Jump to content

Tarihin Daura

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kofar fadar sarki

Tarihin Daura[gyara sashe | gyara masomin]

Gabatarwa[gyara sashe | gyara masomin]

A sanin kowa ne cewar, kowace al'umma da kuma kowace kasa a duniya nan tamu, tana da tarihin asalin kafuwarta, al'adunta da kuma dabi'unta wadanda take alfahari da su. Su ne kuma suke bambanta kasa ko al'umma da waninta. Ta hanyar ilmin tarihi da al'adu da dabi'un kasa ne ake sanin mashahuran mutanen kowace kasa, da kuma irin gudunmuwar da suka bayar wajen daukaka martabar kasarsu ko al'ummarsu, har sun kai fagen zama ababen koyi ga na bayansu. Har ma ta kai ana yin misali da halayen da dabi'un da suka bari don amfanin ya'yannsu da jikokinsu. Masana tarihivbda al'adu da kuma dabi'u na kowacce kasa ko al'umma, yawanci sukan yi amfani ne da kuma tabbatar da sahihancin abin da za su bayyana dangane da tarihin ko al'adun al'umma ko kuma dabi'unta. Yawancin hanyoyin da aka fi amfani da su sune: Na daya, hanyar "Kunne ya gimi-kaka". Wato tarihin baka, irin na wane yaji ga wane, shi kuma ya fada wa wane. Hanya ta biyu, ita ce alamu na zahiri' da za a iya dogara dasu wajen tabbatar da kumakasancewar kasar ko dabi'unta ko kuma al'adunta. Wadanda sun hada da abubuwa kamar su gine-ginen mutanen kasar, tanadaddun kayan tarihi da kuma abubuwan tarihi da aka hako na mutanen da, wadanda suka yi zama a wurin, shekara da shekaru da suka wuce. Hanya ta uku, ita ce ta rubutattun tarihi, ko dai wadanda mutanen da suka rubuta da kansu ko kuma wadanda na bayan su suka rubuta, suka bari ta yin amfani da hanya ta daya da ta biyu. Tarihin kafuwar daular Daura da asalin sarautarta da kuma kafuwar kasashen Hausa, an same shi ne ta wadannan hanyoyi da aka bayyana a sama.[1]

Kasar Daura na da matsayi na musamman a tarihin kasar Hausa. Labarin da ake da shi game da asalin Hausa Bakwai, ya nuna mana cewa daga Daura ne aka fara juyin nan da ya kawo canje-canje a sarautun kasashen Hausa. Tarihin ya nuna mana cewa, mata ne suka fara yin sarautar Daura. Ana kiran wadannan sarauniyoyi Magajiya.[2]

A zamanin Magajiya Shwata ne wani bako sa aka fi sani da suna Bayajida ya zo Daura. Labarin zuwan Bayajida, ya ce shi mutumi nkasar Bagadaza ne a cikin Gabas ta Tsakiya. A Daura ne ya kashe Macijiya da ta addabi mutanen gari. Wannan bajinta da kuma ya yi, ta zama sanadin da ya auri Magajiya. Bayan mutuwar Bayajida da Magajiya, sai sarautar Daura ta koma ga dansu Bawo. Daga nan ne kuma sarautar ta koma hannun maza.

Labari ya nuna mana cewa, 'ya'yan Bawo ne suka yi sarautar kasashen Hausa shida. Wadannan kasashe su ne Daura,Kano,Katsina,Zazzau,Gobir da Rano. Wadanda da Bayajida ya haifa kafin ya iso Birnin Daura a garin gabas, mai suna Biram, ya yi sarauta a gabas ta Biram, (Garun Gabas) wadda ita ce cikon Hausa Bakwai.

Ba mu da cikakken tarihin Daura daga labarin kafuwar mulki, sai bayan jihadin Usman Dan Fodyo da ya auku a farkon karni na goma sha tara.

Shi Shehu Usman Dan Fodiyo, malami ne da ake zaune a kasar Gobir. Shi kuma Bafilatani ne. Yana da almajirai a ko'ina cikin kasar Hausa. Jihadin da ya hubanta domin gyaran addini, an fara shi a kasar Gobir. Bayan an cinye Gobir, sai Shehu Usman Dan Fodiyo ya kafa sabuwar daula ta Musulunci. Haka kuma almajiransa suka gabatar da jihadi a sauran kasashen Hausa, suka tumbuke mulkin Sarakunan Hausa, suka kafa nasu a kasashen mulkin Shehu Usman Dan Fodiyo.

Mallam Isyaku ne almajirin Shehu USman Dan Fodiyo da ya shugabanci jihadi a kasar Daura. Mallam Isyaku ya mamaye garin Daura bayan Sarkin Daura Abdullahi, wanda aka fi sani da Sarki Gwari Abdu, ya fice daga garin tare da jama'arsa.

Mallam Isyaku ne Sarki Fulani na Farko a Daura. Zuri'arsa ta ci gaba da mulkin Daura har 1906 lokacin da aka mayar da sarakunan Daura na asali.

Sarakunan Daura sun yi gudun Hijira na shekara dari daga lokacin da sarkin Gwari Abdu ya fita har zuwa lokacin da Turawan mulkin mallaka suka mayar da su a kan gadon sarautarsu na Daura a cikin 1906.

Sarakunan Daura sun kafa mulkinsu a wurare da dama, a lokacin da suke gudun hijira. Sun zauna a Murya da Yekuwa garuruwan da yanzu ke cikin Jamhuriyyar Nijar. Sun kuma zauna a Yardaje, Toka da Acilafiya kafin su kafa mulkinsu a Zangon Daura wurin da ska fi dadewa. Daga nan ne kuma Turawan mulkin mallaka suka mayar da su a kan sarautar Daura, wato aka mayar da su gidansu na iyaye da kakanni.

Kasar Daurata samu ci gaba a lokacin Sarkin Abdurrahman wanda ya yi shekara 55 a kn gadon Sarautar Daura (daga 1911-1966) . Allah ya jikansa, ya rahamce shi,amin. Da kuma zamanin Sarki Bashar, wanda ya gaji Sarki Abdurrahman a cikin 1966 kuma yake sarautar Daura har zuwa lokacin da Allah ya dauki ransa a ranar Asabar 24 ga Fabarairu 2007.

A ranar Alhamis 1 ga watan Maris 2007 aka dorawa Alhaji Umar Faruk Umar wanda kane ne ga Marigayi Sarkin Daura Muhammadu Bsshar nauyin rikon wannan kasa a matsayinsa na Sarkin Daura na sittin (60). Allah bashi ikon daukar wannan nauyin ya kuma kare shi daga mahassada amin.

Asalin Mutanen Daura da Kafuwar Masarautar Daura[gyara sashe | gyara masomin]

Abu ne mawuyaci kwaraia ce an tabbatar da ainaihin asalin kafuwar kowace irin al'umma ko kasa ba tare da an tabo matsugunnin farko na dan Adam ba. Har yanzu dai babu wani bigire (wuri) takamaimai inda marubuta tarihi suka hadu a kan cewa shi ne inda dan Adam ya fara zama; wasu su ce a nahiyar Afrika ne; wasu su ce a kasashen nahiyar Sin ne; wasu su ce a kasashen Hindu ne; wasu ma sun ce a kasashen Turai ne da dai sauran sassa na kasashen duniyarnan tamu. Duk da haka, masan tarihi da masana dabi'u da al'adun dan Adam da na kasashe da dauloli, sun hadu a kan cewar bigire (wuri) na farkon da dan Adam ya fara wayewa da kuma nuna basira da hikima da zaman duniya mahaliccinsa ya yi masa baiwa da su, shi ne wurin da yanzu aka fi sani da kasashen Gabas ta tsakiya. Daga wannan yanki na duniyanan ne za mu gutsuri tarihin kafuwar masarautar Daura da mutanen Daura. Kusan dukkan litattafan tarihin da suka yi bayanin kafuwar Daular Daura, sun tsamo tarihinne daga cikin mashahurin kundin tarihin nan da aka fi sani da suna "GIRGAM" wanda aka ce a halin yanzu akwai wani sashe na kundin yana can Damagaram. Shi kuma ya karbe shi ne daga wurin Sarki NUu a yayin da yake zaune a Zango sanadiyyar aukuwar mulkin Fulani a Daular Daura. Wani sashe na wannan kundi kuma an ce yana wata cibiyar ajiyar kayan tarihi a Ingila. Shi kuma Turawa ne suka yi dabarar dauke shi daga fadar Daura, a yayin da suke mulkin kasar nan. Har yau kuma ba su dawo da shi ba. Abubuwan da shi wannan littafi Girgam ya nuna shi ne cewar tun zamanin Kana'ana dan Sayyadina Nuhu. mutane ke zaune a wurin da ake kira Falasdinu. Wasu daga cikin wadannan mutane na Kan'ana ne suka yi hijira daga inda suke zaune wato Falasdinu a karkashin jagorancin wani da ake kira Najibu, suka yiwo kudu maso yamma har sai da suka iso wurin da a yanzu ake kira (Lubayya) Libya. A da can kuma duk wannan sashe yana karkashin kasashen Misra ne. A wannan wuri ne su mutanen Najibu suka zauna shekaru masu yawan gaske, har ma suka yi auratayya tsakaninsu da mutanen da suka tarar a wurin, wato kabilar Kibdawa (Coptics) wadanda suka kasance masu bakar fata ne. Sun hayayyafa da wawadannan mutane, ta yadda bayan shekaru masu yawa, sai ya kasance launin jikin jikokin mutanen Najib mutanen Kan'an ya jirkice daga launi irin na Larabawa ya komo na bakaken mutane.[3]

A dai dai lokacin da Najib yayi zango a kasashen Masar sai dan sa Abdukl-Dar ya wuto zuwa kasashen Tura bulus inda ya zauna na wani dan lokaci har ma ya nemi sarauta a daya daga cikin biranen amma mutanen suka ki yarda da su ba bashi. Ganin haka, sai Abdul dar ya taso daga kasashen Turabulus, shi da mutanen sa wadanda suka biyoshi daga inda suka rabu da mahaifinsa wato Masar, suka fuskanci Kudu. Suna tafiya suka ratsa hamadar rairayin nan ta sahara har suka iso wani dausayi mai ni'ima da koramuda ake kira "Gigido". Wurin da aka fi sani da tsohion birni. A wannan wuri mai ni'ima ne suka tsaida shawarsu su zauna. Zaman Abdul dar da mutanensa a wannan wuri "Dausayi" shi ya haifar da kafuwar da garin da yanzu aka sani da sunan 'Daura'. Domin kuwa sanadiyar zamansu a wannan wuri m ai dausayi da koramu, ya sa suka saki jiki har suka kafa gari wanda ya kasaita hae ya zama Daula mai fadi wanda ta mamaye 'yan karkaru dakwe kusa da ita har ma da masu nisa da ita. Bayan mutuwar Abdul dar 'ya'yansa da jikokinsa mata ne suka ringa yin Sarautar wannan daular da ake kira Daura. Ana kiransu da sarautar MAgajiya. Ga sunayensu: Kufuru, Gini, Yakumo, Yakunya, Walzamu, Yanbamu, Gizir-gizir, Innagari, da Daurama itace ta karshe da tayi sarauta a tsohon birni. Itace ta matsa kudu ta kafa garin Daura na yanzu. Daga sunanta ne aka sam i sunan wannan gari Daura, kuma sarautar Daura ta tashi daga MAgajiya ta koma Daurama. Bayan mutuwarta a Daura ga sauran matan da sukayi sarauta: Gamata, Shata, Batatuma, Sandamata, Jamata, Hamata, Zama da Shawata.[4]

Masana Tarihi su suna cewa a zamanin Daurama Shawata ne Bayajidda yazo Daura. Domin itace magajiya ta goma-sha bakwai kuma ta karshe a jerin sarautar mata.[5]

ko da yake anyi bayani cewa, Abduldar da mutanensa sun zauna a Dausayin Gigidohar suka kafa Daula, da kuma bayanin kaurar Sarauniya Daurama zuwa inda garin Daura yake a yanzu, ba wai ana nifin babu wasu mutane da ke zaune a wanna nwuri bane sam sam. A'a, akwai mutane wadanda ke zaune a karkara mai dausayi, tun kafin zuwan su Abduldar da mtanensa. sai dai su wadannan mutane ba wai suna zaune ne a tattare ba, kowa yana zaune ne da iyalinsa da danginsa. Galibinsu mafarauta ne da asu hakar tam. Kuma suna yawo daga wannan wuri zuwa wancan. Basu da wani tsari na Shugabanci ko Addini, balle wani hali na ci gaba ko zamantakewa da dabi'u irin na al'ummar da kanta ya waye ko ya fara wyewa. misali, akwai irin wannan mutane a kewaye da Gigido har ma yawansu na farauta da hakar tama da kuma hanyoyin neman Abinci kan dauke su zuwa wurare masu nisa. Kamar yanda aka same su a wurare kamar Gindin dutsen Dala a kano, kasashen da yanzu aka sani da sunayen Katsina, Rano, Gobir, Zazzau, Gaya, Garun gabas da sauran wuraren da suka zamo kasashe HAusa a yau. Tun da yake irin wadannan mutane ba'a zaune suke wuri gida ba, kuma basu da tsari na shuganci sai ya kasance suna zaune ne cikin tsoro da rashin aminci.

Zuwan Abduldar dausayin Gigido shi ya haifar da kafuwar daular Daura. Bayan mutuwarsa mata suka ringa yin sarautar kasar Daura. Tarihin da aka Samo daga Girgam ya nuna mana cewa mata goma sha bakwai sukayi sarautar Daura kafin sarauta ta koma hannun maza.

Zuwan Bayajida[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2023-03-09. Retrieved 2023-03-09.
  2. https://en.wikipedia.org/wiki/Daura_Emirate
  3. https://www.cambridge.org/core/journals/journal-of-african-history/article/abs/hausa-politics-the-affairs-of-daura-history-and-change-in-a-hausa-state-18001958-by-m-g-smith-berkeley-los-angeles-and-london-university-of-california-press-1978-pp-xix-536-illus-charts-etc-21/3FD9815F0566727DCD503915F0F80C36
  4. https://www.muryarhausa24.com.ng/2018/10/karanta-kaji-takaitaccen-tarihin-daura.html
  5. https://ha.wikipedia.org/wiki/Daura