Igwe Aja-Nwachukwu
Igwe Aja-Nwachukwu | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Shekarun haihuwa | 31 ga Maris, 1952 |
Lokacin mutuwa | 17 Nuwamba, 2015 |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | Minister of Education of Nigeria (en) da Minister of Education of Nigeria (en) |
Ilimi a | Jami'ar Ibadan |
Igwe Aja-Nwachuku (Ranar 31 ga watan Maris ɗin 1952 - ranar 17 ga watan Nuwamban 2015) ɗan siyasar Najeriya ne. Ya ƙare wa'adinsa na ministan ilimi a Najeriya a ranar 17 ga watan Disamban 2008. An naɗa shi ministan ilimi watanni goma sha takwas kafin nan.[1][2] Dr. Sam Egwu ya maye gurbinsa a matsayin ministan ilimi. Dokta Aja-Nwachukwu ya kammala karatunsa na digiri na biyu a Jami’ar Ibadan da digirin digirgir (B.Sc) a fannin ƙididdiga, ya yi MBA Finance, M.Sc Statistics da Ph.D a fannin tattalin arziƙi. Sannan yana da Difloma a fannin Kimiyyar Kwamfuta da Injiniya.
Ya fara aikin gwamnati ne a matsayin jami’in ilimi a ma’aikatar ilimi ta jihar Ebonyi a cikin shekarar 1979 a matsayin malamin lissafi. A tsakanin shekarar 1984 zuwa 2006, ya koyar da harkokin kuɗi da kasuwanci a matsayin malami a jami'ar jihar Abia da jami'ar jihar Ebonyi, Abakaliki . Dr. Aja-Nwachukwu ya kuma tsaya takarar gwamnan jihar Ebonyi ta Najeriya a zaɓen shekarar 2007. Ya kasance ɗan Aja Nwachukwu, Ministan Ilimi na Najeriya na farko.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Jerin mutanen jihar Ebonyi