Sam Egwu
Sam Egwu | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
ga Yuni, 2019 - District: Ebonyi North
29 Mayu 2015 - District: Ebonyi North
17 Disamba 2008 - 17 ga Maris, 2010 ← Igwe Aja-Nwachukwu - Ruqayyah Ahmed Rufa'i →
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 ← Simeon Oduoye - Martin Elechi → | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | 20 ga Yuni, 1954 (70 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Ƙabila | Tarihin Mutanen Ibo | ||||||||
Harshen uwa | Harshen Ibo | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta |
Jami'ar Najeriya, Nsukka Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu | ||||||||
Harsuna |
Turanci Harshen Ibo Pidgin na Najeriya | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Sam Ominyi Egwu CON (an haife shi a ranar 20 ga watan Yunin shekara ta,1954) ɗan siyasar kasar Najeriya ne kuma memba a jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) dke Najeriya. An zaɓe shi gwamnan jihar Ebonyi a zaɓen gwamnan jihar Ebonyi a cikin shekarar 1999 daga ranar 29 ga watan Mayun shekarar, 1999 zuwa 29 ga watan Mayun shekara ta, 2007.[1] Dr Egwu an san shi a matsayin ginshiƙi na ci gaban ilimi a jihar Ebonyi a Najeriya.[2] Ya halarci Jami'ar Najeriya, Nsukka inda ya sami digiri na farko a fannin aikin gona a cikin shekarar, 1981. Daga nan ya samu digirin digirgir a fannin aikin gona daga jami’ar Najeriya dake Nsukka a cikin shekarar 1987 da kuma digiri na uku a fannin aikin gona daga jami’ar fasaha ta jihar Enugu a cikin shekarar 1996. Ya kasance babban malami a jami’ar fasaha ta jihar Enugu kuma ya taɓa zama kwamishinan ilimi a jihar Ebonyi ya ba da gudunmawa wajen nasarorin da aka samu a fannin ilimi a lokacin da yake gwamna.[3]
A cikin shekarar 2008, Shugaba Umaru Ƴar'adua ya naɗa shi Ministan Ilimi, inda ya riƙe har zuwa watan Afrilun shekara ta, 2010 lokacin da Farfesa Ruqayyah Ahmed Rufa'i ya maye gurbinsa.[4]
Egwu shine zaɓin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya zama shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa a babban taronta na ƙasa a cikin shekarar 2008. Duk da haka, a taron da aka yi a ranar 8 ga watan Maris a shekara ta, 2008, ya janye goyon bayan ɗan takara Prince Vincent Ogbulafor, wanda aka zaɓa a matsayin madadin Egwu da babban abokin takararsa, Anyim Pius Anyim.[5]
Zamansa na ministan ilimi ya kasance da ƙungiyar ASUU (Academic Staff Union of Universities) da sauran yajin aikin da ƙungiyoyin jami'o'i ke yi. Hakan ya sa mutane suka nemi a kore shi daga aiki.[6]
A cikin shekarar 2015, ya samu nasarar tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Ebonyi ta Arewa a ƙarƙashin jam’iyyar People’s Democratic Party.[7] A halin yanzu, shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan masana’antu.[8][9]
Kyaututtuka da karramawa
[gyara sashe | gyara masomin]- Kwamandan oda na Niger (CON).
- D.Sc. (Honoriscausa) na Jami'ar Najeriya, Nsukka, 2006.
- D.Sc. (Honoriscausa) na Ebonyi State University, Abakaliki, 2008.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Jerin Gwamnonin Jihar Ebonyi
- Jerin mutanen jihar Ebonyi
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://sunnewsonline.com/2023-ebonyi-governorship-and-zoning-controversy/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-19. Retrieved 2023-03-18.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-18. Retrieved 2023-03-18.
- ↑ https://allafrica.com/stories/201004070116.html
- ↑ https://allafrica.com/stories/200803090001.html
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2009/07/leave-sam-egwu-alone/
- ↑ https://www.nigerianeye.com/2015/04/know-your-senators-list-of-senators.html?m=1
- ↑ https://www.nasco.net/courtesy-visit-by-senate-committee-on-industries/
- ↑ http://www.aitonline.tv/post-senate_committee_sees_to_procurement_of_locally_made_vehicles