Rumbu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Runbu
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na warehouse (en) Fassara, akwati da fixed construction (en) Fassara
Suna a harshen gida σιρός
Maƙirƙiri Franklin Hiram King (en) Fassara
Ƙasa da aka fara Tarayyar Amurka
Contains (en) Fassara dry bulk cargo (en) Fassara
Runbunan karfe a jere a Ralls, Texas, Tarayyar Amerika
Yadda ake gina Rumbu na laka a Arewacin Najeriya

Rumbu wani ɗaki ne ko gini da akeyi don aje hatsi ko kayan abinci aciki, ko kuma gini ne da akeyi don ajiye kayan amfani masu yawa. Ana kuma amfani da rumbuna a ayyukan Noma da Kiwo domin ajiye hatsi, anfiyin amfani dashi ne domin ajiye hatsi, gawayi, siminti da dai sauran kayayyakin abinci da sauransu. Ire-iren rumbuna ya kai kashi biyu akwai na zamani da na gargajiya da kuma na gwamnati dake ajiye kayan masarufi.[1]

Rumbu, abin amfani ne na gargajiya da ake adana kayan amfanin gona da manoma suka noma a cikinsa a ƙasar Hausa.

Ana zuba dukkan nau’ukan kayan amfani da ake son adanawa na tsawon lokaci bayan an girbe su daga gona.

Ana zuba kayayyaki irin su Hatsi, Wake, Gyaɗa, da sauransu kuma a lokaci guda.

Ana amfani da ƙara da kuma ciyawar Gamba wajen yin sa. Sannan kuma bayan wannan akwai rumbun ƙasa. Duk dai aiki iri ɗaya suke yi. Kamar yadda ake da ɗakin kara da kuma na ƙasa; Wato ɗakin kago.

Ana yin amfani da Rumbu na tsawon lokaci kuma an tabbatar da cewa, ya na da tasiri don adana abinci.

Daga Zauren:

Hausawa Da Harshensu[2]

Wani rumbun ƙasa wanda aka ɗauka a jihar Neja, Pandogari, Ringa

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Rumbu/rumbuna". hausadictionary.com. Retrieved 27 December 2021.
  2. https://www.amsoshi.com/2023/09/rumbu.html?m=1