Taiwo Abioye

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Taiwo Abioye
Rayuwa
Haihuwa Jihar Kaduna, 17 ga Janairu, 1958 (66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami

Taiwo Olubunmi Abioye farfesa ce 'yar Nijeriya, a fannin harshen turanci da kuma girama na Ingilishi, tare da ƙwarewa a sarrafa harsuna daban daban, da kuma amfani da ilimin harsuna. Ita ce mace ta farko da ta zama Mataimakiyar Shugaban Jami'a (Deputy Vice Chancellor) a Jami'ar Convenant.[1]

Kuruciya da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haife ta ne a ranar 17 ga watan Janairun shekarar 1958 a Kaduna, ga iyayenta daga Jihar Ogun, Abioye ta yi digirinta na farko a Fannin Harshe a Jami’ar Ahmadu Bello. Yayin da ta kammala da sakamakon mataki na class upper a shekarar 1987. Ta samu digirinta na biyu da na uku wato digirgir a wannan makarantar a shekarar 1992 da 2004.[2] A 1982, Abioye ta kasance daliba mafi hazaka daga cikin daliban da suka kammala karatu a sashin Turanci.[3]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Abioye ta fara koyarwa ne a matsayin mataimakiyar malamin jam'ia a jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1988, a cikin shekaru goma masu zuwa ta zamo babbar malama a jami’ar ABU. A cikin shekara ta 2005, ta shiga Jami'ar Covenan University kuma an ba ta matsayin farfesa mai jiran gado a 2010, sannan ta zama cikakkiyar farfesa bayan shekaru uku. A cikin watan Afrilu na shekarar 2016, ta gargadi membobin kungiyar da ke kula da dalibai da su daidaita kansu da tsarin ofishinsu.[4]A cikin 2011, ta wallaf littafin Language and Ideology in George Ehusani's Writings, George Ehusani da masu duba masu zaman kansu sun karɓi littafin sosai.[5]Ta taba zama DVC (mulki) tsawon shekaru biyu, kafin ta zama mataimakiyar mataimaki a 2014.[6]

Sashin binciken rubutattun mukalai na ilimi wato Google Scholar ta sanya wani labari na 2009 mai taken Typology of rhetorical questions a matsayin salon kwarewa a rubutu. Binciken yayi duba ga yadda 'yan Najeriya suka dauki wani yare wanda ya bambanta da na mahaifiyarsu, musamman yadda ake magana a cikin wadannan yarukan a tsakanin masu amfani da shi ba na asali ba, da kuma tasirin wannan hanyar ga mai magana. Bugu da ƙari, nazarin yayi bincike kan batun tambayoyin lafazi, yayin tattauna wa game da fa'ida da rashin fa'ida tsakanin 'yan Nijeriya. Ana samun takardar a cikin International Journal of Language Society da Al'adu.[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Oyedepo urges FG to Increase funding to education". World Stage. January 18, 2018. Retrieved 2018-01-30.
  2. http://covenantuniversity.edu.ng/content/download/13865/92505/file/TAIWO+ABIOYE+CV-+AUGUST%2C+2016.pdf[permanent dead link]
  3. "admin. "Prof Taiwo Olubunmi Abioye". covenantuniversity.edu.ng. Retrieved 2017-11-23.
  4. Oni, Olamide (April 14, 2016). "Varsity inaugurates post graduate student council". Pulse. Retrieved 2017-11-23.
  5. "Nigeria: Ehusani - Priest, Gentleman and Scholar At 35". allAfrica.com. August 9, 2016. Retrieved 2017-11-23.
  6. http://www.pulse.ng/communities/student/covenant-university-varsity-inaugurates-post-graduate-student-council-id4919531.html
  7. "Taiwo Abioye". Google Scholar. 2017-11-23. Archived from the original on 2021-05-21. Retrieved 2017-11-23.