Jump to content

Terra Kulture

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Terra Kulture

Bayanai
Suna a hukumance
Terra Kulture
Iri ma'aikata da tourist attraction (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Ƙaramar kamfani na
Harshen amfani Turanci
Mulki
Hedkwata jahar Legas
Mamallaki Terra Kulture
Tarihi
Ƙirƙira 2003
terrakulture.com
Terra Kulture Arts & Studio Limited

Bayanai
Suna a hukumance
Terra Kulture
Iri Cultural Institution
Ƙasa Najeriya
Ƙaramar kamfani na
Harshen amfani Turanci
Mulki
Hedkwata Tiamiyu Savage Street, Victoria Island, Lagos
Mamallaki Terra Kulture
Tarihi
Ƙirƙira 2003
terrakulture.com
hoton terra
Terra culyures

Terra Kulture cibiyar fasaha ce da al'adu a Legas mai haɗe da gidan abinci.[1][2]

Lauyan Najeriya Bolanle Austen-Peters ce ta kafa Terra Kulture a shekara ta 2003.[3]

Cibiyar ta kasance gidan cin abinci, da ke aiki a matsayin gidan abinci irin na gida Najeriya, kantin sayar da littattafai da wurin al'adu,[4] tana gudanar da bikin nunin zane-zanen fasaha a Najeriya,[5] wasan kwaikwayo,[6] da karatun littattafai da kuma azuzuwan darussan harshe da suka haɗa da manyan harsunan Najeriya guda uku, Hausa, Ibo da Yarbawa.[1]

Abubuwan da ake yi na shekara-shekara a Terra Kulture sun haɗa da gwanjon[7] fasaha da bikin Taruwa na Ƙirƙirar zane.[8][9]

Terra Arena

[gyara sashe | gyara masomin]

Terra Kulture ya ƙaddamar da gidan kallon wasan kwaikwayo mai kujeru 450 mai suna Terra Kulture Arena, wanda ke da hedkwata a Tiamiyu Savage Crescent, Victoria Island, Lagos, Najeriya.[10]

Terra Academy for The Arts (TAFTA)

[gyara sashe | gyara masomin]

Har ila yau, Terra Kulture tana da haɗin gwiwa tare da Gidauniyar Mastercard don ƙarfafa 65,000 Matasan Najeriya,[11] wani yunƙuri ne wanda zai samar da wani muhimmin sashi na Shirin Terra Academy For The Arts (TAFTA).[12]

  1. 1.0 1.1 Akeem Lasisi (31 October 2014). "Terra Kulture has organised over 200 exhibitions l–Austen-Peters". The Punch. Archived from the original on 29 November 2014. Retrieved 29 November 2014.
  2. Oresanya, Demilade (6 November 2014). "Terra Kulture @10: Making Nigerian Art, Culture and Lifestyle a Priority" . CPAfrica. Retrieved 2 January 2015.
  3. Rita Ohai (2 November 2014). "Austen-Peters: Living for the love of art" . BusinessDay. Archived from the original on 3 March 2016. Retrieved 10 November 2014.
  4. "TERRA KULTURE celebrating a decade of Greatness at the 10th Anniversary of Terra Kulture". Television Africa. 17 November 2014. Retrieved 3 January 2015.
  5. Japheth Alakam (10 December 2014). "The masters showcase class at Distinction 2". The Vanguard. Retrieved 2 January 2014.
  6. Onnaedo Okafor (12 November 2014). "Terra Kulture: The One-Stop Nigerian Cultural Shop" . The Pulse. Retrieved 3 January 2015.
  7. "Art auction market looks up, makes N286.6m in 2013" . Businessday. 10 January 2014. Retrieved 3 January 2014.
  8. Tolu Ogunlesi (17 October 2014). "The Africa report". Retrieved 2 January 2015.
  9. "Drama combines with dance, music at second edition of Taruwa Festival". Daily Independent. Retrieved 2 January 2015.
  10. " 'History made in Nigeria film industry with the new 450-seater theatre". Pulse. Retrieved 3 April 2017.
  11. Terra Kulture, Mastercard Foundation partner to create opportunities for creatives" l. The Guardian . Retrieved 19 June 2022.
  12. Terra Kulture, Mastercard Foundation Partner to Empower 65,000 Young Nigerians" . This Day Live Newspaper. Retrieved 29 June 2022.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]