Zaynab an-Nafzawiyyah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zaynab an-Nafzawiyyah
Rayuwa
Haihuwa Aghmat (en) Fassara, 1039
Harshen uwa Abzinanci
Mutuwa 1117
Ƴan uwa
Abokiyar zama Abu Bakr ibn Umar (en) Fassara
Yara
Karatu
Harsuna Abzinanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Zaynab an-Nafwiyzāyah (Larabci , a harshen Tamazight: Zinb Tanefzawt) (d. 1072), [1] mace ce mai karfin iko daga Berber a farkon kwanakin Masarautar Berber wadda ta samu iko a yankunan kasashen Maroko, yammacin Aljeriya, Mauritania da Al-Andalus na yau. [2]

Ta auri Yusuf ibn Tashfin (r. 1061-1107) kuma an sanar cewa shi ne sarkin garin. Ta kasance ɗaya daga cikin matan Sarakuna Berber da aka ba ta taken malika (Sarauniya), wanda ba matsayi bane da aka fiye ba wa matan sarakunan Musulmi ba, kuma ana kiranta al-qa'ima bi mulkihi (ma’ana: wanda ke kula da mulkin mijinta'), yana nufin sa hannu a cikin al'amuran jihar a lokacin mulkin mijinta. [3] Kodayake ba a taɓa ba da khutba a cikin sunanta ba, an san ta da raba ikon mijinta.[1][3]

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Nazari na farko game da ita na nan a rubuce a boye acikin rubutu na karni na 12 Kitab al-Istibsar, inda ya ce "A lokacinta babu wata da ta fi ta kyawu ko basira ko hangen nesa ... ta auri Yusuf, wanda ya gina mata Marrakech".[4] Wannan aikin ya sanya wa mahaifinta suna Ibrāhīm an-Nafzāwi, ɗan kasuwa ne daga Kairouan.[5]

A cewar Ibn Khaldun, da farko ita ƙwaraƙwarar Yusuf ibn Ali ce, shugaban ƙabilun Wurika da Aylana Berber tare da Aghmat a Maroko. Daga nan sai ta auri Luqūt al-Maghrāwi, Sarkin Aghmat . A shekara ta 1058, an kashe Luqūt a Tadla a yaƙi da Almoravids mahara kuma Zaynab, mai takabarsa ta gaji dukiyarsa.

Bayanan da suka fi cika sun bayyana a cikin (abin takaici ba kammala ba) rubutun farkon karni na 14 Al-bayan al-mughrib . An ce ta samu tayin aure da yawa daga shugabannin kabilun daga ko'ina cikin Morocco, amma koyaushe ta ƙi ta hanyar cewa ba za ta auri wanda ba ya son zama mai mulkin duk ƙasar ba. An ce tana da karfin iko na musamman, kuma ta magana a cikin hikima.

Ta auri Sarkin Almoravid, Abu-Bakr Ibn-Umar a watan Satumba na shekara ta 1068 kuma ta ba da gudummawarta da dukiyarta mai yawa a gare shi. An ce ta rufe idanu Abu Bakr, sannan ta kai shi wani kogo na sirri. Lokacin da ta bude masa ido, sai ya ga dukiyar zinariya da azurfa mai tarin yawa, lu'ulu'u da rubies kewaye da shi. "Duk wannan naka ne" ta ce kafin ta fitar da shi - kuma an sake rufe masa idanu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. (Henry Louis ed.). Missing or empty |title= (help)
  2. Lebbady, Hasna; Hilali, Hiam El (2020). "al-Nafzaouiya, Zaynab". Oxford Research Encyclopedia of African History (in Turanci). doi:10.1093/acrefore/9780190277734.013.467. ISBN 9780190277734. Retrieved 2021-05-19.
  3. 3.0 3.1 Mernissi, Fatima; Mary Jo Lakeland (2003).
  4. ref. Corpus below.
  5. As also Al-bayan al-mughrib.