Wikipedia:Tutorial A
Ina son nayi magana akan abincin mu na aladun Hausa
Rubuta sabuwar mukala / How to create new articles / Comment créer de nouveaux articles
[gyara masomin]Hausa
Rubuta sabbin mukaloli a cikin Wikipedia abu mai sauki ne. Fassarori na gaba, za su taimake ku, saboda za ku iya ƙirƙirar sababbin ƙasidu game da batutuwa da dama, kamar ƙasashe, birane, garuruwa da ƙauyuka, shahararrun mutane, da sauransu. Idan kana da bukatar wata jumla saboda ƙirƙirar sabbin kasidu, za ka iya tambaya anan.
English
It's very simple to create new articles on Wikipedia. The following translations can help you to create stubs (short articles) on a lot of different topics such as countries, cities, towns and villages, famous people, and so on. If you think a sentence could be useful in order to create articles, you can make a suggestion here.
Français
Il est très facile de créer de nouveaux articles sur Wikipédia. Les traductions suivantes peuvent vous aider à créer des ébauches (de courts articles) sur un grand nombre de sujets, tels que les pays, les villes, les personnages célèbres, etc. Si vous pensez qu'une phrase peut être utile pour créer des articles, vous pouvez faire une suggestion ici.
English | Hausa | Français |
---|---|---|
Cities, towns and villages | Birane, garuruwa da Kauyuka | Villes et villages |
Paris is a city located in the Île-de-France region, in France. | Paris birni ne, da ke yankin Île-de-France, a ƙasar Faransa. | Paris est une ville qui se situe dans la région Île-de-France, en France. |
Enugu is a city located in Enugu State, in Nigeria. | Enugu birni ne, da ke jihar Enugu, a ƙasar Najeriya. | Enugu est une ville qui se situe dans l'État d'Enugu, au Nigeria. |
Dadin Kowa is a town located in Jos North LGA, in Plateau State, in Nigeria. | Dadin Kowa gari ne, da ke karamar hukumar Jos North, a jihar Plateau, a ƙasar Najeriya. | Dadin Kowa est une ville [gari : petite ville ; birni : grande ville] qui se situe dans la zone de gouvernement local de Jos North, dans l'État de Plateau, au Nigeria. |
Sabiñanigo is a town located in the provine of Huesca, in the autonomous community of Aragon, in Spain. | Sabiñanigo gari ne, da ke yankin Huesca, a jihar Aragon, a ƙasar Spain. | Sabiñanigo est une ville qui se situe dans la province de Huesca, dans la communauté autonome d'Aragon, en Espagne. |
Gillué is a village located in the municipality of Sabiñanigo, in the province of Huesca, in the autonomous community of Aragon, in Spain. | Gillué ƙauye ne, da ke a lardin Sabiñanigo, a yankin Huesca, a jihar Aragon, a ƙasar Spain. | Gillué est un village qui se situe dans la municipalité [lardi : district] de Sabiñanigo, dans la province de Huesca, dans la communauté autonome d'Aragon, en Espagne. |
Kaduna is two hundred kilometers from Abuja. Kaduna stands on the Kaduna river. | Birnin Kaduna kilomita dari biyu ne daga Abuja. Kaduna na kan kogin Kaduna ne. | Kaduna est à deux cents kilomètres d'Abuja. Kaduna est traversée par la rivière Kaduna. |
Lagos is one hundred kilometers from Ibadan. Lagos is on the Atlantic coast. | Birnin Lagos kilomita dari daya ne daga Ibadan. Lagos na kan Atalantika ne. | Lagos est à cent kilomètres d'Ibadan. Lagos se trouve sur la côte atlantique. |
According to the 2010 census, the population is twenty million. | Bisa ga kidayar jama'a a shekarar 2010, jimillar mutane miliyan ashirin ne. | D'après le recensement de 2010, la population est de vingt millions d'habitants. |
According to the 2015 estimate, the population is twenty-one million. | Bisa ga kimanta a shekarar 2015, jimilar mutane miliyan ashirin da ɗaya. | D'après l'estimation de 2015, la population est de vingt-et-un millions d'habitants. |
Since his election in 2014, Anne Hidalgo has been the mayor of Paris. | Anne Hidalgo ce, shugaban Paris, daga zabenta a shekarar 2014 (ko: Anne Hidalgo, ita ce shugaban Paris, daga zabenta a shekarar 2014). | Depuis son élection en 2014, Anne Hidalgo est la maire de Paris. |
Since his election in 2016, Sadiq Khan has been the mayor of London. | Sadiq Khan ne, shugaban London, daga zabensa a shekarar 2016 (ko: Sadiq Khan, shi ne shugaban London, daga zabensa a shekarar 2016). | Depuis son élection en 2016, Sadiq Khan est le maire de Londres. |
The main economic activities are trade/industry/administration/banking/tourism/services. | Muhimman ayyukan tattalin arziki, su ne kasuwanci/masana'antu/gwamnati/ajiya/shagali/ayyuka. | Les principales activités économiques sont le commerce/l'industrie/l'administration/les activités bancaires/le tourisme/les services. |
***, *** and *** are (famous) people) from Jos. | ***, *** da *** su ne (sannannu, ko shahararrun mutanen) daga birnin Jos. | ***, *** et *** sont des personnes (célèbres) originaires de Jos. |
Countries | Ƙasashe | Pays |
China is a country in Asia. | China/Cina, kasa ne, da ke a nahiyar Asiya. | La Chine est un pays situé en Asie. |
Spain is a country in Europe. | Spain, kasa ne, da ke a nahiyar Turai. | L'Espagne est un pays situé en Europe. |
Algeria is a country in Africa. | Aljeriya, kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. | L'Algérie est un pays situé en Afrique. |
Brazil is a country in South America. | Brazil, kasa ne, da ke a nahiyar Amurka ta Kudu. | Le Brésil est un pays situé en Amérique du Sud. |
Canada is a country in North America. | Kanada, kasa ce, da ke a nahiyar Amurka ta Arewa. | Le Canada est un pays situé en Amérique du Nord. |
Canada has a border with the United States to the South. | Kanada yana da iyaka da Amurka a Kudu. | Au sud, le Canada a une frontière avec les États-Unis. |
Nigeria has borders with Benin to the South, Niger to the North, Chad to the North-East, and Cameroon to the East. | Najeriya tana da iyaka da Benin ta bangaren Yamma, da Nijar ta bangaren Arewa, da Cadi ta bangaren Arewa maso Gabas, kuma da Kameru ta bangaren Gabas. | Le Nigeria a des frontières avec le Bénin à l'ouest, le Niger au nord, le Tchad au nord-est et le Cameroun à l'est. |
Italy has an area of 301,338 square kilometers. | Italiya tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 301,338. | L'Italie a une superficie de 301 338 kilomètres carrés. |
According to the 2017 estimate, Ethiopia has a population of 102,374,044. | Habasha tana da yawan jama'a 102,374,044, bisa ga kimanta a shekarar 2017. | D'après l'estimation de 2017, l'Éthiopie a une population de 102 374 044 personnes. |
The capital of Nigeria is Abuja. | Babban birnin Najeriya, Abuja ne. | La capitale du Nigeria est Abuja. |
Nigeria got its independence in 1960. | Najeriya ta samu yancin kanta a shekarar 1960. | Le Nigeria a pris son indépendance en 1960. |
The official language of Nigeria is English. The national languages of Nigeria are Hausa, Yoruba and Igbo. | Harshen ma'aikatan Najeriya Turanci ne. Harsunan kasar Najeriya su ne, Hausa, Yoruba da Igbo (or : Harsunan kasar Najeriya sun hada da, Hausa, Yoruba da Igbo). | La langue officielle du Nigeria est l'anglais. Les langues nationales du Nigeria sont le haoussa, le yoruba et l'igbo. |
About 50% of Nigerians are Christian, while 50% are Muslim. | Kusan hamsin cikin dari mutanen Najeriya Kirista ne, sa'anan hamsin cikin dari Musulmi ne. | Environ 50 % des Nigérians sont chrétiens, tandis que 50 % sont musulmans. |
***, *** and *** are famous Nigerians. | ***, *** da ***, su ne sannannun (ko shahararrun mutanen) Najeriya. | ***, *** et *** sont des Nigérians célèbres. |
People | Mutane | Personnalités |
P-Square is a singer. | P-Square mawaki ne. | P-Square est un chanteur. |
Fati Niger is famous for her song Girma girma. | Fati Niger sannaniya ce ta wakarta Girma girma. | Fati Niger est célèbre pour sa chanson Girma girma. |
Leonardo da Vinci is a painter. | Leonardo da Vinci mai fenti ne. | Léonard de Vinci est un peintre. |
Chimamanda Ngozi Adichie is a writer. | Chimamanda Ngozi Adichie marubuciya ce. | Chimamanda Ngozi Adichie est une écrivaine. |
Abubakar Adam Ibrahim is famous for his book Season of Crimson Blossoms. | Abubakar Adam Ibrahim shaharre ne ta littafinsa Lokacin jajayen furani. | Abubakar Adam Ibrahim est célèbre pour son livre Season of Crimson Blossoms. |
Atiku Abubakar is a politician. | Atiku Abubakar ɗan siyasa ne. | Atiku Abubakar est un homme politique. |
Sanusi Lamido Sanudi is a traditional leader. | Sanusi Lamido Sanusi ɗan sarauta ne. | Sanusi Lamido Sanudi est un chef traditionnel. |
Ken Saro-Wiwa is an activist. | Ken Saro-Wiwa ɗan muhimman aiki ne. | Ken Saro-Wiwa est un activiste. |
Tukur Buratai is a general. | Tukur Buratai janaral ne. | Tukur Buratai est un général. |
Ayo Oritsejafor is a Christian religious leader. | Ayo Oritsejafor shugaban addinin Kirista ne. | Ayo Oritsejafor est un chef spirituel chrétien. |
Muhammad Sani Yahya Jingir is a Muslim religious leader. | Muhammad Sani Yahya Jingir shugaban addinin Musulunci ne. | Muhammad Sani Yahya Jingir est un chef spirituel musulman. |
Wole Soyinka is a professor. | Wole Soyinka ferfesa ne. | Wole Soyinka est un professeur d'université. |
Aliko Dangote is a businessman. Folorunso Alakija is a businesswoman. | Aliko Dangote ɗan kasuwa ne. Folorunso Alakija 'yar kasuwa ce. | Aliko Dangote est un homme d'affaires. Folornso Alakija est une femme d'affaires. |
Cristiano Ronaldo is a football player. Blessing Okagbare is an athlete. | Cristiano Ronaldo ɗan wasan kwallon qafa ne. Blessing Okagbare magujiya ce. | Cristiano Ronaldo est un joueur de football. Blessing Okagbare est une athlète. |
Sanya Dojo Onabamiro is a researcher. | Sanya Dojo Onabamiro mai bincike ne. | Sanya Dojo Onabamiro est un chercheur. |
Chike Obi is a mathematician. | Chike Obi ɗan lissafi ne. | Chike Obi est un mathématicien. |
Jacob Festus Adeniyi Ajayi is a historian. | Jacob Festus Adeniyi Ajayi ɗan tarihi ne. | Jacob Festus Adeniyi Ajayi est un historien. |
Philip Emeagwali is a computer scientist. | Philip Emeagwali masanin kimiyyar na'ura mai kwakwalwa ne. | Philip Emeagwali est un informaticien. |
Mungo Park is an explorer. | Mungo Park matafiyi ne. | Mungo Park est un explorateur. |
Blessing Okagbare was born on October 9, 1988. | An haife Blessing Okagbare tara ga watan Oktoba a shekara ta 1988. | Blessing Okagbare est née le 9 octobre 1988. |
Aliko Dangote was born on April 10, 1957. | An haifi Aliko Dangote goma ga watan afrilu, shekara 1957 (or: An haife, Aliko Dangote, ran goma ga Afrilu, shekara 1957). | Aliko Dangote est né le 10 avril 1957. |
Politics | Siyasa | Vie politique |
Goodluck Jonathan was president of Nigeria from 2010 to 2015. | Goodluck Jonathan ya zama shugaban ƙasar Najeriya daga shekara ta 2010 zuwa 2015. | Goodluck Jonathan a été président du Nigeria de 2010 à 2015. |
Ngozi Okonjo-Iweala was minister of Finance of Nigeria from 2003 to 2006 and from 2011 to 2015. | Ngozi Okonjo-Iweala, ta yi ministan Ƙudi a Najeriya daga shekara 2003 zuwa 2006 kuma daga 2011 zuwa 2015. | Ngozi Okonjo-Iweala a été ministre des Finances du Nigeria de 2003 à 2006 et de 2011 à 2015. |
Rabiu Kwankwaso was minister of Defense from 2003 to 2007 and governor of Kano State from 1999 to 2003 and from 2011 to 2015. | Rabiu Kwankwaso, ya yi ministan Tsaro na Najeriya daga shekara 2003 zuwa 2007. Ya yi gwamnan jihar Kano daga shekara 2003 zuwa 2007, ya sake yi a shekara 2011 zuwa 2015. | Rabiu Kwankwaso a été ministre de la Défense de 2003 à 2007 et gouverneur de l'État de Kano de 1999 à 2003 et de 2011 à 2015. |
Yemi Osinbajo became Vice-President of Nigeria in 2015. | Yemi Osinbajo ya zama mataimakin shugaban ƙasar Najeriya a shekara ta 2015. | Yemi Osinbajo est devenu vice-président du Nigeria en 2015. |
Johnson Aguiyi-Ironsi was killed in 1967. | An kashe Johnson Aguiyi-Ironsi a shekarar 1967. | Johnson Aguiyi-Ironsi a été assassiné en 1967. |
Sports | Wasanni | Sport |
In 2014, the Germany national football team won the World Cup. | A shekarar 2014, 'yan wasan kwallon Jamus sun ci wasan Gasar wasan kwallo na duniya. | En 2014, l'équipe d'Allemagne de football a remporté la Coupe du monde. |
Neymar has played for FC Barcelona from 2013 to 2017. In 2017 he moved to Paris Saint-Germain. | Neymar ya buga wasan kwallo ma Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona daga shekara 2013 zuwa 2017. A shekara 2017 ya tafi Kungiyar kwallon kafa ta Paris. | Neymar a joué au FC Barcelone de 2013 à 2017. En 2017, il a été transféré au Paris Saint-Germain. |
Academic life | Jami'a | Enseignement et recherche |
In 2016, she received the Nobel Prize for Literature/Peace/Medicine / the Fields Medal / the Bank of Sweden Prize in Economic Sciences. | A shekara ta 2016, ta ƙarba kyautar Nobel ta adabi/zaman lafiya/magani / kyautar Fields / kyautar Bankin Swidi ta tattalin arziki. | En 2016, elle a reçu le prix Nobel de littérature/de la paix/de médecine / la médaille Fields / le prix de la Banque de Suède en sciences économiques. |
Bayero University Kano is a university situated in Kano, Kano State, Nigeria. It was founded in 1977. It has 37,747 students. The Vice Chancellor is Muhammad Yahuza Bello. | Jami'ar Bayero Kano, tana a Kano (jihar Kano, Najeriya). An kafa ta a shekara ta 1977. Tana da dalibai 37,747. Shugaban jami'ar Muhammad Yahuza Bello ne. | L'université Bayero est située à Kano, dans l'État de Kano, au Nigéria. Elle a été fondée en 1977. Elle compte 37 747 étudiants. Le vice-chancelier est Muhammad Yahuza Bello. |
It has faculties of Health Sciences, Agriculture, Arts & Islamic Studies, Clinical Sciences, Education, Engineering, Law, Science, Earth and Environmental Studies, Pharmacy, Social Management Science and Computer Science & Information Technology. | Tana da tsangayoyi na Kimiyyar Lafiyan Jiki, Noma, Adabi da Ilmin Islamiyya, Kimiyyar Asibiti, Ilmi, Injiniya, Doka, Kimiyya, Kimiyyar Duniya da Muhalli, Kantin Magani, Kimiyyar Zaman Jama'a kuma Kimiyyar Na'ura mai Kwakwalwa da Fasahar Labarai. | Elle a des facultés de sciences de la santé, agriculture, arts et études islamiques, sciences médicales, éducation, ingénierie, droit, science, études environnementales, pharmacie, gestion et informatique. |
Geography | Ilimin duniya | Géographie |
The Niger River is 4,180 km long. Its basin is 2,117,700 km2 in area. Its average flow is 5,589 m3/s, varying from 500 m3/s to 27,600 m3/s. Its source is in the Guinea Highlands, in southeastern Guinea. Its main tributary are the Bani River, the Sokoto River, the Kaduna River and the Benue River. It runs through Mali, Niger and to Nigeria, discharging into the Atlantic Ocean through the Niger Delta. The cities of Tembakounda, Bamako, Timbuktu, Niamey, Lokoja and Onitsha are located on the banks of the Niger River. | Kogin Neja na da tsawon kilomita 4,180. Zurfinta marubba’in kilomita 2,117,700 a kasa. Matsakaicin saurinta 5,589 m3/s wanda ya bambanta daga saurin 500 m3/s zuwa 27,600 m3/s. Mafarinta daga tsaunukan Guinea, a kudu maso gabashin Guinea. Kananan rafufukanta su ne Rafin Bani, Rafin Sakkwato, Rafin Kaduna da na Benuwe. Ta bi cikin Mali, Nijer da Najeriya zuwa Tekun Atalanta wanda ta bi Neja Delta. Waxannan biranen na samuwa a gefen kogin Neja; Tembakounda, Bamako, Timbuktu, Niamey. | Le fleuve Niger est long de 4 180 kilomètres. Son bassin mesure 2,117,700 km2. Son débit moyen est de 5,589 m3/s, variant de 500 m3/s à 27,600 m3/s. Il prend sa source dans les monts Loma, en Guinée. Ses principaux affluents sont les rivières Bani, Sokoto, Kaduna et Bénoué. Il traverse le Mali, le Niger et le Nigeria, se jetant dans l'océan Atlantique en formant le delta du Niger. Les villes de Tambacounda, Bamako, Tombouctou, Niamey, Lokoja et Onitsha sont situées sur les rives du Niger. |
Mount Idoukal-n-Taghès, also named Mount Bagzane, is a mountain located in the Aïr Mountains, in Niger. It is the highest mountain in Niger. It is 2,022 meters high. | Dutsen Idoukal-n-Taghes, wanda wanda yana da lakabin Dutsen Bakzani, Dutse ne wanda na samuwa a sararin Neja. Dutsen ne mafi tsawo a Neja. Tsawonta mita 2,022. | Le mont Idoukal-n-Taghèse, aussi appelé mont Bagzane, est un sommet situé dans le massif de l'Aïr. C'est le plus haut sommet du Niger. Son altitude est de 2 022 mètres. |
Corsica is an island in the Mediterrean Sea. It is part of France. It is located south east of the French mainland and west of the Italian Peninsula. Its area is 8,680 km2 and its population is 330,000. | Corsica tsibiri ne da ke a Tequn Yammanci. Bangaren Faransa ne. Tana samuwa a kudu maso gabas a ainihin vangaren Farasanci a kuma yammancin Tekun Italiya. Tana da filin marubba’in kilomita 8,680 da yawan mutane 330,000. | La Corse est une île située dans la mer Méditerranée. Elle fait partie de la France. Elle est située au Sud-Est de la partie continentale de la France et à l'ouest de la péninsule italienne. Sa superficie est de 8 690 km2 et sa population de 330 000 habitants. |
The Bab-el-Mandeb is a strait located between Yemen on the Arabian Peninsula, and Djibouti and Eritrea in the Horn of Africa. It connects the Red Sea to the Gulf of Aden. The distance across is about 20 miles (30 km) from Ras Menheli in Yemen to Ras Siyyan in Djibouti. | Bab-el-Mandeb mashigin teku wanda ta ke tsakanin Yemen a tequn Arabiya, da Djiibouti da Eritrea cikin Kakakin Afirka. Ya haxa Jan Teku da mashigar ruwar Aden. Nisan ketere ya kusan mil 20 (kilomita 30) daga Ras Menheli a Yemen zuwa Ras Siyysn a Djibouti. | Le détroit de Bab-el-Mandeb est situé entre le Yémen, dans la péninsule arabique, et Djibouti et l'Érythrée, dans le Corne de l'Afrique. Il relie la mer Rouge au golfe d'Aden. Sa largeur est de 30 kilomètres du Ras Menheli, au Yémen, au Ras Siyyan, à Djibouti. |