Kolapo Ishola
Kolapo Ishola | |||
---|---|---|---|
2 ga Janairu, 1992 - 17 Nuwamba, 1993 ← Abdulkareem Adisa - Adetoye Oyetola Sode → | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Kolapo Olawuyi Ishola | ||
Haihuwa | ga Yuni, 1934 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Yaren Yarbawa | ||
Mutuwa | 9 ga Augusta, 2011 | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Jam'iyyar SDP |
Haihuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Anhafi kolapo Olawuyi Ishola (6 Yunin shekarar 1934 – 9 ga Agusta 2011) ɗan siyasan Najeriya ne wanda aka zaɓa a tsarin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a matsayin Gwamnan Jihar Oyo, Nijeriya, mai riƙe da mukami tsakanin Janairu 1992 zuwa Nuwamban shekarar 1993 a lokacin Jamhuriyya ta Uku . [1]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Ishola ya fara aiki a matsayin Mataimakin Bincike a Ma'aikatar Kasa, (1956-1959), sannan a matsayin Infeto na Gine-gine tare da Gwamnatin Ibadan (1959-1960). Ya kuma yi aiki a matsayin mai binciken filaye da gwamnatin tarayya. Ya yi karatu a Landan kuma ya zama abokin aikin Royal Institution of Chartered Surveyors . A shekarar 1969 ya samu takardar shaidar lasisin Surveyors na Najeriya. [2]
Gwamna
[gyara sashe | gyara masomin]An zaɓi Ishola ne a dandalin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a matsayin gwamnan jihar Oyo a watan Disambar shekarar 1991, inda ya hau mulki a ranar 2 ga Janairun shekarar 1992. A ranar 3 ga Satumba 1992 Ishola ya kafa hukumar hidimar koyarwa ta makarantun gaba da firamare ta jihar Oyo. Ya kuma kafa Makarantar Kimiyya, Pade, wanda gwamnatin mulkin soja ta yi watsi da ita. Ishola ya bar ofis a ranar 17 ga Nuwamba 1993 lokacin da Janar Sani Abacha ya karbi mulki. [3]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Kolapo Olawuyi Ishola ya rasu ne a lokacin dayaks bacci da sanyin safiyar ranar talata, 9 ga watan Agusta, 2011 a Ibadan, Kudu maso Yammacin Najeriya, yana da shekaru 77. [4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.vanguardngr.com/2011/08/kolapo-ishola-ex-oyo-gov-dies-at-77/
- ↑ https://independent.ng/family-celebrates-10yrs-rememberance-of-former-oyo-governor-kolapo-ishola/
- ↑ http://saharareporters.com/2011/08/09/ex-oyo-state-governor-kolapo-ishola-dead-nation
- ↑ https://pmnewsnigeria.com/2011/08/09/ex-oyo-gov-kolapo-ishola-dies/