Jump to content

Abdullahi bin Uthman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdullahi bin Uthman
Rayuwa
Haihuwa Masarautar Aksum, 620
Mutuwa Madinah, Disamba 625 (Gregorian)
Makwanci Al-Baqi'
Ƴan uwa
Mahaifi Sayyadina Usman dan Affan
Mahaifiya Rukayyah
Ƴan uwa
Sana'a
Imani
Addini Musulunci
tbatin sunan abdullah

Abd Allah bn Uthman (Larabci: عبد الله ابن عثمانc. An haife shi a shekara ta 620 zuwa Nuwamba 625), ya kasance ɗan khalifa na uku Usman (r. 644-656) da Ruqayya bint Muhammad. An haife shi a Abyssinia, Abd Allah shine jikan Annabin Musulunci Muhammad na farko.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekara ta 615 Ruqayya ta auri wani fitaccen musulmi, Uthman ibn Affan. Ta yi masa rakiya a Hijira ta farko zuwa Abyssinia, [1] [2] [3] inda ta yi fama da zubar ciki. Sun koma Abyssiniya a shekara ta 616, [4] [2] [3] a nan Ruqayya ta haifi da, Abdallah a shekara ta 619.

Iyayensa, Uthman da Ruqayya suna daga cikin wadanda suka dawo Makka a shekara ta 619. [5] Uthman ya yi hijira zuwa Madina a shekara ta 622, kuma Ruqayya ta bi shi daga baya. [2] [3]

Muhammad ya tambayi Usama, shin ka taba ganin kyawawan ma'aurata fiye da wadancan biyun? kuma ya yarda cewa bai taɓa ba. [6]

Mus'ab al-Zubayri ya ruwaito cewa a lokacin da Uthman ya yi hijira zuwa kasar Abisiniya, yana tare da matarsa Ruqayya bint Muhammad . An haifi wani yaro mai suna Abd Allah a kasar Abisiniya a shekara ta 2 kafin Hijira. [7]

Mahaifiyarsa, Ruqayya tayi rashin lafiya a watan Mayu shekara ta 624. Uthman ya samu uzuri daga aikin soja domin ya kula da ita. Ta rasu a cikin watan, a ranar da Zaidu bn Haris ya koma Madina da labarin nasarar da suka samu a yakin Badar. Lokacin da kakansa Muhammad ya dawo Madina bayan yakin, dangi sun tafi suna baƙin ciki a kabarin ta.

Abd Allah ya rasu bayan zakara ya cizan masa ido a watan Nuwamba shekara ta 625 ( Jumada al-Thani 4 AH) yana ɗan shekara shida. [8] Muhammad ya jagoranci sallar jana'izarsa. [9] Abd Allah ya rasu a Madina. Shi kadai ne yaron Ruqayya. [2] [3]

  1. Ibn Ishaq/Guillaume pp. 146, 314.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 Ibn Saad/Bewley p. 25.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 Tabari/Landau-Tasseron p. 162.
  4. Ibn Ishaq/Guillaume p. 146.
  5. Ibn Ishaq/Guillaume p. 168.
  6. Jalal al-Din al-Suyuti. Tarikh al-Khulafa. Translated by Jarrett, H. S. (1881). History of the Caliphs, p. 155. Calcutta: The Asiatic Society.
  7. Usd al-ghabah fi marifat al-Saḥabah by Ali ibn al-Athir, Volume 2, Pg 571
  8. Madelung 1997.
  9. Kitab Tabaqat Al-Kubra by Ibn Sa'd Volume 2, Part 3, Pg.131