Kaletapwa Farauta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Kaletapwa Farauta
mataimakin gwamna

Rayuwa
Haihuwa Numan (Nijeriya), 28 Nuwamba, 1965 (58 shekaru)
ƙasa Najeriya
Mazauni Numan (Nijeriya)
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Jami'ar Najeriya, Nsukka
Jami'ar Modibbo Adama ta Fasaha ta Tarayya, Yola.
Federal College of Education, Yola (en) Fassara
Jami'ar Najeriya, Nsukka
Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Tambuwal
(1979 - 1983)
Matakin karatu Digiri a kimiyya
Master of Science (en) Fassara
Doctor of Philosophy (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami, mataimakin shugaban jami'a da ɗan siyasa

Kaletapwa George Farauta (an haife ta a ranar 28 ga watan Nuwamba a shekarar 1965) farfesa ce kuma 'yar siyasa sannan 'yar Najeriya, wacce Ita ce mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa a yanzu tun a shekarar 2023[1][2][3][4][5][6]. Ta kasance mataimakiyar shugabar jami'ar jihar Adamawa, Mubi daga shekarun 2017 zuwa 2022.[7] [8] [1][2]Tsohuwar kwamishinar ilimi ce ta jihar Adamawa kuma shugabar zartaswa ta ilimi ta bai ɗaya. [2]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Kaletapwa Farauta a ranar 28 ga watan Nuwamba a shekarar 1965 a ƙaramar hukumar Numan ta jihar Adamawa.[3] [6][5][9]Ta samu takardar shaidar kammala makarantar firamare a Numan II Primary School, Numan a shekarar 1979. A shekarar 1983 ta samu takardar shedar babbar makaranta a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) Yola. A shekara ta 1987, ta samu takardar shedar ilimi ta ƙasa a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) Yola. [10]. Ta yi digirinta na farko da na biyu a fannin aikin gona a Jami’ar Najeriya Nsukka a shekarun 1989 da 1995. Ta samu digirin digirgir a Jami’ar Fasaha ta Tarayya a halin yanzu da ake kira Modibbo Adama Federal University of Technology, Yola. [8][5][9]

Nadtin siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Daga watan Yuli zuwa watan Oktoba na shekarar 2014, Farauta ta yi aiki a matsayin Babbar Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Farko ta Jihar Adamawa (ADSUBEB). A ranar 28 ga watan Agusta 2015 Farauta ta karbi muƙamin kwamishiniyar ma'aikatar ilimi ta jihar Adamawa kuma yta bar ofishin a ranar 17 ga watan Yuli a shekarar 2017. [2][10][5]

Mataimakiyar shugaban jami'a[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 17 ga watan Yulina shekarar 2017, gwamnan jihar Adamawa na lokacin, Sanata Muhammad Umaru Jibrilla Bindow ya naɗa ta mukaddashin shugabar jami'ar jihar Adamawa. Daga karshe Ahmadu Fintiri ya tabbatar da ita a matsayin mataimakiyar shugabar gwamnati. [11]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Seth supports my decision to take new deputy, says Fintiri". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2022-08-04. Retrieved 2022-10-16.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 Jeremiah, Urowayino (2022-07-01). "Gov Fintiri dumps deputy, picks don". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2022-10-16.
  3. 3.0 3.1 "Fintiri unveils female professor as running mate for 2023 guber poll". The Nation Newspaper (in Turanci). 2022-08-03. Retrieved 2022-10-16.
  4. "Fintiri unveils female running mate, praises deputy gov". Punch Newspapers (in Turanci). 2022-08-03. Retrieved 2022-10-16.
  5. 5.0 5.1 5.2 5.3 Hammangabdo, Hussaini (2022-06-30). "JUST-IN: Gov Fintiri Picks Adamawa Varsity VC, Prof. Farauta, As Running Mate" (in Turanci). Retrieved 2022-10-16.
  6. 6.0 6.1 Bello, Usman (2022-08-03). "2023: Adamawa Gov picks Female Professor as running mate". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2022-10-16.
  7. "Adamawa University begs indigenes to seek admission - P.M. News" (in Turanci). Retrieved 2022-10-16.
  8. 8.0 8.1 "Fintiri unveils female professor as running mate for 2023 guber poll". The Nation Newspaper (in Turanci). 2022-08-03. Retrieved 2022-10-16.
  9. 9.0 9.1 "2023: Gov. Fintiri unveils Adamawa varsity VC as running mate" (in Turanci). 2022-08-03. Retrieved 2022-10-16.
  10. 10.0 10.1 "Professor Kaletapwa Farauta: Meet Adamawa Governor female running mate for 2023 with intimidating credentials". Apex News Exclusive (in Turanci). Retrieved 2022-10-16.
  11. Blueprint (2022-07-14). "On Fintiri's running mate Farauta". Blueprint Newspapers (in Turanci). Archived from the original on 2022-10-17. Retrieved 2022-10-17.