Jump to content

Smart Adeyemi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Smart Adeyemi
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Smart (en) Fassara
Sunan dangi Adeyemi
Shekarun haihuwa 18 ga Augusta, 1960
Wurin haihuwa Jihar Kogi
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya, mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ilimi a Jami'ar Fasaha ta Tarayya Owerri
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party
Personal pronoun (en) Fassara L485

Smart Adeyemi (an haife shi ne a ranar 18 ga watan Agustan shekarar 1960 a Iyara a ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi[1]) an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma a jihar Kogi, Najeriya, ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007. Ɗan jam'iyyar APC[2]ne. An sake zaɓen sa a matsayin Sanata a karo na uku a ranar 30 ga watan Nuwamban shekarar 2019.

Shekarun farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Smart Adeyemi a ranar 18 ga watan Agusta na shekara ta 1960.

Ya sami shaidar kammala karatun digirinsa ne a fannin hulɗa da jama'a, difloma a fannin shari'a, difloma mai zurfi kumafanni a Mass Communication, da kuma digiri na biyu a fannin harkokin gwamnati daga Jami'ar Fasaha ta Tarayya ta Owerri, kuma ya zama ɗan jarida.

Ya kasance shugaban ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2006.[2]

Sana'ar siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

An zaɓi Adeyemi a majalisar dattawa a cikin watan Afrilun shekarar 2007. A kan kujerarsa ta Majalisar Dattawa an naɗa shi a kwamitoci masu kula da harkokin kasuwanci, masana’antu, Federal Character & Inter-Government Affairs (Chairman), Babban Birnin Tarayya da Kasafin Kuɗi.[2] An kuma naɗa shi mataimakin shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa.[3]

A wani nazari na tsakiyar wa’adi da aka yi wa Sanatoci a cikin watan Mayun shekarar 2009, jaridan ThisDay ta lura cewa Adeyemi ya yi aiki a kan ƙudirorin doka kan Address na Ƙasa da kuma gyaran dokar ɗa’ar ma’aikata da kuma dokar kotu, kuma ya ɗauki nauyin gabatar da ƙudiri uku.[4]

A cikin watan Mayun shekarar 2010 jaridar Daily Sun ta ce Adeyemi ya buƙaci Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta fara bincike kan ƴan majalisar dokokin ƙasar da ya zarga da cin hanci da rashawa. Adeyemi ya ce an yi masa kuskure. Ya ce, “Ban taɓa cewa majalisar nan ta cin hanci da rashawa ba ce [...] To amma idan akwai ƴan kaɗan da suka yi almundahana to EFCC ta ci gaba da bankaɗo su.[5]

Sai dai duk da musanta hakan, shugaban majalisar dattawa, David Mark, ya sanar da kafa kwamitin wucin gadi na mutum shida da zai binciki lamarin, yana mai bayyana hakan a matsayin babban zargi. Shugaban kwamitin zai kasance ƙarƙashin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa , Kanti Bello, sannan ya haɗa da Sanata Ayogu Eze, Olorunnimbe Mamora, James Manager, Adamu Talba da Zainab Kure.[6]

Zargin Adeyemi dai ya yi kama da wanda Sanata Nuhu Aliyu daga jihar Neja ya yi a cikin watan Janairun shekarar 2008, wanda ya haifar da martani mai ƙarfi daga sauran ƴan majalisar.[7]

Adeyemi ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP domin sake tsayawa takarar Sanata a Kogi ta Yamma a zaɓen watan Afrilun shekarar 2011. Sai dai wata kotu ta soke zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP da aka gudanar a ranar 4 ga watan Afrilun shekarar 2011, inda ta ce ba a bi ƙa'ida ba kamar yadda dokar zaɓe ta bayyana.[8]

An sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani a ranar 7 ga watan Afrilu, inda Adeyemi ya doke abokin hamayyarsa Abiye Abinso da ƙuri’u 1,124 da ƙuri’u biyu.[9] A zaɓen 9 ga watan Afrilun shekarar 2011, Adeyemi ya ci gaba da riƙe kujerar sa.[10]

Kwanan nan Adeyemi ya lashe zaɓen kujerar sanata mai wakiltar mazaɓar bar Kogi ta Yamma a karo na uku; ya kayar da Sanata Dino Melaye a wani ƙarin zaɓen da kotun kolin ƙasar ta bayar, domin sake gudanar da sabon zaɓe bayan an soke nasarar Sanata Dino Melaye. Adeyemi ya yi nasara ne da tazarar ƙuri’u sama da 20,000.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-01-12. Retrieved 2023-04-04.
  2. 2.0 2.1 2.2 https://web.archive.org/web/20160303171511/http://www.nassnig.org/senate/member.php?senator=87&page=1&state=24
  3. https://sunnewsonline.com/webpages/features/encounter/2009/mar/28/encounter-28-03-2009-002.htm[permanent dead link]
  4. https://allafrica.com/stories/200905250350.html
  5. https://sunnewsonline.com/webpages/news/national/2010/may/27/national-27-05-2010-010.htm[permanent dead link]
  6. https://web.archive.org/web/20110717044256/http://thewillnigeria.com/politics/4660-Senate-Sets-Hoc-Committee-Probe-Smart-Adeyemi.html
  7. https://web.archive.org/web/20100612201757/http://234next.com/csp/cms/sites/Next/News/5574410-183/assembly_watch_smart_adeyemi_and_charges.csp
  8. https://web.archive.org/web/20110407022706/http://tribune.com.ng/index.php/news/19964-nass-election-court-nullifies-smart-adeyemis-candidature-orders-fresh-primary
  9. https://web.archive.org/web/20110411201438/http://tribune.com.ng/index.php/news/20186-smart-adeyemi-wins-pdps-court-ordered-primary-election
  10. https://www.vanguardngr.com/2011/04/why-i-was-re-elected-sen-adeyemi/