Akwai yuwar admin ya goge wannan shafin matukar ba'a inganta ta ba.
Tsibirin Bamuda Duk da [1] cewa a duniya
abubuwan mamaki dake faruwa a cikinsu ba tare
da Dan Adam ya fahimci musabbabansu ba,
Tsibirin Bamuda (Bermuda Island ko Bermuda
Triangle) ne kadai ya fi shahara a bakunan
mutane sanadiyyar haka. Wannan shahara ta
samo asali ne daga nahiyar Amurka
(South America), a hankali labarin ya ci gaba da
yaduwa zuwa sauran kasashen duniya. Manyan
ababen mamakin da ake ikirarin suna faruwa a
muhallin tekun da wannan tsibiri yake sun hada
da bacewar jiragen sama – masu dauke da
fasinjoji dan kasuwa ko na soji – da jiragen
ruwa – manya da kanana da na shawagi. Idan
suka bace a galibin lokuta, ba a ganin buraguzan
jirgin balle a kaddamar da bincike kan dalilan da
suka haddasa faruwar hadarin. Wannan
al’amaran ababen al’ajabi ne. A cewar masu bayar da
labarai, bai tsaya a bacewar jirage ba tare da
ganin buraguzansu kadai ba, har da wasu
labarai masu ruda kwakwalwa kan irin yanayin
da tekun ke kasancewa na launi da kuma
sulmuya a wasu lokutan, ko kuma wasu irin
dabi’u da ake ikirarin gira-gizan da ke saman
teku ke shiga, a yayin aukuwar hadarurrukan
da suka fara faruwa shekaru kusan dari biyu da
suka gabata. Ire-iren wadannan labarai sun
samo asali ne daga irin jawaban da masu lura da
na’urar filin saukan jiragen sama da ke tsibirin ke
bayarwa. Ko wadanda ake tarawa wajen
binciken da hukumomin gwamnatin Amurka da
ke lura da ire-iren wadannan hadarurruka ke yi.
Da wannan, marubuta suka sa wa wannan
muhalli suna: The Bermuda Triangle (Kusurwar
Bamuda), ko kuma The Devil’sTriangle
(Kusurwar Shedan).
A halin yanzu da dama cikin wadanda suka taba
jin labarin wannan bigire na Bamuda, sun yarda
cewa wani wuri ne mai cike da almara, kamar
yadda galibin turawa masu bincike suka fada.
Da kuma cewa babu wanda ya san abin da ke
haddasa wannan al’amari, sai Allah (ga
wadanda suka yarda da Allah kenan), ko kuma
dabi’a ta shu’umcin wurin. Wasu suka ce aljanu
ne a wurin. Wasu suka ce akwai wasu halittu ne
na musamman da a harshen Turanci ake kira
Aliens, masu haddasa hakan. Wasu suka ce a'a,
irin yanayin wurin ne kawai. Da dai sauran
ra’ayoyi masu kama da haka. Shin, meye
gaskiyar wadannan zantuttuka da ake ta yi kan
wannan tsibiri? Wani irin bincike aka yi wajen
gano hakan? Jiragen ruwa da na sama guda
nawa suka bace a wannan mahalli? Rayuka
nawa suka salwanta? Wa da wa suka yi rubuce-
rubuce kan haka cikin Malam Kimiya da masu
sha’awar rubutu kan al’amuran mamaki a
duniya? Meye ra’ayin nazarin da Malaman
Kimiyya suka yi kan dalilin faruwar wadannan
abubuwan mamaki? Shin, wai ma tukun, a
duniya akwai wasu wurare ne masu irin wannan
dabi’a, ko dai tsibirin Bamuda ne kadai? In eh
akwai, to me ya sa na tsibirin Bamuda ya sha
bamban, ya shahara fiye da sauran a duniya?
Wadannan, da ma wasu tambayoyi, za mu samu
amsoshinsu cikin makonni masu zuwa in Allah
Ya yarda.
A Ina Tsibirin Yake?
Kafin mu yi nisa, asalin tsibirin Bamuda, watau
Bermuda Islands, yana gab da tsakiyar tekun
Atlantika ne, Arewa da Jihar Fulorida da ke
Amurka. Kuma duk da cewa ana danganta
wannan wuri ko kusurwa da tsibirin Bamuda, sai
dai ba a wannan tsibiri kadai wannan kusurwa
yake ba. Kusurwar Bamuda wani wuri ne da ya
hada manyan gabar tekunan kasashe guda uku
da ke nahiyar Arewaci da kuma kudancin
Amurka. Kusurwar farko ta faro ne daga gabar
Fulorida ta kasar Amurka, ta zarce zuwa gabar
babban tsibirin Puerto Rico da ke yamma maso-
kudu da gabar Fulorida. Daga tsibirin Puerto
Rico kuma kusurwar ta cilla Arewa, inda ta tike a
gabar tsibirin Bamuda da ke kusa da tsakiyar
tekun Atlantika. Wannan wuri ko mahalllin teku
da ke tsakanin wadannan gabobi guda uku, shi
ake kira The Bermuda Triangle, ko The Debil’s
Triangle.
An danganta wannan kusurwa da tsibirin
Bamuda ne saboda a nan ya tike, kuma galibin
ababen hawa kamar su jiragen sama da na ruwa
wadanda ake amfani da su wajen kasuwanci da
shawagi da atisayen soji a wannan nahiya, duk a
can suke tikewa kafin su komo inda suka taso.
Ko kuma daga can suke wucewa zuwa wasu
nahiyoyin, irin su Turai da Arewacin Amurka da
kasashen Asiya.
Wannan kusurwa ta Bamuda ita ce bigiren da
jiragen sama da na ruwa ke shawagi fiye da
kowane wuri a duniya. An kiyasta cewa akalla
akan samu sawun jiragen sama daga wannan
nahiya zuwa kasashen turai da sauran nahiyoyi,
sama da dubu hamsin a shekara. Bayan haka,
akwai jiragen ruwa da na kasuwanci da na
shawagi ko yawon bude ido, da kuma jiragen
saman atisayen soji da Hukumar Sojin Amurka
ke turawa suna shawagi, watau kai-komo don
yin atisaye. Har wa yau akwai masu shawagi da
kananan kwale-kwalen shakatawa wadanda a
harshen turanci ake kira Pleasure Boats, da
kuma jiragen ruwan tsere da ake kira Yatchers.
Bayan haka, akwai filayen saukan jiragen sama a
dukkan kusurwoyin nan uku, tare da tashar
jiragen ruwa masu karban manya da kananan
jiragen da ke shawagi a wannan wuri. Sannan
kuma sai miliyoyin masu zuwa yawon bude ido
daga sauran kasashen duniya, musamman ma
Amurka da Turai. A takaice dai, wannan wuri
rayayyen wuri ne da sawun jirgin ruwa da na
sama da na masu ziyara ba su daukewa; daga
shekara zuwa shekara.
Zai dace mai karatu ya rike wannan karatu kan
yawan zirga-zirgar da ake yi a wannan wuri,
domin zai taimaka masa wajen karba ko rashin
karbar dalilan da wasu marubuta suka bayar
wajen yanke hukuncinsu na karshe.
Yaushe Abin Ya Fara?
Wannan kusurwa da ake wa take da “Kusurwar
Shedan” – ko Debil’s Triangle – ya fara cin
jiragen sama da na ruwa ne shekaru kusan dari
biyu da suka gabata, duk da cewa ba a fara
fahimtar hakan ba sai wajen shekaru casa’in
zuwa dari da suka wuce.
Wannan wani sashi ne daga tsibirin bermuda.
Daga nan ne aka fara
danganta hadarurrukan da suka gabata da
wannan yanayi mai ban mamaki. Kamar yadda
bayanai suka gabata, wannan kusurwa ta
Bamuda ta yi kaurin suna ne wajen hadararruka
masu ban mamaki, inda bayan hadarin ake rasa
abin da ya haddasa shi, ko kuma a ma kasa
samun buraguzai ko gawawwakin wadanda suka
rasa rayukansu da ma na jirgin gaba daya.
A wasu lokuta a kan samu sakon neman agaji
daga direbobin jiragen sama cewa suna ganin
wasu abubuwa masu ban tsoro ko firgitarwa.
Kafin a mayar da jawabin ceto garesu, sai kawai
a nemi hanyar sadarwa a rasa. Wani kuma zai
bugo ne cewa ba ya ganin gabansa, bayan kuma
a na’urar lura da yanayin sararin samaniya babu
wata matsala da na’urar ke hangowa: babu
yanayin hazo mai firgitarwa, babu ruwan sama,
babu alamar mahaukaciyar guguwa mai yi wa
jiragen ruwa dibar karan mahaukaciya, amma
sai kawai a ji hanyar sadarwar ta yanke.
Mafi shahara daga cikin abubuwan mamaki da
suka faru a wannan kusurwa shi ne hadarin
tawagan jiragen kai hari da darkake abokan gaba
na kasar Amurka masu suna Flight 19, wadanda
hukumar sojin sama na kasar Amurka ta aika
don yin shawagi a wannan kusurwa cikin
shekarar 1945. Duk da cewa ana lura da tafiyar
wannan tawaga na jirage ta hanyar na’ura
hangen nesa sadda suka baro cikin kasar
Amurka, sai dai cikin lokaci guda kawai sai aka
neme su aka rasa. Da aka nemi sadarwa da
shugaban tawagar, sai ya ce: “A yanzu muna
shiga wani irin farin ruwa ne...al’amura sun fara
lalacewa. Bamu san inda muke ba a halin
yanzu...ruwan kore ne...a a, fari ne!”, sai
sadarwa ta yanke a tsakanin masu lura da
na’urar da wannan shugaban tawaga.
Bayan faruwar wannan lamari, an yi ta bincike
cikin teku ba a samu buraguzan wadannan
jirage ba balle wadanda suke ciki. Babu wanda
ke da wani bayani gamsasshe kan abin da ya
haddasa wannan hadari har zuwa yau, balle
bayani kan hakikanin wurin da abin ya auku. A
lokacin da aka tura wata tawa
ga ta manema
jirage, da suka isa wurin da na’urar ta sanar da
faduwarsu, babu abin da aka gani a wurin.
Daga nan aka ci gaba da samun ire-iren
wadannan hadarurruka masu ban mamaki da
al’ajabi. Wasu a kan samu bayanai kan batansu,
bayan tsawon lokaci; wasu kuma ko alama ba a
samu, sai dai kawai a hakura,bamuda dai takasance waje ne dake tsakiyan ruwa wanda malamai da dama suka bayyana banda ubangiji bawanda yasan menene yake cikin tsibirin bamuda dai malamai sunce kaman malam muhammad Auwal Adam wanda akafi sani da albani yace banda al-arshin allah madaukakakin sarki babu wani waje ko kuma wani masarauta da tafi tafkin tekun bamuda tsaro a duniya gaba daya.