Jump to content

Irène Assiba d'Almeida

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
D'Almeida in 2013

Irène Assiba d'Almeida mawakiyar ƙasar Benin ce, mai fassara sannan kuma ƙwararriya a fannin adabi. Ita ce Farfesa na Nazarin Watsa Labarai da yaren Faransanci a Jami'ar Arizona.

An haifi Irène Assiba d'Almeida a Dakar, Senegal, ga iyayen Dahomeyan. Ta yi karatu a Benin kafin ta sami digiri na BA a Jami'ar Amiens da ke Faransa, da kuma MPP daga Jami'ar Ibadan a Najeriya. Ta sami digirin digirgir a shekarar 1987 daga Jami’ar Emory da ke Amurka. Ta haɗa kai da Olga Mahougbe wajen fassara littafin nan na Chinua Achebe Arrow of God zuwa harshen Faransanci. [1]

Littafin farko na D'Almeida, marubutan matan Afirka na Faransanci, (Francophone African women writers) an yi marhabin da shi a matsayin "wani taron na Afirka, Mata da Harshen Faransanci". [2] Ita ce mai shirya taron 2010 na Ƙungiyar Adabin Afirka, wanda aka gudanar a Jami'ar Arizona. An wallafa gudummawar a matsayin Eco-imagination: African and diasporan literatures and sustainability (2013). [3]

  • Francophone African Women Writers: destroying the emptiness of silence. Gainesville: University Press of Florida, 1994.
  • (ed.) A Rain of Words: a bilingual anthology of women's poetry in Francophone Africa. Charlottesville: University of Virginia Press, 2009. Translated by Janis A. Mayes.
  • (ed. with John Conteh-Morgan) "The original explosion that created worlds": essays on Werewere Liking's art and writings. Amsterdam; New York: Rodopi, 2010.
  • (ed. with Lucie Viakinnou-Brinson and Thelma Pinto) Eco-imagination: African and diasporan literatures and sustainability. Trenton, New Jersey: Africa World Press, 2013.
  • (ed. with Sonia Lee) Essais et documentaires des Africaines francophones: un autre regard sur l'Afrique. Paris: L'Harmattan, 2015.
  • (with Elsie Augustave) Autour de "L'enfant noir" de Camara Laye: un monde à découvrir. Paris: l'Harmattan, 2018.
  1. Stella and Frank Chipasula, ed., The Heinemann Book of African Women's Poetry, Heinemann, 1995, p. 216.
  2. Sylvie Kandé, "Review of Francophone African Women Writers: Destroying the Emptiness of Silence", Research in African Literatures, Vol. 27, No. 2 (Summer 1996), pp. 226–229.
  3. Professor Irène Assiba d'Almeida[permanent dead link]