Jump to content

Nura M Inuwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nura M Inuwa
Rayuwa
Haihuwa Dala, Nigeria, 18 Satumba 1989 (34 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mawaƙi
Imani
Addini Musulunci

Nura Musa Inuwa, Ana kiran shi da Nura ko kuma M inuwa, An haife shi ne a ranar 18 ga watan satumba shekara ta alif dari tara da tamanin da tara 1989, a cikin garin Kano, a cikin garin Gwammaja a karamar hukumar Dala.[1][2] ya kasance mawakin hausa, mai rubuta wake, kuma furodusan fim a masana'antar Kannywood. Nura m inuwa Mawakine mai hikima gamida azanci.

Wakoki[gyara sashe | gyara masomin]

Aisha humaira, Rai-dai, Badi ba rai, Soyayyar facebook, Sayyada, Mijin biza, Abinda yake Ruhi, Alkuki, Yan kudu, Zurfin ciki, Soyayyace, Faggen soyayya, inka iya zance, Ga wuri ga waina, Ummi, Uwar mugu Babban gida, Dan gwamna, Manyan mata, Hubbi, Matan zamani, Dan baiwa, Basaja, Zurfin ciki, Abbana, Alkawari, Dawo dawo, Wata ruga, Yar fulani, Salma, Mai gadan zinari, Labarina, Yan arewa, Duniyar masoya, Mailaya, In ka'iya zance, Daren Alkhairi Soyyayya Ruwan zuma, Uwar Amarya Nabiyo Haske Matan Gida.[3]

Kambu da Lamban Girma[gyara sashe | gyara masomin]

Kundin Wakoki[gyara sashe | gyara masomin]

  • Rigar aro
  • Wasika
  • Dan magori
  • Makashinka
  • Afra
  • Siyan baki
  • Matan gida
  • Soyayya
  • Ranar aurena
  • Ma'aurata.
  • Mai sauraro
  • Ni daku
  • Lokaci
  • Ango da sauransu.

Daukakar Sa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara waka a shekarar 2007 ya fara ne da wakar siyasa amma nasararsa tafara ne daga shekarar 2010.

Mawakin nayin salon wakokin siyasa, aure, zauranci, soyayya da kuma wakokin finafinan shirin kannywood.

Wasu wadanda ba asan ko suwayeba Sun wasa masa ruwan acid a shekarar 2012.

Nura yayi waka tare mawaka dayawa kamarsu Umar m sharrit, Billio, Ali show dade sauransu sanan a wakarsu ta siyasa a shekarar 2015 yayi hadaka da mawakan siyasa na arewa Irinsu Rara, Aminu ala, hussaini danko, Adam a Zango, Ali jita, Nazifi Asnanik, Dade sauransu. Kawo yanzu mawakin Yayi wakoki da suka Kai 550 wacce yafiso itace rigar aro.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-08-30. Retrieved 2019-12-23.
 2. https://hausa.legit.ng/amp/1101084-dandalin-kannywood-shahararren-mawaki-nura-m-inuwa-zai-angwance.html&ved=2ahUKEwj7h9D3kcbmAhUCyxoKHfDWDoAQFjAMegQICBAB&usg=AOvVaw0BbJrtsWq7_JXNBurrsPNA&ampcf=1[permanent dead link]
 3. https://www.bbc.com/hausa/amp/labarai-46693772&ved=2ahUKEwj7h9D3kcbmAhUCyxoKHfDWDoAQFjAKegQIBBAB&usg=AOvVaw3iEVIXZHda-89PFwZ1Rsvr&ampcf=1[permanent dead link]