Wizkid
Wizkid | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Ayodeji Ibrahim Balogun |
Haihuwa | Lagos, 16 ga Yuli, 1990 (34 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Yarbawa |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Jihar Lagos |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi, mai rubuta waka da mawaƙi |
Tsayi | 5 ft |
Kyaututtuka | |
Artistic movement | Afrobeats |
Kayan kida | murya |
Jadawalin Kiɗa |
RCA Records (mul) Starboy Entertainment |
Imani | |
Addini | Katolika |
mercuryhd.com… |
ayodeji ibrahim balogun(a
An haife shi a ranar 16 ga watan Yuli shekara ta( 1990 )a garin Surulere dake Jihar Lagos a Nijeriya.[1] Anfi saninsa da shahararran sunansa wato Wizkid. Mawakin Nigeriya ne kuma marubucin wakoki ne . Yafara rera waka tun yana da shekara goma sha daya,(11) sannan yayi kokarin fitar da albam tareda Glorious Five, wata kungiya ce dashi da wasu abokansa a coci suka samar da ita. A shekara ta (2009), ya kulla wata yarjejeniya dashi da Banky W.'s record label Empire Mates Entertainment (E.M.E). Yakaiga shahara a shekara ta (2010 )tareda fitar da wakar "Holla at Your Boy" daga cikin albam din daya fara fitar wa a studiyo dinsa, Superstar (2011). "Tease Me/Bad Guys", "Don't Dull", "Love My Baby", "Pakurumo" da "Oluwa Lo Ni" dukkanin su suma yafitar dasu daga cikin albam dinsa na Superstar. Albam din studiyon Wizkid na biyu, Ayo, yafitar da ita a watan September a shekara ta( 2014) wadanda wakoki shida sukazo kafinta: "Jaiye Jaiye", "On Top Your Matter", "One Question", "Joy", "Bombay" da "Show You the Money".
A shekara ta( 2016 ), Wizkid yasamu sanayya a kasashen duniya bayan tarayyarsa tareda Drake on the global hit, "One Dance", wanda yakaiga zama na daya a kasashe( 15 ), wanda yahada da United States, United Kingdom, Canada and Australia. Kari akan ayyukan wakokinsa daya gudanar shi kadai, kuma Wizkid yayi tarayya da wasu mawaka da dama kuma yafito acikin wakar "Girl" (tareda Bracket), "Fine Lady" (tareda Lynxxx), "Sexy Mama" (tareda Iyanya), "Slow Down" (tareda R2Bees), "The Matter" (tareda Maleek Berry), "Pull Over" (tareda KCee) da kuma "Bad Girl" (tareda Jesse Jagz).'[2]
Bayan fitowar albam dinsa nabiyu da karewar kwantaraginsa dayayi na shekara 5, Wizkid yabar E.M.E. a( 1 ) ga watan Maris shekara ta( 2017 ), Billboard magazine tayi rehoton Wizkid yakulla yarjejeniya na fitarda albobi tareda RCA Records.[3] bayanin yarjejeniyar yafito daga jaridu da dama tun a watan September a shekara ta( 2016 ).[4] Shugaba kuma CEO na RCA Records, Peter Edge, ya tabbatar da yarjejeniyar yayin dayake jawabi da Music Business Worldwide a watan January a shekara ta (2017 ).[5]
Ansa shi a matsayi na 5th a Forbes da Channel O acikin jerin masu kudin mawakan Afirka( 10 )na shekara ta ( 2013 ).[6][7] A watan Fabrairu na shekara ta( 2014 ), Wizkid yazama mawakin Nigeriya na farko dayake da mabiya sama da miliyan daya a shafin Twitter.[8][9] haka kuma, yazama mawakin Afirka nafarko daya kasance a shekara ta( 2018 ) acikin Guinness World Records akan gudunmuwarsa a cikin wakar Drake "One Dance".[10][11]
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Wizkid
-
lakanin wizkid
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Wizkid pops N300m champagne at 23rd birthday bash?". Punch Nigeria. Archived from the original on 29 October 2013. Retrieved 9 October 2013. Unknown parameter
|deadurl=
ignored (|url-status=
suggested) (help) - ↑ "Wizkid". 2021-05-21. Archived from the original on 2021-05-21.
- ↑ Adelle Platon (1 March 2017). "WizKid Signs Multi-Album Deal With RCA Records/Sony Music International: Exclusive". Billboard. Retrieved 11 March 2017.
- ↑ "Wizkid Signs Record Breaking Deal With Sony Music/RCA". Okay Africa. 9 September 2016. Retrieved 4 February 2017.
- ↑ "Sony Battles Online Leak of Wizkid/Drake's One Dance Follow-Up". Music Business Worldwide. 18 January 2017. Retrieved 4 February 2017.
- ↑ "Wizkid richer than 2Face, Banky W – Forbes". The City Reporters. 2 September 2013. Retrieved 15 December 2013.
- ↑ "Sarkodie Makes Forbes Top 10 Richest Africa Artistes". The Chronicle. 3 September 2013. Retrieved 15 December 2013.
- ↑ "Wizkid- First Nigerian Artiste To Hit A Million Twitter Followers". Modern Ghana. 20 February 2014. Retrieved 5 March 2014.
- ↑ "Guess Which Nigerian Artiste Becomes The First To Gain 1 Million Followers on Twitter". Naij News. 20 February 2014. Retrieved 5 March 2014.
- ↑ Durosomo, Damola (22 September 2017). "Wizkid Is Named In the 2018 Guinness Book of World Records". OkayAfrica. Retrieved 22 October 2017.
- ↑ "Wizkid enters Guinness World Book of Records 2018 - Vanguard News". vanguardngr.com. 22 September 2017. Retrieved 27 September 2017.