Mohammad Bin Salman Al Saud ( Larabci: محمد بن سلمان بن عبد العزيز آل سعود ; an haife shi a ranar 31 ga watan Agusta shekara ta alif 1985) shi ne Yariman Masarautar Saudiyya, Mataimakin Firayim Minista na farko na Saudi Arabia kuma shi ne ƙaramin Ministan tsaro a duniya.
Mohammad kuma shine shugaban gidan masarautar gidan Saud, kuma shugaban majalisar harkokin tattalin arziki da ci gaba. An bayyana shi a matsayin mai iko a bayan kursiyin mahaifinsa, Sarki Salman . [1]
An nada Mohammad a matsayin Yarima mai jiran gado a watan Yunin 2017 bayan shawarar da ta yanke daga Muhammad bin Nayef don cire kansa daga dukkan mukamai, wanda ya sa Mohammad ya zama magajin sarauta.
A watan Oktoban 2018, Mohammad ya samu kururuwa a duniya saboda zargin da ake yi masa cewa yana da hannu a kisan dan jaridar The Washington Post dinJamal Khashoggi amma wanda ke da alhakin kisan Jamal Khashoggi yana gidan yari.