Jump to content

Olu Maintain

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Olu Maintain
Rayuwa
Haihuwa Lagos,, Satumba 1976 (48 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mai rubuta waka

Olumide Edwards Adegbulu (an haife shi a watan Satumbar shekarar 1976), anfi saninsa da sunan Olu Maintain (wani lokaci ana kiransa Mista Yahooze ), mawaƙin kasar Najeriya ne. Shi ne ya kafa ƙungiyar kaɗe-kaɗe da aka fi sani da Maintain, tare da dan uwansa, Tolu Ogunniyi. Adeboye Bammeke, wanda aka fi sani da Big Bamo, ya shiga ƙungiyar, wadda ta fitar da albam guda shida tsakanin shekarar 1998 zuwa shekarar 2004 tare da fitattun wakokin albam ɗin "I Catch Cold", "Domitila" da "Alo" kafin su rabu a shekarar 2004.[1][2]

Olu ya yi fice a watan Mayun shekarar 2007 tare da fitar da waƙar " Yahooze " wanda a zahiri ya ya kashe kuɗi mai yawa daga kundin na farko na studio, Yahooze (2007), da albam na biyu, Maintain Reloaded (2008). Ya yi haɗin-gwiwa da Big Bamo a cikin waƙar "Kowonje". Wakar "Yahooze" ce Mafi Zafafa ta Shekara a Kyautar Nishadantarwa ta Najeriya.[3]

A shekarar 2008, ya yi wasa a dandalin Royal Albert Hall, London inda yayi amfani da wakar ta "Yahooze", kuma ya gayyato Colin Powell, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka a lokacin.[4]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a watan Satumbar shekarar 1976 a jihar Legas, yammacin Najeriya, amma ya fito daga jihar Ondo, kudu maso yammacin Najeriya. Iyayensa likitoci ne; mahaifinsa likita ne, mahaifiyarsa kuma ma'aikaciyar jinya ce.[5]

A shekarar 2001, ya sami satifiket na shaidar difloma a fannin lissafi daga Kwalejin Kimiyya da fasaha ta The Polytechnic, Ibadan, amma ya fara aikin waka a shekarar 1997. A wannan shekarar, ya saki kundin sa na farko, Domitila. An fitar da waƙar a watan Oktobar shekarar 1998.[6]

A ranar 27 ga watan Yulin,shekarar 2009, ya fito da kundin waka, mai taken: tWith All Due Respect, Press Play, cikin albam ɗin ya ƙunshi wakar "What a Man Can Do" wadda yayi haɗin-gwiwa tare da Kentro World.[7]

A cikin watan Janairun 2012, ya saki waka ɗaya, " Nawti ", wanda ya sami lambar yabo ta Najeriya Nishaɗi don Mafi kyawun Bidiyo na Shekara da Mafi kyawun Bidiyon Reggae/Dancehall na Shekara a Kyautar Bidiyon Waƙoƙin Najeriya.[8] A ranar 4 ga watan Janairun, shekarar 2013, ya fito da waƙoƙi guda biyu, masu taken " Hypnotize Me ", haɗin-gwiwa tare da 50 Cent da mawaƙiya Olivia, sai "Oya Dancia", haɗin-gwiwa tare da mawaƙi Fatman Scoop.[9]

Jadawalin Wakoki

[gyara sashe | gyara masomin]
Kundin waƙoƙi
  • Olu Maintain (2017)
Mai waka ɗaya

Kyaututtuka da zaɓe

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Fading groups on Nigeria's music scene". The Punch – Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 27 May 2012. Retrieved 15 June 2015.
  2. "You don't see me often because I'm a legend – Olu Maintain – Vanguard News". Vanguard News. 3 April 2015. Retrieved 15 June 2015.
  3. "Sex is like breathing – Olu Maintain – Vanguard News". Vanguard News. 20 February 2015. Retrieved 15 June 2015.
  4. "Save the last dance". The Punch – Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 4 July 2012. Retrieved 15 June 2015.
  5. "Why I abandoned my newly bought house for a hotel -----Olu Maintain". Modern Ghana. Retrieved 15 June 2015.
  6. "Nigeria's music industry making global impact, says Olu Maintain – Vanguard News". Vanguard News. 20 May 2014. Retrieved 15 June 2015.
  7. "Olu Maintain drops new single "What a man can do" – Vanguard News". Vanguard News. 12 July 2009. Retrieved 15 June 2015.
  8. "Olu Maintain drops 2 new-year singles". Vanguard News. 4 January 2013. Retrieved 15 June 2015.
  9. "Olu Maintain: My Collabo With 50 Cent, Articles – THISDAY LIVE". thisdaylive.com. Archived from the original on 18 May 2013. Retrieved 15 June 2015.
  10. "New Music Olu Maintain – 'Cinderella' ft. 2face Idibia". Pulse Nigeria. Joey Akan. 16 June 2015. Archived from the original on 18 June 2015. Retrieved 16 June 2015.