Lawan Dambazau
Malam Lawan Dambazau,' (An haife shi a shekara ta alif dari tara da ashirin da biyu ,1922) a dambazawa, karamar hukumar ɗan batta dake garin Kano. ya dawo kano wajen ƴan uwan mahaifinsa lokacin yana da shekara biyar kuma a nan ya girma[1].
Farkon Rayuwa da Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Ya fara karatun addini a garin kano, daga baya yayi kaura zuwa Maiduguri don neman ilimin addinin Musulunci. (Unguru, potiskum da Azare a shekara ta alif dari tara da arba'in1940) ya rubuta littafi da yawa kamar su “ A true Northerner Aminu Kano (1956), the struggle for Nepu and PRP (1992), politics and region in Nigeria (1992)[2].
Bayan kammala karatunsa, ya dawo garin Kano inda ya hada gangami don wayar da kan mutane akan addini, zamantakewa dakuma siyasa, shi da manyan attajiran lokacinsa kamar su Ibrahim Waziri (1966-1992), Babban mawaki Aliyu Akilu dakuma Qadi Baffa Mahmud[3].
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Mallam lawan dambazau ya fara hidimar neman ƴanci tun kafin kafa NEPU a shekara ta 1950 sannan bayan kafa NEPU ya zama daya daga cikin ƴan kungiyan. A lokacin sabon abu ne ga al’umma don suna tsoron yin gaba da gaba da turawan mulkin mallaka. Mallam Dambazau ya sami cikas da maqiya musamman a Maiduguri inda ya kafa jama’atul islamiyya (watau Islamic party). Shine sakataren janar na kumgiyar na farko, inda ya dsamu horo da azabtarwa matuka daga turawa, da makiyansa. Mallam Dambazau da Abokansa kamar su Aminu Kano (1920-1983) da Mallam Sa’ad Zungur (1914-1958), sunyi yakin neman ƴancin kasan nan tsakanin (1914-1958). Mallam lawan mutum ne mara tsoro mai dumbin kwarjini da wanda wasu daga cikin shuwagabannin soja lokacin Gen. Olusugun Obasanjo, kan nemi shawara wurinsa kafin neman kujeran mulkin kasan[4].
Rasuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Mallam Lawal Dambazau ya rasu a safiyar laraba 13th ga watan satimba shkara ta 2000. A asibitin horo na Aminu Kano a garin Kano (lokacin yan shekara 78 da rayuwa), bayan yayi jinya na dan lokaci. An burne shi misalin karfe goma na safe a makabartar “kukar bulukiya” a bisa tsarin musulunci. Ya rasu ya bar yaya 8 da mata guda (yaya- Abba, Halima, Rukayya, Zubaida, Bashir, Najib, Hassan & fauziyya)[5].
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]Shatsari SS. (1991) Tributes to a Hero of the Masses. Mallam Lawan Dambazau.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Shatsari SS. (1991) Tributes to a Hero of the Masses. Mallam Lawan Dambazau. p.1
- ↑ Shatsari SS. (1991) Tributes to a Hero of the Masses.Mallam Lawan Dambazau. pp.1-3
- ↑ Shatsari SS. (1991) Tributes to a Hero of the Masses.Mallam Lawan Dambazau. p.3.
- ↑ Shatsari SS. (1991) Tributes to a Hero of the Masses.Mallam Lawan Dambazau. pp. 6-11
- ↑ Shatsari SS. (1991) Tributes to a Hero of the Masses.Mallam Lawan Dambazau. p.29
.