Jump to content

Jihadin Islama a Masar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jihadin Islama a Masar
Bayanai
Gajeren suna EIJ
Iri armed organization (en) Fassara da ƙungiyar ta'addanci
Ƙasa Misra
Ideology (en) Fassara Islamism (en) Fassara
Mulki
Shugaba Ayman al-Zawahiri (en) Fassara da Muhammad abd-al-Salam Faraj (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 1979
Wanda ya samar
Dissolved ga Yuni, 2001
inda masar take a taswiran duniya

Jihadin Islama a Masar (EIJ), [1] [2] asalin sunansa al-Jihad, [3] [4] ƙungiya ce ta 'ƴan ta'adda a Masar bisa tushen wuce gona da kuma iri na fassarar Islama. Tana kuma aiki tun a ƙarshen shekarun 1970. Tana ƙarƙashin takunkumin duniya da Majalisar Dinkin Duniya a matsayin ƙungiyar da ke da alaƙa da al-Qaeda. [5] Haka nan gwamnatoci da yawa a duniya sun dakatar da shi, gami da na Tarayyar Rasha . [6]

Tun 1991 ta ke jagorancin Ayman al-Zawahiri, wanda yanzu shi ne shugaban kungiyar al-Qaeda. A cewar Zawahiri, EIJ "ya kuma banbanta da kungiyar Takfir wal Hijra saboda ba ma daukar mutane kafirai saboda zunubansu. Kuma mun sha bamban da kungiyar ‘Yan'uwa Musulmi saboda wani lokacin ba sa adawa da gwamnati”. [7]

tutar masar

Babban burin ƙungiyar shi ne asalin kifar da gwamnatin Masar tare da maye gurbinta da ƙasar musulinci bisa tsarin da take tunanin yakamata musulinci ya kasance. Daga baya ta faɗaɗa manufofinta waɗanda kuma suka haɗa da kai wa Amurka da Isra'ila hari, da sauran muradun Misira da ƙasashen waje.

Jihadin Islama ne ke da alhakin kisan Anwar Sadat a 1981. Yarjejeniyar Sadat da Sinai da Isra’ila, wacce ta amince da mulkin Yahudawa, ya ba su haushi sosai. [4]

Haɗewa da Al Qaeda

[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Yunin 2001, Al Qaeda da Jihadin Islama na Masar, wadanda suke da alaƙa da juna tsawon shekaru, suka hade cikin 'Qaeda al-Jihad'.

"... membobin ƙungiyar Jihadin Islama da jagoranta, Ayman al-Zawahiri, sun samar da ƙashin bayan shugabancin [al-Quaeda]. A cewar jami’ai a hukumar leken asirin ta CIA da FBI, Zawahiri ne ke da alhakin yawancin ayyukan ta’addancin da aka yi wa Amurka ”.
  1. Larabci: الجهاد الإسلامي المصري‎ (EIJ), formerly called simply Islamic Jihad الجهاد الإسلامي and Liberation Army for Holy Sites.
  2. Global Briefings, Issue 27, September 1998, “Osama Bin Laden tied to other fundamentalists”.
  3. " and then "the Jihad Group", or "the Jihad Organization"
  4. 4.0 4.1 Wright, Lawrence, Looming Tower, Knopf, 2006, p.123
  5. Affiliates of al-Qaeda and the Taliban, United Nations Security Council Committee 1267
  6. ‘Terror’ list out; Russia tags two Kuwaiti groups Archived 2007-03-11 at the Wayback Machine, Arab Times, February 2003
  7. al-Zayat, Montasser 2002. The road to al-Qaeda.