Jump to content

Jami'ar Ilimi ta Sa'adatu Rimi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jami'ar Ilimi ta Sa'adatu Rimi

Bayanai
Iri jami'a
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 14 ga Faburairu, 2023
srcoe.edu.ng

Sa'adatu Rimi University of Education Kano jami'ar ilimi ce mallakin gwamnatin jaha a jihar Kanon Najeriya . Gwamnatin jihar Kano ta mayar da jami’ar daga kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi zuwa jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi a shekarar 2023.[1][2][3][4][5]

Laburaren ko dakin karaton Kwalejin yana cikin babban ɗakin karatu tare da kayayyakin karato dasuke dauke da bayanai akan yanar kizo da kuma Wanda ba a yanar gizo ba Laburare na karkashin jagorancin mai shugabancinta mai suna Malama Mabruka Abubakar Abba.

Jami'ar koyarwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Hukumar Jami’ar Kasa wato (NUC) ta amince da daukaka darajar SRCOE daga kwaleji zuwa jami’a. Wannan mataki ta zo ne bayan da hukumar ta amince da kudurin da gwamnatin jihar Kano ta aike domin daukaka ta.

Ilimi Kyauta

[gyara sashe | gyara masomin]

An bai wa daliban wannan jami'a masu fama da nakasa ilimi kyauta.

Kwalejin Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso, wacce gwamnatin jihar Kano ta kafa a shekarar 1981, wadda wadda aka fi sani da Advanced Teacher’s College, Waje, ta kasance a sansanin Alhazai. An canza mata suna College of Education, Kumbotso, a 1982, ta koma Zariya Road, Kano, a karkashin Cibiyar Ilimi ta Jihar Kano. A shekarar 1987, aka raba cibiyar, wanda ya haifar da cin gashin kansa ga Kano State Polytechnic, Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano, da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano. Kwalejin tana da cibiyoyi biyu a Gumel da Kumbotso, tare da gwamnatin tsakiya a Gumel. Kwalejin ta rabu ne sakamakon kirkiro jihar Jigawa, inda ta kafa kwalejin ilimi ta jihar Jigawa da kwalejin ilimi ta jihar Kano. Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano ta rabu zuwa Wudil (Kimiyya da Ilimin Sana'a) da Kumbotso (arts, languages, and social sciences). Cibiyoyin biyu sun hade ne a Kumbotso bayan kafa Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kano . Daga baya aka canza wa kwalejin suna Sa’adatu Rimi College of Education, Kumbotso, domin karrama matar gwamnan farar hula na farko a jihar Kano , Abubakar Rimi.[6][7][8]

Jami'ar Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Hukumar Jami’ar Kasa, NUC, ta amince da daukaka darajar SRCOE daga kwaleji zuwa jami’a. Wannan shawarar ta zo ne bayan da hukumar ta amince da kudurin da gwamnatin jihar Kano ta aike domin daukaka kara.[9][10]

  1. "Redirect Notice". www.google.com. Retrieved 2023-08-16.
  2. Omidiji, Rachael (2023-02-13). "Ganduje receives letter of recognition for newly approved university in Kano". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2023-08-16.
  3. "FG approves upgrade of Rimi College to university - Daily Trust". dailytrust.com. Retrieved 2023-08-16.
  4. Usman, Mustapha (2023-02-14). "NUC upgrades Sa'adatu Rimi COE to university". Daily Nigerian (in Turanci). Retrieved 2023-08-16.
  5. Sulaiman (2023-02-15). "NUC Ta Daga Darajar Kwalejin Sa'adatu Rimi Zuwa Jami'a A Kano" (in Turanci). Retrieved 2023-08-16.
  6. Dokaji, Rahima Shehu (2023-02-15). "An mayar da Kwalejin Sa'adatu Rimi da ke Kano matsayin jami'a". Aminiya (in Turanci). Retrieved 2023-08-16.
  7. "Sa'adatu Rimi College of Education srcoe| School Fees, Courses & Admission info". universitycompass.com. Retrieved 2023-08-16.
  8. "Sa adatu Rimi College Of Education | Kano | Listed in Education - Colleges & Universities". www.nigeriabusinessweb.com (in Turanci). Retrieved 2023-08-16.
  9. HotPen (2021-10-21). "Kano Govt. to upgrade Sa'adatu Rimi College of Education to University status | HOTPEN" (in Turanci). Retrieved 2023-08-16.
  10. "Time Express Nigeria » KNHA UPGRADES SA'ADATU RIMI COLLEGE TO UNIVERSITY OF EDUCATION, INCREASE RETIREMENT AGE, OTHERS" (in Turanci). 2023-01-31. Retrieved 2023-08-16.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]