Simeon Bamire

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Simeon Bamire
mataimakin shugaban jami'a

Rayuwa
Haihuwa Oyan (en) Fassara, 18 ga Janairu, 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Malami
Imani
Addini Kiristanci

Adebayo Simeon Bamire (an haife shi a ranar 18 ga watan Janairu 1959) malami ne ɗan Najeriya kuma farfesa a fannin tattalin arzikin noma wanda shine babban mataimakin shugaban (Vice-chancellor) na Jami'ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, tun a shekarar 2022.[1][2][3][4][5][6] A baya ya taɓa zama mataimakin (Vice-chancellor) shugaban jami'ar.[7][8]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Bamire ɗan Oyan ne a ƙaramar hukumar Odo-Otin a jihar Osun a Najeriya. Ya fara karatunsa ne a Datus Preparatory School, Accra, Ghana, sannan ya koma St. Charles' Grammar School, Osogbo domin makarantar sakandare a tsakanin shekarun 1972 - 1976. Ya samu gurbin shiga Jami’ar Ife (wato Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife) a lokacin inda ya karanta fannin tattalin arzikin noma a tsangayar aikin gona inda ya kammala digiri na ɗaya da na biyu da na uku; Bachelor of Agriculture a shekara ta 1985, M.Phil. a shekara ta 1992, da kuma PhD a shekara ta 1999 bi da bi.[8]

Aikin ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Bamire ya fara aikinsa na ilimi a Sashen Nazarin Tattalin Arzikin Noma a matsayin Mataimakin Malami a shekara ta 1992 kuma ya zama Farfesa a shekarar 2008. Ya kasance masani mai ziyara a Cibiyar Noma ta Ƙasa da Ƙasa (IITA), Ibadan; Mataimakin Dean, Faculty of Agriculture, Obafemi Awolowo University a cikin shekarun 2007/2008 da 2008/2009 ilimi zaman; Shugaban Sashen Nazarin Tattalin Arziki na Aikin Gona na 2010/2011 na zaman karatu kuma tsohon shugaban tsangayar aikin gona na Jami'ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife. Ya kuma yi aiki a matsayin shugaban tsakanin 1 ga watan Agusta 2013 da 31 Yuli 2015.

Bamire memba ne na kungiyar masana tattalin arzikin noma ta Najeriya (NAAE) da Leadership for Environment & Development (LEAD). Har ila yau, mamba ne na shirin Drought Tolerant Maize for Africa Project and Agribenchmark dake nan Jamus.[8]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Bamire ya auri Felicia Bosede Bamire kuma suna da yara huɗu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "BREAKING: OAU gets new Vice-Chancellor, Professor Simeon Bamire". Vanguard Ngr. Retrieved March 17, 2022.
  2. "Obafemi Awolowo University Names Professor Bamire As New Vice Chancellor". TribuneOnlineNG. March 17, 2022. Retrieved March 17, 2022.
  3. "Breaking: Prof Bamire emerges new Vice Chancellor of OAU". TVC News. March 17, 2022. Retrieved March 17, 2022.
  4. "EXCLUSIVE: Top contenders revealed as OAU appoints new VC today". PremiumTimesNG. March 17, 2022. Retrieved March 17, 2022.
  5. "BREAKING: OAU Gets New VC". Independent.NG. March 17, 2022. Retrieved March 17, 2022.
  6. "BREAKING: OAU Appoints New Vice-Chancellor". WithinNigeria.com. March 17, 2022. Retrieved March 17, 2022.
  7. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0
  8. 8.0 8.1 8.2 "PROFESSOR A.S. BAMIRE DVC ACADEMICS". GreatIfeAlumniWorldwide.org. Archived from the original on April 25, 2022. Retrieved March 17, 2022.