai Kaduna a kwanan nan.

Inda ya ƙara da cewar; za’a gina makarantu da asibiti da kuma gidaje don inganta rayuwar al’ummar dake zaune a wannan yanki.[22]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.voahausa.com/a/jirgin-sama-mara-matuki-ya-kai-hari-kan-wasu-masu-bikin-mauludi-a-kaduna/7383434.html
  2. https://www.rfi.fr/ha/najeriya/20231204-mutane-30-suka-mutu-a-harin-jirgin-sojin-saman-najeriya-kan-masu-maulidi-a-kaduna
  3. https://www.premiumtimesng.com/regional/nwest/648806-at-least-31-civilians-killed-in-kaduna-military-airstrike.html
  4. https://dailytrust.com/breaking-kaduna-villagers-bombed-during-maulud-celebration/
  5. https://www.trtafrika.com/ha/africa/nijeriya-ta-tabbatar-mutum-85-sojoji-suka-kashe-bisa-kuskure-a-kaduna-16110281
  6. https://punchng.com/outrage-as-warplane-kills-85-in-kaduna-village-bombing/
  7. 7.0 7.1 https://edition.cnn.com/2023/12/05/africa/nigerias-president-calls-for-investigation-after-85-civilians-killed-in-drone-attack/index.html
  8. https://www.aljazeera.com/news/2023/12/5/nigerian-military-drone-attack-kills-85-civilians-in-error
  9. https://hausa.legit.ng/news/1566928-rundunar-sojin-sama-ta-yi-martani-kan-zargin-kai-harin-bam-kan-masu-maulidi-a-kaduna-ta-roki-jamaa/
  10. https://www.channelstv.com/2023/12/04/naf-denies-carrying-out-bomb-attack-in-kaduna-village/
  11. https://aminiya.ng/sojojin-sama-sun-musanta-kashe-masu-taron-mauludi-a-kaduna/
  12. 12.0 12.1 https://punchng.com/nigerian-army-admits-bombing-villagers-in-error-kaduna/
  13. 13.0 13.1 https://www.vanguardngr.com/2023/12/air-force-denies-bombing-kaduna-village/
  14. 14.0 14.1 https://dailytrust.com/breaking-army-claims-responsibility-for-bombing-of-kaduna-villagers/?fbclid=IwAR18kMaHtXPQBVLIRa15Ah7boSQnqZK-z2geqXdxlegWsgKu9AlbuKSCkMk
  15. 15.0 15.1 https://thenationonlineng.net/army-takes-responsibility-for-bombing-of-civilians-in-kaduna/
  16. https://www.bbc.com/hausa/articles/cd1pw7ekj15o
  17. https://www.facebook.com/100064878062378/posts/743384094500853/?mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
  18. https://www.channelstv.com/2023/12/04/governor-sani-orders-probe-of-kaduna-bomb-incident/
  19. https://www.thecable.ng/uba-sani-orders-investigation-into-airstrike-which-killed-over-30-kaduna-villagers/amp
  20. https://punchng.com/acf-jni-want-justice-for-kaduna-bomb-victims/
  21. https://dailytrust.com/northern-elders-demand-justice-for-kaduna-bombing-victims/
  22. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g2qr40l2xo