Simeon Oduoye
Simeon Oduoye | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2007 - 6 ga Yuni, 2011 ← Akinlabi Olasunkanmi - Olusola Adeyeye → District: Osun Central
ga Augusta, 1998 - Mayu 1999 ← Walter Feghabo (en) - Sam Egwu →
22 ga Augusta, 1996 - ga Augusta, 1998 ← Cletus Komena Emein - Habibu Idris Shuaibu → | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Ikirun (en) , 13 ga Afirilu, 1945 | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Ƙabila | Yaren Yarbawa | ||||||
Harshen uwa | Yarbanci | ||||||
Mutuwa | Osogbo, 21 ga Maris, 2014 | ||||||
Karatu | |||||||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Simeon Olasukanmi Oduoye (13 ga Afrilun 1945 - 21 Maris 2014) ɗan sandan Najeriya ne kuma mai kula da jihohi guda biyu jihar Neja da jihar Ebonyi. An zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Osun ta tsakiya a watan Afrilun 2007 a dandalin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).[1][2]
Fage
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Simeon Oduoye a ranar 13 ga watan Afrilun 1945. Ya samu takardar shedar makarantar Afirka ta Yamma a shekarar 1964 daga makarantar Akinorum Grammar School, Ikirun. Ya shiga aikin ƴan sandan Najeriya a ranar 1 ga watan Yulin 1965. Ya zama Mataimakin Sufeto Janar na ƴan Sanda, inda ya yi ritaya a cikin shekarar 1999. Ya kasance Mai Gudanarwa a Jihar Neja da Ebonyi daga 1996 zuwa 1999. Ya kasance shugaban NSPRI daga 2005 zuwa 2007. Shi ne Shugaba kuma Manajan Darakta na Layo Woodmill Nigeria Ltd.[1][3]
A matsayinsa na mai kula da jihar Ebonyi, ɗaya daga cikin ayyukansa na farko shine kafa kwamitin da zai sake fasalin ma’aikatan jihar don tabbatar da tsari, girma, kiyaye dokoki da ƙa’idoji.[4] A wata hira da aka yi da shi a watan Oktoba na shekarar 2009, Sanata Julius Agbo ya buga misali da gwamnatin Oduoye na wani mutum mai tsari da ya yi ƙoƙarin kafa ma’aikatan gwamnati a jihar Ebonyi.[5]
Aikin majalisar dattawa
[gyara sashe | gyara masomin]An zaɓi Simeon Oduoye ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Osun ta tsakiya a watan Afrilun 2007 a jam'iyyar (PDP). An naɗa shi a kwamitocin tsaro da leƙen asiri, wutar lantarki, sufurin ƙasa, harkokin cikin gida, yaƙi da cin hanci da rashawa na miyagun ƙwayoyi da sojojin sama.[1]
A watan Mayun 2008, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan tsaro da leƙen asiri na ƙasa,[6] Oduoye ya ce majalisar dattawa ta kusa amincewa da kafa wata kotu ta musamman kan laifukan kuɗi.[7]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Shi ne mahaifin Abidemi Oduoye, Kayode Oduoye, Olanike Oduoye, Olajumoke Oduoye, Olaoluwa Oduoye da Babatunde Oduoye.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 https://web.archive.org/web/20160303180737/http://www.nassnig.org/senate/member.php?senator=54
- ↑ https://web.archive.org/web/20140323092144/http://www.osundefender.org/?p=155263
- ↑ http://senatorsimeonoduoye.com/meet%20the%20senator.html[permanent dead link]
- ↑ https://fissionclassifieds.com/
- ↑ https://web.archive.org/web/20110726120557/http://thenationonlineng.net/web2/articles/21790/1/Senator-Why-lawmakers-deserve-automatic-ticket/Page1.html
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/tag/national-intelligence-agency-nia
- ↑ http://allafrica.com/stories/200805120540.html