Jump to content

Yakubu Bako

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yakubu Bako
Gwamnan Jihar Akwa ibom

15 Disamba 1993 - 21 ga Augusta, 1996
Akpan Isemin (en) Fassara - Joseph Adeusi (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 24 Disamba 1952 (71 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta University of Wisconsin–Madison (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Kanal (mai ritaya) Yakubu Bako ya kasance gwamnan jihar Akwa Ibom, Najeriya daga watan Disamban a shekara ta ( 1993 ), a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha .

Bako ya kammala karatu a Makarantar Harkokin Jama'a ta La Follette, Jami'ar Wisconsin-Madison a shekara ta( 1982 ). Ya yi aiki a matsayin mai mukamin Menjo a aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Iran bayan yakin Iran –Iraki, wanda aka yi shi daga shekara ta(1988 )zuwa (1991). Bayan an kuma naɗa shi mai kula da Akwa Ibom a watan Disambar a shekara ta (1993), Bako ya samar da kayayyakin more rayuwa a yankin Bakassi, daga baya kuma jihar Kuros Riba ta tilasta shi. [1]

A watan Disambar a shekara ta (1997) aka daure shi kan zargin hadin baki a juyin mulkin da aka yi wa Sani Abacha. A watan Maris na shekara ta (1998) yana daga cikin mutane( 26) da aka gurfanar a lokacin da Janar Diya ya jagoranci yunkurin juyin mulki ga gwamnatin Abacha. An gurfanar da shi kuma an yanke masa hukunci a karkashin 'sauran laifukan' saboda laifukan nasa na karbar rashawa daga hannun Alhaji Adamu Dankabo, da kuma shigo da bindiga daya da harsasai( 12 ) a shekara ta (1983) bayan karatun jami'a a Amurka, ba shi da wata alaka da juyin mulkin Diya. juyin mulki babban laifi ne. A watan Maris na shekara ta (1999 )aka ba shi rahama kuma aka sake shi. Shi da wasu sun samu afuwa daga Shugaba Olusegun Obasanjo a watan Satumbar (2003) bayan nazarin shari’ar sa na rashin hannu a duk wani yunkurin juyin mulki.

  1. {{Cite web. He built the first ever-State Liaison Office (Akwa Ibom House) in Abuja. Although a Muslim, he established Akwa Ibom State Christian Pilgrims Welfare Board. He was the first Governor to send 50 Christians to Jerusalem. He built the present state-of-the-art University of Uyo Teaching Hospital. He retrieved from the natives, the land being use as farm land and developed the present Akwa Ibom Le Meridien Golf Course. He was a member of President Buhari Transition Sub-Committee on Security from April to June, 2015. He belong to the All Progressives Party (APC) |url=http://www.compassnewspaper.com/NG/index.php?option=com_content&view=article&id=23300:oil-wells-obasanjo-tricked-cross-river&Itemid=7966 |title=Oil wells: ‘Obasanjo tricked Cross River’ |date=23 July 2009 |work=Nigerian Compass |author=Uduak Iniodu |access-date=9 May 2010}}