Jump to content

Nurain Muhammad Siddiq

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nurain Muhammad Siddiq
Rayuwa
Haihuwa Umm Dam (en) Fassara da Q101247447 Fassara, 1982
ƙasa Sudan
Mutuwa Khartoum, 7 Nuwamba, 2020
Yanayin mutuwa accidental death (en) Fassara (traffic collision (en) Fassara)
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a qāriʾ (en) Fassara da Liman
Imani
Addini Musulunci
surahquran.com…

Nurain Muhammad Saddiq (Ana kuma kiransa da Nurain, Nurein, Ana kuma kiransa da Saddique) (an haife shi a shekarar 1982, ya rasu ranar 7 ga watan Nuwamba shekarar 2020) babban Liman ne a kasar Sudan, an kuma sanshi ne ta hanyar kwarewar sa da karatun Alqur'ani mai girma da kuma Qira'a mai dadi gami da ratsa zuciya. Liman ne a masallacin Kartum da sauran Masallatu a cikin birnin Sudan, da Kartum.

Ya mutu a hadarin mota yana da shekaru 38.

Alamma Nurain yana da mata hudu da ’ya’ya takwas, maza da mata, babbar yarinyar sa mace ce.

Tarihin Rayuwar sa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Siddiq a shekara ta 1982 a wani gari mai suna Farajab na kasar Sudan. A shekarar 1998 ya shiga makarantar khalwa a khorsi sannan ya zama dalibin fitaccen malamin nan Sheikh Makki a kasar Sudan. Bayan kammala karatunsa, ya ci gaba da karatunsa na Musulunci a Khorsi, inda ya shafe shekaru 20 yana neman ilimi a karkashin malamai daban-daban. Daga baya ya zama almajirin Sheikh Makki a Khartoum babban birnin kasar Sudan. [1] An haifi Siddiq a unguwar Umm Dam a Arewacin Kordofan kuma ya girma a cikin gida mai iyali oai wanda yake a karkahin kulawar iyalin sa. Yana dan shekara 17 ya haddace Al-Qur'ani a cikin Qira'at Al-Douri'an Abi 'Amr da Hafs. Daga nan ya shiga jami’ar Qur'ani mai tsarki ta Musulunci, inda ya kammala. [1] Siddiq ya halarci gasannin Qur'ani na kasa da kasa da dama, musamman a kasashen Malaysia, Dubai, Saudi Arabia, da Libya .

Siddiq ya samu karbuwa a fadin duniyar musulmi ta hanyar bidiyoyin karatunsa a shafukan sada zumunta. Bidiyoyin Siddiq da yawa sun tattara miliyoyin ra'ayoyi akan kafar sada zumunta ta YouTube .

A ranar 7 ga Nuwamba, 2020, Siddiq ya mutu a wani hatsarin mota a Khartoum yana da shekaru 38. Sauran abokan tafiyar sa u 3, wadanda suma Hafizai ne sun mutu a wannan hadarin: Ali Yaqoub, Abdullah Awad Al-Karim, da Muhannad Al-Kinani. Sai kuma Sayed bin Omar wanda shi rauni kawai yaji a hatsarin motar..Akwai tazarar kilomita 18 tsakaninu da Omdurman lokacin suna dawowa daga Wadi Halfa lokacin da motar tasu ta yi karo da babbar mota. Bayan rasuwara labarin ya karade hafukan ada zumunta

Salon karatun

[gyara sashe | gyara masomin]

An bayyana Qira'ar Siddiq a matsayin abin tauayi, mai sanya nutuwa. Sautinsa na musamman ya sa ya zama mashahurin Alaramma a duniyar musulmi. Karatun Siddiq ya yi kama da ma'aunin rubutu biyar ko pentatonic wanda ya zama ruwan dare a yankunan da musulmi ke da rinjaye na Sahel da kuma yankin tsakiyar Afirka.

Bayan rasuwarsa, Omar Suleiman ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa "Duniya ta rasa daya daga cikin mafi dadin karatu [muryoyin] a zamaninmu."

Hind Makki, wata jami'ar koyar da addinin musulunci 'yar Sudan da Amurka ta ce game da karatun Siddiq na cewa "Akwai sahihancin Afirka da mutane ke nunawa ko da ba za su iya bayyana ainihin abin da yake ba kuma suna son sa," in ji ta.

Siddiq ya iya karantawa a cikin qira'at na Al Douri'an Abi 'Amr da Hafs .

  1. 1.0 1.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :02