Jump to content

Masallacin Camlica

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masallacin Camlica
Çamlıca Camii
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaTurkiyya
Province of Turkey (en) FassaraIstanbul Province (en) Fassara
District of Turkey (en) FassaraÜsküdar (en) Fassara
Coordinates 41°02′N 29°04′E / 41.03°N 29.07°E / 41.03; 29.07
Map
History and use
Foundation stone laying ceremony 2013
Ƙaddamarwa7 ga Maris, 2019
Addini Mabiya Sunnah
Maximum capacity (en) Fassara 63,000
Karatun Gine-gine
Style (en) Fassara Ottoman architecture (en) Fassara
Tsawo 107.1 m
Parts Hasumiya: 6
Offical website
Masallacin Camlica

Masallacin Camlica ko (Çamlica Mosque a harshen Turkanci) wani Masallaci ne a birnin Istanbul na kasar Turkiya. Masallacin zai dauki masallata 63,000 kuma akwai bangaren wurin kayan tarihi na Musulunci, ma'ajiyar Zane-zane, dakin karatu, dakin taro, da filin ajiye ababen hawa na karkashin kasa wanda zai iya daukar ababen hawa 3500.[1]

Wasu mata masu zane ne su biyu Bahar Mızrak da Hayriye Gül Totu, suka zana masallacin akan kudin turkiya TL Miliyan 150 (dalar Amurika miliyar $66.5 ). Masallacin yana daya daga cikin manyan aiyuka da gwamnatin kasar Turkiya ta yi domin ta nuna ma duniya irin karfin tattalin arziki da wadatar kasar da kuma daukaka jam'iyya mai mulki ta AK Party.

An bude masallacin a ranar 4 ga watan Mayu 2019 ta hanyar jagorancin shugaba Recep Tayyip Erdoğan na Turkiya. Shugabannin kasashen duniya da wakilai da dama ne suka samu hallara a wajen bikin bude masallacin kamar Shugaban Senegal Macky Sall da na Gine Alpha Conde da na Albaniya Illir Meta da firaministan Falasdinu Muhammad Shtayyeh.

Kayatattun hotuna na wasu sassan masallacin

  1. "Turkey's largest mosque opens its doors in Istanbul". Gulf Times. Istanbul. DPA. Retrieved 5 May 2019.