Jump to content

Ibrahim Jalo Waziri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ibrahim Jalo Waziri
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

1960 - 1966
Rayuwa
Haihuwa Gombe,, 17 Disamba 1926
Mutuwa 12 Nuwamba, 1984
Sana'a

Ibrahim Jalo Waziri (16 ga Disamba, 1926 - Nuwamba 1984) ya kasance malami, mai gudanarwa, shugaban gargajiya kuma dan siyasa daga Arewacin Najeriya wanda aka zaba sau biyu a matsayin Kakakin Majalisar Tarayya na Wakilin Nijeriya daga shekara ta alib 1960 zuwa shekara ta alif 1963 da shekara ta alib 1963 har zuwa juyin mulkin soja na shekara ta 1966 a cikin Janairu.

Ibrahim Jalo Waziri a cikin taro

An haifi Jalo a garin Gombe, jihar Gombe a cikin dangin mai ba da shawara na masarauta a masarautar Gombe, mahaifinsa. Bafulatani ne daga zuriyar Nafada Muhammadu Jingudo shi ne 'Ubandoma' na masarautar. Ya fara karatunsa a makarantar Alkur'ani kafin a shekarar alib 1936 ya shiga makarantar Elementary ta Gombe zuwa shekara ta alib 1940 sannan ya halarci makarantar Midil ta Bauchi daga shekara ta alib 1940 zuwa shekara ta alib 1943 shekara ta kuma a can ya je ya halarci makarantar sakandare da ake kira Barewa College kafin ta zama Katsina College sannan Kwalejin Kaduna daga karshe ya koma Barewa daga shekara ta alib 1943 zuwa shekara ta alib 1946. Ya shiga Kwalejin Horar da Malamai, Zariya a ashekara ta alib 1946 kuma ya kammala a shekara ta alib 1948 da shedar Grade II kuma ya tafi kwas na Kananan Hukumomin Yammacin Afirka daga Makarantar Tattalin Arziki ta London daga shekara ta alib 1954 zuwa shekara ta alib 1955.

Bayan ya gama karatunsa, ya fara aiki a matsayin malami a shekara ta alif 1948 a makarantar Midil ta Bauchi zuwa ahekara ta alib 1952 inda ya zama Shugaban makarantar firamare ta Gombe, a wannan shekarar ce mahaifinsa ya rike mukamin 'Ubandoma' na masarautar Gombe.

Daga baya anyi masa lakabi da Wazirin Masarautar Gombe a lokacin yana Landan don karantar ilimin Karamar Hukuma a shekarar ta alib 1956 a can.

https://www.sunnewsonline.com/northern-group-eulogises-late-jalo-waziri/ https://www.thisdaylive.com/index.php/2020/10/01/i-love-the-flamboyance-of-second-republic-senators/ https://nigerianwiki.com/Ibrahim_Jalo_Waziri Archived 2023-11-22 at the Wayback Machine https://blerf.org/index.php/biography/alhaji-ibrahimjalo-mp-cfr-waziri-gombe/