Theresa May
Theresa May yar siyasar Birtaniya ce. An haife ta a shekarar 1956 a Eastbourne, East Sussex da ke Birtaniya. Theresa May ta hau kujerar fira-ministan Birtaniya daga watan Yulin shekarar 2016 bayan da David Cameron ya ajiya aiki. May tayi marabus a matsayin firayim minista a watan Yulin shekarar 2019 kuma Boris Johnson ne kuma ya gaje ta.[1][2]