Jump to content

Martin Odegaard

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Martin Odegaard
Rayuwa
Haihuwa Drammen Municipality (en) Fassara, 17 Disamba 1998 (26 shekaru)
ƙasa Norway
Harshen uwa Norwegian (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Hans Erik Ødegaard
Abokiyar zama Helene Spilling (mul) Fassara  (2024 -
Ma'aurata Helene Spilling (mul) Fassara
Karatu
Harsuna Norwegian (en) Fassara
Turanci
Yaren Sifen
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Norway national under-15 association football team (en) Fassara2013-201320
  Norway national under-16 association football team (en) Fassara2013-201460
Strømsgodset IF (en) Fassara2014-2015235
  Norway national under-17 association football team (en) Fassara2014-201440
  Norway men's national association football team (en) Fassara2014-351
  Norway national under-21 association football team (en) Fassara2014-2018185
  Real Madrid CFga Janairu, 2015-19 ga Augusta, 2021110
SC Heerenveen2017-2018433
SBV Vitesse (en) Fassara2018-20193911
  Real Sociedad (en) Fassara2019-2020367
Arsenal FC2021-2021202
Arsenal FC20 ga Augusta, 2021-unknown value
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Lamban wasa 8
Nauyi 68 kg
Tsayi 178 cm
Imani
Addini Kiristanci
IMDb nm11686908
Odegaard

Martin Odegaard (an haifeshi ranar 17 ga watan Nuwamba, 1998), ya kasance babban dan kwallan ƙasar Norway. Kuma dan wasan tsakiya ne sannan kuma shike da mukamin Captain a duka kungiyoyin guda biyu da kungiyar Arsenal da kuma kungiyar shi ta kasa wato Norway. Sannan kuma yana daya daga cikin manyan yan wasan tsakiya a duniya. An sanshi ne ta dalilin basirar shi, da kuma hikima ta iya fasin.[1][2]

Dan wasan ya fara buga kwallan ƙafa ne yana dan shekara goma sha biyar a shekarar 2014 ya fara buga wasa ne a wata kungiya mai suna Stromsgodset. Sannan ya kafa tarihi na zama dan kwallo mai karancin shekaru da yafi kowa zura kwallo a raga. A shekarar alif 2015, inda akayi cinikin shi da kudi da suka kai darajar £4m inda ya kafa tarihi na zama dan kwallo mafi karancin shekaru a kungiyar. Bayan wasu yan wasanni da yayi, ya ziyarci kungiyoyi da dama a matsayin dan wasan aro inda yaje lig din Eredivisie inda yaje kungiyar Heerenveen da kuma Vitesse. Sai kuma lig din laliga inda yaje real sociedad a matsayin aro daga shekarar alif 2017 zuwa 2019. Dan wasan ya lashe kofin copa del ray a shekarar alif 2019. Bayan nan kuma, ya sake zuwa wani aron, inda yaje kungiyar Arsenal a aro daga bisani kuma kungiyar Arsenal din ta samu nasarar kammala daukarshi a matsayin dan wasanta na dindindin inda aka kammala siyanshi da kudi £30m a shekarar alif 2021.[3]

Bayan yayi kaka mai kyau tare da kungiyar ta Arsenal, an sanar da dan wasan a matsayin kaftin na kungiyar a shekarar 2021.

Dan wasan ya fara wakiltar kasarshi ne a shekarar alif 2014 lokacin yana dan shekara 15, haka zalika ya kafa tarihi na kasancewa dan kwallo mafi karancin shekaru da ya wakilci kasar Norway kuma ya kasance dan wasa mafi karancin shekaru da ya buga gasar Uefa Championship wasannin kwalifayin inda ya ya zama cikakken dan wasan Norway a shekarar 2021.

Rayuwar baya

[gyara sashe | gyara masomin]
Martin Odegaard

An haifi dan wasan 17 Nuwamba, 1998, a garin Drammen, ya kwashe shekarar sa ta farko a wata karamar kungiya "Drammen Strong".[4] Mahaifinsa Hans erik Odegaard, shima ya kasance tsohon mai buga wasan tamaula ne, ya kasance wani bangare na kungiyar kuma koci na yaran nasa a kungiyar. A shekarar 2005, odegaard ya kasance dan shekara shida, lokacin ne yan uwansa suka zuba 50000 domin ya cika musu burukansu na zama babban dan wasa. Odegaard yasha gwagwarmaya kafin ya zama babban dan wasa inda yake shafe tsawon lokaci a filin atisaye.[5]

Rayuwar kwallon baya

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar alif 2019, dan wasan ya jona sansani na matasa a kungiyar Stromsgodset, saidai yana yin atisaye ne da tsofaffin yara. Kwararren dan kwallan Norway din, yakan ziyarci kungiya ta yara masu basira. Sannan dan wasan ya buga wasan shi na farko a kungiyar Buskerud shekarar alif 2010 wanda lokacin ne ya cika da shekara goma sha daya. Inda abokan wasanninsa suka bashi shekaru 2 wasu ma 3. Sai dai bayan kocin ya fahimci hakan, sai ya tafiyar da abubuwa cikin kwarewa da basira. Odegaard yakan yi atisaye duk sati ne tare da wannan kungiya har tsawon shekara ukku 3. Dan wasan ya buga wasa a matsayin dan wasan baya na bangaren hagu, saboda kocin ya fahimci wasu dalilai da ya kamata ya buga wajan saboda zai samu damar taba kwallo sosai kuma zai kware wajan ansar kwallo. Saidai da an gwada shi a gaba da an samu abinda akeso saboda kwanyar sa da kuma basirarshi wanda kocin nashi bai fahimci hakan ba.[6]

Martin Odegaard

A shekarar alif 2011 lokacin yana dan shekara goma sha biyu ya kayatar da tsohon kocinsa sosai Lars Tjaenas lokacin da akayi wasan kasa da kasa ta yan shekaru kasa da goma sha shida U16.

Stroamsgodset

[gyara sashe | gyara masomin]

Odegaard ya fara atisaye ne da babbar kungiyar Stromsgodset a shekarar alif 2012 lokacin yana dan shekara goma sha ukku. Kuma ya fara buga wasa a wannan shekarar tashi ta farko, yayi wasan ne a tsakiyar shekara inda ya buga wasan sada zumunta da kungiyar Mjondalan. Sannan ya samu karamin lokaci na ziyartar wasu wurare atisaye, inda ya zitarci kungiyar Bayern Munich da kuma Manchester United.

A shekarar alif 2013 lokacin yana dan shekara 14, danwasan ya buga ma dukka kungiyoyin Stromsgodset hada masu bi masu wato kannensu mafi yawanci yan shekara 17 da 18 da kuma team din na ukku da kuma na biyar.

A watan junairu shekarar 2014, dan shekara 15 din ya shiga cikin babbar kungiya ta Stromsgodset, a lokacin ya kasance yana daya daga cikin yan wasan Stromsgodset na shekarar, saidai babu wata kwararrar kungiyar da ya sama hannu. A dokar gasar sun zayyana cewa idan har zaka buga wasa a Tippeligaen, dole sai dan wasa nada rijista a matsayin babban dan wasa.

Martin Odegaard

Kasan cewar kungiyar ta saka sunan Odegaard a cikin jerin sunaye na biyu (B) hakan ne yabashi damar buga wasanni ukku a shekarar. Odegaard bai samun damar yin atisaye da kungiyar tashi duk rana saboda yanayin karatu da yakeyi. Kamar yadda akayi yarjejeniya ta yin atisaye sau biyu da marece tare da kungiyar Mjondalen kuma a Lokacin mahaifinsa yana daya daga cikin masu bada horo.

Ya fara buga ma kungiyar Stromsgodset wasa a gasar babban lig inda ya buga wasa da kungiyar hamayya Aalesunds FK a wurin wasa na Marienlyst Stadion a ranar 13 shekarar 2014 lokacin yana dan shekara goma sha biyar 15 da kwanaki 118. Da wasan yakasance dan wasa mafi karancin shekaru daya buga wasa a Tippelingaen. A ranar 5 ga watan May, ya cike kwantiragi a matsayin kwararren dan wasa a kungiyar ta Stromsgodset inda kwantiragin zai kare a shekarar alif 2015. Wannan shi yasa aka cire dokar buga wasanni ukku duk shekara. Kwanaki goma sha daya da suka wuce, yaci kwallo ta farko a matsayinshi na dan wasa mai kwarewa kuma ya zama gwarzon mai jefa kwallo a raga a Tippelingaen lokacin da ya zura kwallo ta hudu inda kungiyar ta samu nasara da ci 4-1 a wasan da suka buga da Sarpsborg. Ya fara buga wasa a gasar turai a 16 ga wata juli inda ya canji dan wasa mai suna lars Christopher vilsvik a karshen mintina biyar inda sukasha kashi da ci daya mai ban haushi 1-0 a hannun Steaua București a gasar kofin zakarun nahirar turai a wasan tsallakewa na biyu.

A juli din da ya wuce, wasan waje da sukayi da Sandnes Ulf, ya bada damar tattaunawa mai ma'ana a jaridu. Dan wasan ya bada gudummawa wajan zura kwallo ga kungiyar shi inda ya zura kwallo kuma ya taimaka aka zura kwallo a raga. Kuma an harbe shi a cikin gidan abokan hamayyarsu inda alkalin wasa ya bada bugun daga kai sai mai tsaron raga, sai dai ansamu rashin sa'a saboda an barar da kwallon daga abokin wasanshi. Saboda kwazon da yayi, dan kwallon ya samu karbuwa sosai inda aka yanke shawar ya asanyashi cikin wadanda zasu buga wasanni da manyan kasashe na nahiyar turai. Tsohon mai bada horo na kasar Norway Nills Jorhan Semb yace bayan wasan da aka buga, dan wasan shine dan shekara 15 din da yafi kowane dan shekara 15 kyau sannan ya kara da cewa dan wasan kada yayi sauri wajan cewa zai wakilci babbar kungiya ta kasa. Sai dai a Lokacin dan wasan yace inda za'a tambayeshi ko yanaso ya wakilci babbar kungiya ta kasa? To da amsar daze bayar itace ehh! A wasan waje da suka fafata da kungiyar Ik Start a ranar 15 ga watan Ogusta a cikin shekarar, yana buga wasa ne a matsayin dan kwallon gefe na hagu inda ya taimaka aka zura kwallaye guda 3 a kungiyarshi ta stromsgodset a wasan da aka samu nasara daci 3-2. Yaci kwallo biyu a wasan shi na farko matsayin kwararren dan wasa inda suka lallasa kungiyar lillestrome SK daci 2-1 a ranar goma sha tara 19 ga watan Oktoba. Kungiyar stromsgodset ta gama a mataki na 4 a gasar lig hakan ne ya basu damar tsallakewa domin buga gasar zakarun turai a karon farko. Odegaard ya zura kwallo biyar 5 acikin wasanni 23 kuma ya bada gudummawa anci kwallo 7 a gasar lig da suka buga. A watan Disamba shekarar alif 2014, karshen season din Norway, yayi atisaye da manyan kugiyoyi na nahiyar turai, yayi atisaye da babbar kungiya ta Bayern Munich, Liverpool, daga bisani ya ziyarci wajan atisaye na Arsenal Colney.[7][8]

Real madrid

[gyara sashe | gyara masomin]

Yaje kungiyar a shekarar 2015 zuwa 2017.

A ranar ashirin da daya 21 shekarar alif 2015 kungiyar Real madrid ta samu nasarar cimma yarjejeniya da dan wasan daga kungiyar Stromsgodset bayan yayi atisaye da kungiyar na watannin baya. Kafafen sadarwa na Sifaniya sun ruwaito cewa kudin yarjejeniya ta siyan dan wasan kudine da suka kai darajar £3 miliyan. Haka zalika kafar sadarwa ta kasar Norway itama ta ruwaito cewa an dauki dan wasan ne a kudi da suka kai darajar £35 miliyan kroner. A jimlace kudin sun kama £4 miliyan wanda zasu iya yakai £75 miliyan kroner. A jimlace kuma zai iya kaiwa 8 zuwa 8.5 miliyan a wata yarjejeniya bayan ansa hannu a kungiyar Real madrid inda aka cimma matsaya cewa dan wasan zai buga ma babbar kungiya da kuma karamar kungiya ta Real Madrid. Zai buga wasa da kungiyar inda zinedine zidane ke jagoranta a lokacin.[9]

Ya fara buga wasa a kungiyar Real madrid inda ya fito cikin masu jira wato benci a ranar 4 ga watan Fabrairu a wasan sada zumunta da kungiyar ta buga da Baijin Gusan inda wasan ya tashi canjaras 3-3. Haka zalika dan wasan ya samu nasarar shiga cikin babbar kungiya kuma sunanshi ya fito cikin wadanda zasu buga gasar zakarun nahiyar turai. Anba dan wasan lamba 21 wadda zai dinga sakawa yayin doka wasanni. Bayyanarshi a Castilla yazo ne a ranar takwas 8 ga watan Fabrairu inda ya shigo a matsayin dan benci a wasan sada zumunta da kungiyar ta buga da kungiyar Atletico Bilbao yayin da wasan ya tashi canjaras daci biyu da biyu 2-2 a Segunda Division B. A ranar ashirin da daya 21 ga watan Fabrairu, yacima kungiyar Real madrid kwallo ta farko a wasa da suka buda da Barakaldo Cf inda wasan ya tashi hudu da nema 4-0 a filin wasa na Alfredo S Stepano stadium kuma shine ya bude raga da kwallon farko da ya zura cikin mintina 7 da farawa.

A watan Afrilu, an ajiye dan wasan a matsayin benci a Castilla bayan rashin nasara da suka samu sau hudu 4 inda suka fara samun matsaloli da masu ruwa da tsaki na kungiyar inda ya dinga zama a benci kuma alhali yana atisaye da babbar kungiya, duk da dai hada karin bambancin yare. Mai horar da babbar kungiyar wato Carlo Ancelotti yayi kira ga masu goyon bayan kungiyar dasu kara yin hakuri da dan wasan, saboda yana sabawa ne a hankali da yanayin canjin kasa da kuma sabuwar kungiyar sa.

A ranar 26 ga watan aprilu, an sanya shi cikin jerin yan wasa da zasu gwabza wasan a gida, wannan shine karo na farko da ya shiga a gasar Laliga wasan da aka buga da Ud Almeria inda kocin Real madrid wato Ancelotti ya fito wasan babu wasu zaratan yan kwallan shi na 11 din farko. Daga cikin yan wasan babu Gareth bale, luka modric, da kuma karim Benzema. Saidai kuma duk da hakan kungiyar ta samu nasara daci 3-0.

A ranar 23 ga watan May, a wasan karshe da akayi a shekarar ya buga wasa inda aka sakoshi a minti na 58 inda ya anshi wanda ya zura kwallayen uku duka a raga kuma gwarzon dan wasa mai kwarewa wanda a shekarar ma shine mafi kyawun dan wasa a duniya, kuma FIFA ta girmama shi da kyautar Ballon d o a shekarar wato Cristiano Ronaldo. Ya zama shine dan wasa na farko mai karancin shekaru a kungiyar Real madrid da shekaru 16 da kuma kwanaki 157 na haihuwa.

Odegaard ya zama mai buga wasa a koda yaushe a Castilla shekarar 2015-16.

A ranar 17 ga watan Aprilu, 2016 an yabeshi a Diario As saboda kokarin da yayi a wasan gida da aka buga inda aka samu nasara daci 3-0 da kungiyar SD Gernika club har ya samo bugun daga kai sai mai tsaron raga wanda Mariano ya buga kuma yaci kwallan. Kuma wannan nasarar tasa kungiyar ta hau bisa teburi. Kungiyar ta samu nasarar zama saman guruf din inda ta haye kungiyar Bakaldo CF a rana ta karshe inda dan wasan ya samu damar jefa kwallo a raga inda suka lallasa kungiyar La roda CF da ci 6-1

Odegaard ya fara wasanshi na farko a kungiyar Real madrid a ranar 30 Nuwamba 2016 kwanaki 679 bayan kammala sa hannu a kungiyar, ya buga mintina casa'in rass a wasan insa suka lallasa kungiyar cultural leonesa daci 6-1 a gasar copa del ray.[10]

2017 - 2020 zaman aro a kasar Netherland da kuma Spain

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 10 ga watan Junairu 2017 club din dutch SC Heerenveen suka wallafa cewa dan wasan ya jona su da yarjejeniyar watanni 18 a zaman aro. A Lokacin ya kusa kulla yarjejeniya da Barcelona a yanda mai kula da cinikinsa ya fada, sai dai a Lokacin aka hukunta kungiyar tashi daga cinikin yan wasa saboda wani laifi dasuka aikata. Ya fara buga gasar eridivisie kwanaki hudu baya inda suka samu nasara daci 2-0 a wasan gida da suka buga da odo den haag inda ya canji arba zanelli a mintuna na karshe. Bayan wasan ya tattauna da jaridar fox sport akan ficewar sa a sabon wurin da yake, wasannin sa na farko a heerenveen basuyi kyau ba inda ya buga kwallo gaban mai tsaron raga sau daya sai kuma ya taimaka akaci kwallo sau daya cikin wasanni bakwai da ya buga tare da kungiyar. Daga baya kuma aka dinga canja shi sannan kuma mai bada rohon mai suna Jurgen steppel ya meda dan wasan benci. Yaci kwallan shi ta farko ga frissians a ranar goma sha takwas ga watan Mayu a cikin wasanni goma sha biyar da ya buga. A rashin nasara da suka samu a gida inda Kungiyar ultretch ta lallasa su daci 3-1 a wasan farko na kusa da wasan karshe, sai dai wasan ya kare da jumillar kwallaye 5-2.[11]

A shekarar alif dubu biyu da goma sha bakwai 2017 zuwa shekarar alif dubu biyu da goma sha takwas 2018 dan wasan ya zama mai buga wasa kullum wato cikin sha dayan farko inda yaci kwallan shi ta farko a kungiyar heerenveen din a wasan da suka samu nasara daci 4-0 inda suka lallasa kungiyar F. C Twente a ranar goma sha takwas ga watan Nuwamba shekarar alif 2017.

A ranar ashirin da daya ga watan Ogusta, shekarar alif dubu biyu da goma sha takwas 2018 kugiyar tashi ta Real Madrid tayi sanarwa cewa dan wasan zai kara tafiya wani zaman aron a kakar 2018 zuwa 2019 inda ya koma wata kungiyar ta Eridivisie SBV vitesse inda ya kokarta yaci kwallaye guda goma sha daya 11 kuma ya taimaka akaci kwallaye goma sha biyu 12. Bayan wannan muhimmiyar rawa da ya taka, dan wasan yasamu karbuwa ga magoya bayan kungiyar harma suka zabe shi a matsayin dan kwallan da yafi kowa a shekarar.

A ranar biyar 5 ga watan July, shekarar alif dubu biyu da goma sha tara 2019 yaje zaman aro a Real sociedad inda ya shafe shekara daya kacal inda kungiyar ta Real Madrid din ta yanke shawarar dawowa da dan wasan ya dawo gida domin ya karasa sauran kwanakin aron da suka rage masa.

A ranar ashirin da biyar ga watan Ogusta, yaci kwallan sa ta farko a gasar laliga a wasan da suka kece raini da mallorca inda suka samu nasara daci daya mai ban haushi a filin wasa na estadi mallorca san moix.

A ranar sha hudu ga watan September, yaci kwallan shi ta biyu a wasan gida da suka fafata da kungiyar hamayya kuma babban wasa a garin madrid da kungiyar Atletico Madrid inda sukayi musu wankan jego daci biyu da nema 2-0 inda ya taka rawar gani sosai inda ya amshi kyautar wanda wafi kowa kokari a wasan.[12]

Ya taimaka an jefa kwallo a raga ne na karon farko inda ya jefa ma abokin wasan sa kwallo daga yadi na ashirin zuwa kafar abokin wasan nasa mai suna Mikel Oyarzabal a gaban fellow basques na Deportivo Alaves yayinda magoya baya sukayi ta yabonsa saboda abin a yaba da yayi da kuma nuna bajinta da kuma basira da Allah ya hore masa. A watan September, shekarar alif dubu biyu da goma sha tara 2019, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da yafi kowane dan wasa kyau na watan a gasar ta Laliga.

A watan Fabrairu, shekarar 2020 ya zura ma kungiyar Real Madrid kwallo a ragarsu domin ya taimaka ma kungiyar da yake zaman aro domin ta samu damar fitar da Kungiyar tasa ta asali daga gasar Copa del ray a shekarar 2019-2020 matakin kusa da na kusa da karshe.[13].

Zaman aro na 2020-21

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan da ya buga wasanni tara kacal a lokacin farkon kakar wasa ta Real Madrid bayan zaman aro a Real Sociedad, Ødegaard ya bayyana karara cewa yana son barin kungiyar a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a lokacin hunturu don neman kwallon kafa na farko. A ranar 27 ga Janairu 2021, Ødegaard ya koma kulob din Arsenal na Premier a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa. Ya yaba da jagorancin kulob din da kuma salon wasan, inda ya yanke shawarar cewa Arsenal za ta zama "kungiyar da ta dace da ni sosai." zabin da kuma cewa kowa a kulob din ya yi farin cikin shigar da shi cikin tsare-tsaren Arsenal.[14]

Kwanaki uku bayan ya sanya hannu, ya fara buga wasansa na farko da abokan hamayyarsa Manchester United a gasar Premier, inda ya maye gurbin Emile Smith Rowe a wasan da suka tashi 0-0 a gida. A ranar 14 ga Fabrairu, ya fara buga gasarsa ta farko ga Arsenal a wasan da suka doke Leeds United da ci 4–2 a gida. A ranar 11 ga Maris, Ødegaard ya ci wa Arsenal kwallonsa ta farko da yadi 20 a wasan da suka doke Olympiacos da ci 3-1 a waje a wasan farko na zagaye na 16 na gasar Europa. Daga baya an zabi wannan burin a matsayin Goal na Arsenal na wata. A ranar 14 ga Maris, Ødegaard ya zura kwallo a wasannin baya-baya, inda ya ci kwallonsa ta farko a gasar Premier a wasan da Arsenal ta doke Tottenham da ci 2-1 a gida a wasan 203 na Arewacin London. An zabi Ødegaard a matsayin Gwarzon dan wasan Arsenal na watan Maris 2021.[15]

2021-yanzu: Canja sheka na dindindin da Zama kyaftin na kulob

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 20 ga Agusta 2021, Arsenal ta ba da sanarwar sanya hannu na dindindin na Ødegaard a cikin yarjejeniyar da ta kai Yuro miliyan 35 tare da yuwuwar ƙarin abubuwan da za su haura kusan Yuro miliyan 40. Ødegaard ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru hudu har zuwa 2025 tare da kulob din yana da zabin tsawaita shekara ta biyar. Zai buga wasansa na farko a kakar wasan da suka doke Manchester City da ci 5-0 a waje. Ya ci kwallonsa ta farko a kakar wasa ta bana da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da suka doke Burnley da ci 1-0, abin da ya baiwa Arsenal nasara a jere. A ranar 18 ga Disamba, Ødegaard ya sami taimakonsa na farko na kakar wasa a wasan da suka doke Leeds da ci 4–1. Ya kare watan ne da kwallaye uku da ci uku a wasanni shida, kuma an zabe shi a matsayin gwarzon dan wasan Premier na watan. A karshen kakar wasa ta bana, Arsenal ta kammala gasar Premier a matsayi na biyar, bayan da ta rasa buga gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa ta gaba.[16]

A ranar 11 ga Fabrairu 2024, a wasan da suka ci West Ham 6-0 a waje, Ødegaard ya zama dan wasa na farko da aka yi rikodin tun 2003 – 04 don kammala wucewa 100+ (107), ya haifar da aƙalla dama biyar (7), kuma ya taimaka maƙalai da yawa ( 2) a gasar Premier guda daya. A ranar 12 ga Maris, ya taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar Arsenal da ci 1-1 a kan agg., 4–2 a bugun fenariti a kan Porto, ya ba da taimako ga bugun daga kai sai mai tsaron gida da Arsenal ta yi a bugun daga kai sai mai tsaron gida. -na karshe a karon farko cikin shekaru 14. A ranar 23 ga Afrilu, Ødegaard ya taka rawar gani a nasarar gida da ci 5-0 a kan Chelsea, yana taimakawa kwallaye na uku da na biyar, kuma ya zama dan wasa na farko na Arsenal tun Mesut Ozil da ya haifar da damammaki takwas daga bude-bakin wasa a wasan Premier. Ya ƙare kakar wasa a matsayin ɗan wasan da ke da mafi yawan damar da aka ƙirƙira daga buɗe wasa a cikin 2023–24 Premier League kakar, tare da 88. An tabbatar da Ødegaard a matsayin gwarzon dan wasan Arsenal bayan karshen kakar wasa ta bana, inda ya lashe kyautar a karo na biyu a jere.[17]

martin
martin
  1. "10 Best Midfielders In The World Right Now In 2023". 1SPORTS1. 2 July 2023. Retrieved 31 July 2023.
  2. Ajith, Shambhu (23 July 2023). "5 best midfielders in world football right now". Sportskeeda. Retrieved 31 July 2023.
  3. "Martin Odegaard named as Norway captain at just 22 years-old". Just Arsenal News. 13 March 2021. Archived from the original on 7 November 2022. Retrieved 7 November 2022
  4. "Acta del Partido celebrado el 23 de mayo de 2015, en Madrid" [Minutes of the Match held on 23 May 2015, in Madrid] (in Spanish). Royal Spanish Football Federation. Archived from the original on 17 April 2023. Retrieved 6 August 2019.
  5. "Drammen Strong ecstatic over hundreds of thousands from Martin Ødegaard". Drammens Tidende (in Norwegian). Edda Media. 29 January 2015. Archived from the original on 2 February 2015. Retrieved 6 February 2015.
  6. Drammen Strong ecstatic over hundreds of thousands from Martin Ødegaard". Drammens Tidende (in Norwegian). Edda Media. 29 January 2015. Archived from the original on 2 February 2015. Retrieved 6 February 2015.
  7. "Dobbel opptur for Ødegaard" [Twice the luck for Ødegaard]. Drammens Tidende (in Norwegian). 17 January 2014. Archived from the original on 12 October 2014. Retrieved 17 January 2014.
  8. Ødegaard besøkte Arsenal i dag" [Ødegaard visited Arsenal today]. Verdens Gang (in Norwegian). 16 December 2014. Archived from the original on 8 February 2015. Retrieved 9 February 2015. Martin Ødegaard (16 tomorrow) spent the last day of his 15th year on a visit to Arsenal.
  9. Martin Odegaard: Teenager completes Real Madrid move". BBC Sport. 22 January 2015. Archived from the original on 29 January 2015. Retrieved 9 February 2015.
  10. Victor, Tom (30 November 2020). "Martin Ødegaard makes his full Real Madrid debut almost *2 years* after signing". Sports Joe. Archived from the original on 29 August 2022. Retrieved 29 August 2022.
  11. Video: Martin Odegaard finally scores first goal for Eredivisie club Heerenveen". FourFourTwo. 18 May 2017. Archived from the original on 9 September 2017. Retrieved 8 September 2017
  12. "Martin Ødegaard, September Player of the Month in LaLiga Santander". La Liga. 4 October 2019. Archived from the original on 9 October 2019. Retrieved 4 October 2019.
  13. "Internazionale 0–2 Real Madrid". UEFA. 25 November 2020. Archived from the original on 27 November 2020. Retrieved 26 November 2020.
  14. "Martin Odegaard transfer: Arsenal sign Real Madrid midfielder on loan until the end of the season". Sky Sports. 27 January 2021. Archived from the original on 13 January 2023. Retrieved
  15. Odegaard is our March Player of the Month". Arsenal F.C. Archived from the original on 1 April 2021. Retrieved 1 April 2021.
  16. de Roché, Art (24 May 2022). "Arsenal 2021–22 season review: Top-class Tomiyasu, erratic form and the beauty of team goals". The Athletic. Archived from the original on 24 August 2022. Retrieved 24 August 2022.
  17. Odegaard retains men's Player of the Season award". Odegaard retains men's Player of the Season award. 28 July 2024. Retrieved 26 July 2024.