Vincent Ado Tenebe
Vincent Ado Tenebe (an haife shi a ranar 17 ga watan Agusta, a shekarar 1958) masanin aikin gona ne na kasar Najeriya . Shi ne tsohon mataimakin shugaban jami'ar jihar Taraba Jalingo sannan kuma tsohon shugaban jami'ar budaddiyar jami'ar Najeriya[1] .
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Vincent Ado Tenebe a jihar Kaduna, a Nigeria, ranar 17 ga watan Agusta, a shekarar 1958[2][3]. Ya samu shaidar kammala karatunsa na firamare daga St. Patrick Primary School Maiduguri tsakanin shekaraar 1965 zuwa 1971. Ya samu takardar shedar karatunsa ta yammacin Afirka a shekarar 1976 daga Makarantar Sakandaren Gwamnati, Yerwa, Maiduguri, Najeria.[4] Ya yi digirinsa na farko, B.Sc. (Agric) cum laude, da digiri na biyu, M. Sc. A fannin aikin gona a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya; Ya yi karatun Ph.D a fannin aikin gona a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi. [3]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Vincent Ado Tenebe ya fara aiki a matsayin mataimakin digiri na biyu a shekarar 1984 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa. A 1988, an nada shi shugaban gonar jami'ar[5]. A shekara ta 1995, ya zama shugaban sashen samar da amfanin gona na cibiyar. A shekarar 2003 ya zama Farfesa a fannin Aikin Gona a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Afirka da ke Bauchi. [5]
Sana'ar gudanarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Vincent ya zama mataimakin shugaban jami'ar Open University a ranar 7 ga watan Maris, a shekarar 2008.[6] Ya zama mataimakin shugaba na biyu na National Open University of Nigeria,a ranar 14 ga watan Oktoba,a shekarar 2010. [5] [6]A shekarar 2017 ya zama mataimakin shugaban jami'ar jihar Taraba.[7]
Memba da zumunci
[gyara sashe | gyara masomin]A 1986, ya zama memba na Agriculture Society of Nigeria (ASN) 1986. Bayan shekara guda, ya zama memba na kungiyar kula da gonaki ta Najeriya. A shekarar 2002 ne, ya zama Fellow na Institute of Cost Management (FCM). A 2012, ya zama Fellow na National Institute for Education and Research (FNIER) kuma a wannan shekarar ya zama Fellow na Nigeria Society for Experimental Biology (FNISEB). Bayan shekara daya, ya zama dan kungiyar malamai ta Najeriya (FASSONT). A shekarar 2014, ya zama Fellow na Chartered Institute of Human Capital Development of Nigeria kuma a shekarar 2015, ya zama Fellow na Biotechnology Society of Nigeria (FBSN).[8]
Nassoshi
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Viashima, Sylvanus (October 19, 2019). "My vision for Taraba State University – Professor Tenebe". Sunnewsonline. Retrieved December 4, 2023.
- ↑ Edet, Hope (2017-04-03). "TENEBE, Prof. Vincent Ado". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2023-12-03.
- ↑ 3.0 3.1 "Professor Vincent Ado Tenebe - Laweh University College" (in Turanci). Retrieved 2023-12-03.
- ↑ "Prof. Vincent Ado Tenebe: An Embodiment of Professionalism". Top Celebrities Magazine (in Turanci). 2015-10-22. Retrieved 2023-12-03.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 "Vincent Ado Tenebe". The Academic Union Oxford. Retrieved December 3, 2023.
- ↑ 6.0 6.1 "Deputy Vice Chancellor Administration | NOUN". nou.edu.ng. Retrieved 2023-12-04.
- ↑ "Taraba State University Jalingo". TARABA STATE GOVERNMENT (in Turanci). Archived from the original on 2023-12-04. Retrieved 2023-12-04.
- ↑ "Taraba State University Jalingo". TARABA STATE GOVERNMENT (in Turanci). Archived from the original on 2023-12-04. Retrieved 2023-12-04.