Aisha Dahiru Ahmad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aisha Dahiru Ahmad
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 -
Aisha Dahiru Ahmad - AMINU IYA ABBAS (en) Fassara
District: Adamawa Central
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: Yola North/Yola South/Girei
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
Rayuwa
Cikakken suna Aishatu Dahiru Ahmed
Haihuwa Kaduna, 11 ga Augusta, 1971 (52 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Southampton (en) Fassara
Jami'ar Jihar Nasarawa
Harsuna Turanci
Fillanci
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da injiniyan lantarki
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress

Aishatu Dahiru Ahmed, wacce aka fi sani da Binani, ‘yar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa. Tsohuwar Sanata ce data wakilci Adamawa ta tsakiya a majalisar wakilai ta tara a karkashin Tutar jam'iyyar APC.

Farkon Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Aisha a ranar 11 ga watan Agusta, shekara ta alif ɗar tara da sabain da  daya1971A.c. Ta taba zama ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a matsayin mamba a jam’iyyar People’s Democratic Party tsakanin 2011 zuwa 2015.

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Binani ta yi karatun firamare da sakandare a jihar Kaduna kafin ta wuce Jami’ar Southampton, inda ta samu digiri na uku a fannin Eleteical Engineering.[1]


AIki[gyara sashe | gyara masomin]

Binani ta kafa kamfanin Binani Nigeria Limited, kungiyar Binani Group of Companies da nufin bunkasa da inganta tattalin arzikin yankin Arewa maso Gabas.

SIYASA[gyara sashe | gyara masomin]

Ta shiga harkar siyasa ne a shekarar 2011 lokacin da aka zabe ta a matsayin ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya Daga jihar, Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Daga baya ta sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ta tsaya takarar Sanata inda ta lashe zaben kujerar a matsayin  sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya.
A matsayinta na yar majalisar dattijai, Binani ta yi aiki a matsayin shugabar kwamitin majalisar dattawa kan manufofin ci gaba mai dorewa (SDGs).

Takarar Gwamna[gyara sashe | gyara masomin]

Sanata Aisha Dahiru Ahmed Binani ta lashe tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Adamawa inda ta doke maza shida da kuma jiga-jigan siyasar Jihar Adamawa.

A zaben fidda gwanin dai, Binani ta samu kuri’u 430, wanda ya zama mafi rinjaye a zaben, inda ta doke Nuhu Ribadu, tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Action Congress kuma Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC na farko, wanda ya samu kuri’u 288.
Muhammadu Jibrilla Bindow, gwamna mai barin gado ya zo na uku da kuri’u 103, Abdurrazaq Namda ya zo na biyu da kuri’u 94 sai Wafari Theman da 39.
Wafarniyi Theman da Umar Mustapha Madawaki ne suka samu matsayi na biyar da shida a zaben fidda gwanin.[2]
A ranar 14 ga Oktoba, 2022, wata babbar kotun tarayya da ke Yola ta soke takarar Binani a matsayin yar  takarar gwamnan Jihar Adamawa ta jam’iyyar APC.

Hukuncin da kotun ta yanke, ta bayyana cewa babu dan takarar jam’iyyar APC a jihar a zaben 2023 amma ta ce masu kara da wadanda ake kara suna da damar daukaka kara kan hukuncin.[3] Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa.

Mista Fintiri ya lashe zaben cike gurbin da kuri'u 9,337.  Ya kayar da babbar abokiyar hamayyar sa, Aisha Dahiru, wanda aka fi sani da Binani, ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ta zo ta biyu a zaben da kuri’u 6,513.[4]

A babban zaben da aka gudanar da kuma zaben da aka sake Fintiri na Jam'iyyar PDP ya samu kuri’u 430,861 yayin da yar takarar APC ta samu kuri’u 398,788.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.shineyoureye.org/person/aishatu-dahiru-binnan
  2. https://dailytrust.com/seven-things-to-know-about-aisha-binani/
  3. https://www.bbc.com/pidgin/articles/czq3dg723ewo
  4. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/594019-updated-inec-declares-pdps-fintiri-winner-of-adamawa-governorship-election.html