Zakir Naik
Zakir Naik | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Mumbai, 18 Oktoba 1965 (58 shekaru) |
ƙasa |
Indiya Saudi Arebiya |
Mazauni | Maleziya |
Karatu | |
Makaranta |
Kishinchand Chellaram College (en) Topiwala National Medical College and BYL Nair Hospital (en) University of Mumbai (en) |
Harsuna |
Turanci Harshen Hindu Indonesian (en) Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | likita, marubuci, intellectual (en) , Mai da'awa, likitan fiɗa, docent (en) , motivational speaker (en) , orator (en) da mai yada shiri ta murya a yanar gizo |
Muhimman ayyuka | Zakir Naik (en) |
Kyaututtuka |
gani
|
Imani | |
Addini | Musulunci |
zakirnaik.com |
Dr Zakir Abdul Karim Naik (an haife shi 18 ga watan Oktoba, shekara ta 1965) ɗan ƙasar Indiya ne kuma mai wa'azi na addinin Musulunci,[1] shine ya assasa kuma shugaban cibiyar Islamic Research Foundation (IRF).[2] Kuma shi ya kafa tashar talabijin ta Peace TV.[3] Lakcocin sa sun samu karɓuwa sosai, musamman a tsakanin Musulmai a nahiyoyi daban-daban. Ya samu kyautar sarki Faisal na Saudiyya ta ƙasa da ƙasa wadda yake bayarwa King Faisal International Prize a shekara ta 2015.[4][5] Ya tashi daga Indiya a shekara ta 2016.[6] Saboda gwamnatin Indiya ta zarge shi cewa maganganunsa na tada ƙayar baya a tsakanin jama'a, sai kuma suna zargin shi da almundahanar kuɗi. Sai dai duk waɗannan zarge-zargen da tuhume-tuhumen da suke masa sun kasa bada ƙwaƙƙwarar hujja wannan shine dalilin da yasa wasu suke ganin bai rasa nasaba da yadda gwamnatin ƙasar take takurawa musulmai musamman a yankin da aka rinjaye su. A ƙarshe har yunkurin ƙwace muhallai da dukiyarsa da suke a ƙasar dake indiya sukai, sai dai sun samu cikas saboda kotu ta hana gwamnatin ƙasar yin haka saboda rashin dalilin zargin.[7]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Zakir Naik ya halarci makarantu da dama inda ya samu shaidar zama kwararran likita wato "Bachelor of Medicine and Surgery".
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Shukla, Ashutosh. "Muslim group welcomes ban on preacher". Daily News and Analysis. 22 June 2010. Retrieved 16 April 2011. Archived 7 August 2011 at WebCite 7 August 2011.
- ↑ "Dr. Zakir Naik". Islamic Research Foundation. Retrieved 16 April 2011. Archived 6 January 2010 at the Wayback Machine.
- ↑ RASHID (21 July 2013). "Peace TV network crosses 200 million viewership". Arab News. Retrieved 18 January 2018.
- ↑ "Indian Islamic scholar Zakir Naik receives Saudi prize for service to Islam". dna. 2 March 2015.
- ↑ "10 Times Zakir Naik Proved That He Promoted Anything But Peace". HuffPost India (in Turanci). 2016-07-07. Retrieved 2020-10-23.
- ↑ "India formally requests Malaysia to extradite fugitive Islamic preacher Zakir Naik". www.timesnownews.com (in Turanci). Retrieved 2020-10-23.
- ↑ "Tribunal Restrains Enforcement Directorate From Taking Over Zakir Naik's Assets" (in Turanci). NDTV.COM. 10 January 2018. Retrieved 27 November 2022.