Jelani Aliyu
Jelani Aliyu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Kaduna, 11 Satumba 1968 (56 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta | College for Creative Studies (en) |
Sana'a | |
Sana'a | designer (en) da ɗan kasuwa |
jelanialiyu.com |
Jelani Aliyu (akuma n haife shi a ranar 11 ga watan Satumban Shekarar 1966) ɗan Najeriya ne mai ƙera motoci, wanda ya yi aiki da kamfanin ƙera motoci na Amurka General Motors. Ya kasance babban mai tsara zane-zane a GM, har zuwa lokacin da shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin Babban Darakta na Hukumar ƙera motoci da cigaban Najeriya (NADDC) a shekarar 2017.
Tasowa da Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An kuma haifi Aliyu a shekarar 1966 a Kaduna Nijeriya, a cikin dangin Alhaji Aliyu Haidar da Hajiya Sharifiyya Hauwa Aliyu, shi ne na biyar a cikin ’ya’ya bakwai a gidan wadanda ’yan asalin Dogon-daji ne a Jihar Sokoto , wannan ne ya sa aka koma da matashin Aliyu Sokoto don neman ilimi. Ya yi karatu a Sokoto Capital School daga shekarar 1971 zuwa 1978 sannan ya yi karatu a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Sakkwato inda ya samu lambar yabo na dalibin da ya fi kowa yaye a Technical Drawing.
A shekarar 1986, Aliyu ya sami admission don karantar Architecture a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria. Sai dai da sauri Aliyu ya fice daga jami'ar inda ya gano cewa karatu a jami'ar da wuya ya ba shi damar ci gaba da burinsa na zama mai zanen mota domin karatu a can baya aiki kamar yadda ake yi a polytechnic sannan ya wuce zuwa Federal Polytechnic Birnin Kebbi da ke Kebbi State daga 1986 zuwa shekarar 1988 inda ya sami associate digiri a fannin architecture tare dkuma a lambar yabo na Gwarzon Ɗalibai. Yayin da yake can ya fara neman izinin shiga makarantun zane a Turai da Amurka wanda zai kai shi GA sana'ar Ƙera motoci.[1][2][3]
A shekarar 1990, Hukumar bayar da tallafin karatu ta Jihar Sakkwato ta dauki nauyin daukar nauyin Aliyu don yin karatu a Amurka a College for Creative Studies da ke Detroit don karantar fasahar kere-kere. Yayin karatun Aliyu ya sami lambobin yabo biyu masu daraja daga Kamfanin Motoci na Ford da Michelin, Amurka. A shekarar 1994, Aliyu ya samu digirin sa a fannin kera motoci, nan take ya shiga tawagar [General Motors], inda ya fara aikin ƙere-ƙere.[4][5][6]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1994 bayan kammala karatunsa daga College for Creative Studies, Aliyu ya shiga General Motors.[4] A General Motors Aliyu shi ne mai co-desinger na Oldsmobile Bravada, [[Buick]. Rendezvous]] da Opel Astra kuma shine jagorar zanen waje na Pontiac G6 da Chevrolet Volt, abin hawa na lantarki tare da sleek arcing roofline.
Lokacin da yake magana game da inspiration na sana'arsa ta ƙera motoci a cikin wata hira, Jelani ya ce;
Na kasance ina son zane. Waɗannan abubuwa ne daban-daban a kusa da ni, mutane, abubuwa, tsire-tsire, da kuma abubuwa daga tunanina. Na girma cikin ƙaunar science fiction sannan kuma a cikin fina-finai, za ku ga yawancin spacecraft na zayayyu da sauran abubuwa na futuristic waɗanda za su ƙarfafa ni in yi hangen nesa. Ina kuma son motoci sosai, duk da cewa a lokacin ba mu da Ferrari a Sakkwato. Duk da haka, muna da mujallu da na gan su, kuma sun ƙarfafa ni. Don haka na haɗa soyayyata na zane da motoci na yanke shawarar zama mai zanen mota.[7]
Ya kuma ce, abin da ya zaburar da shi iyayensa ne domin sun bar shi ya yanke shawarar abin da yake son yi. Misali, lokacin da ya je Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya yanke shawarar ba zai ci gaba da zama a can ba, sun ƙarfafa masa guiwa. Ba su nace cewa dole ne ya zauna a wurin ba. Akan zanen Chevrolet Volt, ya ce;
Duba wani ɗan ƙaramin ganye, kauri ne kawai na 'yar millimita amma duk da haka ingantacciyar masana'anta ce,.. Na yi ƙoƙarin fahimtar ingancin yanayi da ƙirarsa kuma na jawo waɗannan concepts na yi amfani da su a Chevrolet Volt.[7]
Sanannun Zayyanoni
[gyara sashe | gyara masomin]- 2004 Pontiac G6
- 2010 Chevrolet Volt
Kuma ga
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Nigerian You might not hear about meet Jelani Aliyu". Nigeria Television Authority. January 2014. Archived from the original on 27 February 2021. Retrieved 17 June 2020.
- ↑ "Jelani Aliyu The design revolutionary". The Guardian Nigeria. January 2015. Archived from the original on 9 December 2019. Retrieved 17 June 2020.
- ↑ "Welcome home Jelani Aliyu". The Nigeria Pilot. January 2015. Archived from the original on 22 June 2020. Retrieved 17 June 2020.
- ↑ 4.0 4.1 "American Dreamers Jelani Aliyu 40". Crains Detroit. 25 March 2007. Retrieved 20 June 2020.
- ↑ "Jelani Aliyu General Motors designer of the Chevy Volt". Life and Times Magazine. January 2015. Retrieved 29 August 2018.
- ↑ "Jelani Aliyu". Auto Josh. 14 April 2017. Retrieved 20 June 2020.
- ↑ 7.0 7.1 "Welcome home Jelani Aliyu". The Punch Nigeria. January 2015. Retrieved 17 June 2020.