Ofishin Binciken Tsaron Najeriya
Ofishin Binciken Tsaron Najeriya | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | government agency (en) da accident investigation agency (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Mulki | |
Hedkwata | Abuja, Lagos, da Ikeja |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2006 |
nsib.gov.ng |
Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya (NSIB), wacce a da ita ce Hukumar Binciken Hatsari (AIB),[1] tana binciken hadurran jiragen sama da abubuwan da suka faru a Najeriya. Tana da hedikwata a harabar filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja. [2]
Hukumar ta kai rahoto ga Shugaban Najeriya ta hannun Ministan Sufurin Jiragen Sama na Tarayya. Kwamishinan hukumar, wanda kuma shine babban jami’in gudanarwa shine Engr. Akin Olateru.
A watan Satumban, 2020, Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da kafa makarantar horar da AIB a Najeriya.[3]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]A baya ma’aikatar sufurin jiragen sama ta yi bincike kan haɗurran jiragen. A cikin shekarar 1989, an kafa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya (FCAA), kuma Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama ta MOA ta zama Sashen Sabis na Tsaro na FCAA. A cikin wannan shekarar an kafa Ofishin Binciken Hatsari (AIB), wanda ke ƙarƙashin Ma'aikatar Jiragen Sama, kuma FCAA ba ta da alhakin binciken haɗari. Daga baya an canza sunan ofishin zuwa Ofishin Bincike da Rigakafin Hatsari. A matsayin wani ɓangare na Dokar Jirgin Sama na 2006, AIB ta zama hukuma mai cin gashin kanta kuma ta sake suna Ofishin Binciken Hatsari.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "NSIB, NIGERIAN NAVY SIGN AGREEMENT ON TRANSPORTATION SAFETY". Nigerian Safety Investigation Bureau. 2022-12-21. Retrieved 2023-07-09.
[...]the NSIB, formerly known as Accident Investigation Bureau (AIB),[...]
[permanent dead link] - ↑ "Home Error in Webarchive template: Empty url.." Accident Investigation Bureau. Retrieved on 4 November 2011. "HEAD OFFICE Nnamdi Azikiwe International Airport".
- ↑ "FG Approves AIB Training School–Bureau Commissioner". Geeky Nigeria. 2020-09-05. Retrieved 2020-09-06.
- ↑ " About AIB Archived January 3, 2012, at the Wayback Machine." Accident Investigation Bureau. Retrieved on 26 February 2012.
Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]