Julie Manning
Julie Manning | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Morogoro (en) , 24 ga Janairu, 1939 (85 shekaru) |
ƙasa | Tanzaniya |
Harshen uwa | Harshen Swahili |
Karatu | |
Makaranta | University of East Africa (en) |
Harsuna |
Turanci Harshen Swahili |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa, Lauya da mai shari'a |
Julie Catherine Manning, (An haife ta ranar 24 ga watan Janairu, 1939). ƴar kasar Tanzaniya ce kuma lauya ce, alkali, ƴar siyasa. Matar Tanzaniya ta farko da ta fara karatun shari'a, ta kasance alkaliya a babbar kotu kafin ta zama ministar shari'a daga shekarar 1975 zuwa 1983.
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin 1963 Julie Manning ta zama mace ta farko da ta fara karatun shari'a a Jami'ar Gabashin Afirka.Daga baya ta yi aiki a matsayin mai ba da doka a zauren Attorney General's Chamber.[1] A shekarar 1973 aka nada ta alkali a babbar kotun kasar Tanzaniya, wanda hakan ya sa ta zama mace ta farko a Afirka ta zama alkalin babbar kotun kasar a gabashi ko tsakiyar Afrika.[2] A cikin 1975 an nada ta ministar shari'a, inda ta zama daya daga cikin mata biyu na farko da suka yi aiki a majalisar ministocin Tanzaniya.[3]
Bayan Joseph Warioba ya gaji Manning a matsayin Ministan Shari'a a 1983, ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara a ofishin jakadancin Tanzaniya Ottawa, Kanada.