Jump to content

Ahmed Mumin Warfa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmed Mumin Warfa
Rayuwa
Haihuwa Mogadishu
ƙasa Somaliya
Mutuwa 24 ga Maris, 2021
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Koronavirus 2019)
Karatu
Makaranta Somali National University (en) Fassara
University of Florence (en) Fassara
Uppsala University (en) Fassara
Matakin karatu Digiri
master's degree (en) Fassara
Doctor of Philosophy (en) Fassara
Sana'a
Sana'a botanist (en) Fassara da university teacher (en) Fassara
Employers Somali National University (en) Fassara  1991)

Ahmed Mumin Warfa ( Somali </link> , Larabci: أحمد مومين وارفا‎ </link> ) wani masanin kimiyar ƙasar Somaliya ne wanda ya kware a fannin ilmin kimiyyar halittu, wanda tare da abokin aikinsa Mats Thulin suka gano Cyclamen somalense . Ya riƙe muƙamin shugaban (rector) na Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Zamzam daga shekarar 2020 har zuwa rasuwarsa.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Komawa Somalia

[gyara sashe | gyara masomin]

Warfa malami ne a jami'ar ƙasar Somaliya, inda ya koyar da ilimin halittu da aikin gona . Ya kuma gudanar da bincike akai-akai tare da abokan aikinsa a Somaliya, inda tare da Haɗin gwiwar gano nau'o'in halittu da dama, musamman a yankin Bari na arewa maso gabashin ƙasar.

Da barkewar yaƙin basasa a shekarar 1991 da kuma rufe jami'ar, Ahmed ya zama mai son zaman lafiya.  matsayin mai fassara ga Majalisar Ɗinkin Duniya da kafa majalisu don sulhuntawa a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha . Yunkurin nasa ya haifar masa da rikici da jagororin mayakan sa kai na yankin. A shekarar 1994, da kyar ya tsira daga yunkurin kisa.

Ahmed Mumin Warfa a wajen taro

Yaransa su ne Sumaya Mumin, Ismail Mumin, Daud Ahmed Mumin, Hibo Mumin, Farah Mumin, Mohamed Mumin, Aisha Mumin, Yusuf Mumin, Dahir Mumin, Halima Mumin, Fadumo Mumin, da Fadumo Mumin.

Daga bisani Warfa ya bar Somalia zuwa Nairobin Kenya, daga nan ya yi hijira zuwa Amurka, inda ya koyar da ilimin halittu a Kwalejin Al'umma ta Salt Lake da Jami'ar Brigham Young da ke Utah . Ya ci gaba da halartar taro kan ilimin tsiro a matsayin babban mai magana ko mai ba da gudummawa.

Har ila yau, Warfa ya taka rawa sosai a cikin harkokin Somaliya da na Somaliyawa, ko a matsayin mai sulhuntawa da ke aiki da Majalisar Dinkin Duniya da Shugaban Somaliya [1] ko kuma a matsayin mai fafutuka don tara kuɗaɗe don ayyuka kamar Jami'ar Hiiraan .

A cikin shekarar 2020, Warfa ya koma Mogadishu don zama shugaban jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Zamzam .

  1. The new Africa: dispatches from a changing continent By Robert M. Press pg 197