Jump to content

Rukayya Dawayya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Rukayya Umar Daw IIaiya (an haife ta ranar 17 Oktoba 1985) yar wasan Kannywood ce daga jihar Kano Nigeria . [1]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Rukayya Umar Dawayya ranar 17 ga Oktoba shekarar 1985 a Kano. Mahaifinta dan kasuwa ne dan garin Matazu jihar Katsina yayin da mahaifiyarta ta fito daga jihar Borno . Dawayya ta yi Makarantun Firamare da Sakandare a Kano inda ta samu takardar shaidar harshen Larabci a kasar Saudiyya. Dawayya ta kuma samu takardar shaidar kammala Diploma a fannin aikin jarida a Jami’ar Bayero Kano . [2] [3]

Rukayya Umar Dawaiya ta fara fitowa a fim a shekarar 2000 a cikin fim dinta na farko mai suna "Dawayya" wanda ya sa aka ba ta sunan Dawayya. A shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa ta yi kaurin suna a cikin fim din Dawayya wanda ya kara mata kwarin gwiwar ci gaba da shirya fina-finai. Dawayya ta yi fina-finai sama da 150 a masana’antar fina-finan Hausa. Dawayya jakadiya ce a wasu kamfanoni a ciki da wajen Najeriya. Kuma itama 'yar siyasa ce kuma 'yar kasuwa. [1] [2] [3]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Dawayya ta yi aure a shekara ta 2012 kuma ta rabu a shekarar 2014. [4] Ta haifi da wanda aka haifa a Makka, Saudi Arabia . [5]

  • Ummi Sambo
  • Rudani
  • Alkibla
  • Angon hajiya
  • Igama
  • Hamdala
  • Jarumai
  • Khusufi. [6]
  1. "Why I'll act, pursue political career - Dawayya". Daily Trust (in Turanci). 2019-12-21. Archived from the original on 2023-05-17. Retrieved 2022-03-25.
  2. "Tarihin Jaruma Rukayya Dawayya(Rukayya Umar)". Haskenews-All About Arewa. Retrieved 2022-03-25.
  3. "Ina Jin Dadin Yadda Jama'a Suka Karbi Harkar Fim Na Hausa, Har Ma Yara Sun Watsar Da Indiyanci Sun Rungumi Hausa - in ji Jaruma Rukayya Umar". VOA. Retrieved 2022-03-25.
  4. "Auren Rukayya Dawayya ya mutu". Aminiya (in Turanci). 2014-10-09. Retrieved 2022-03-25.
  5. Blueprint (2014-10-27). "My ex divorced me through text message – Rukayya Dawayya". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2022-03-25.
  6. "Rukayya Umar | Actress, Writer, Location Management". IMDb (in Turanci). Retrieved 2025-05-02.