Jump to content

Aisha Pamela Sadauki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aisha Pamela Sadauki
Gwamnan jahar Niger

1986 - Disamba 1987
Dabid Mark - Lawan Gwadabe
Rayuwa
Haihuwa Zaria, 12 ga Afirilu, 1949 (77 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Jami'ar Tsaron Nijeriya
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da minista

Aisha Pamela Sadauki 'yar siyasa ce a Najeriya wacce ta kasance kwamishina kuma mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna a lokacin mulkin soja na Abubakar Tanko Ayuba.[1]

An haifi Pamela Sadauki a shekarar 1945. Ta halarci makarantar mishan ta Katolika na St-Louis da ke Kano kuma ta sami digiri na farko a fannin Home Economics tare da digiri na biyu a fannin Nutrition daga Jami'ar Jihar Iowa a shekarar 1968.[2] An naɗa ta mataimakiyar gwamnan Jihar Kaduna a watan Agusta na shekarar 1990 a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida.[3] Sannan daga baya an naɗa ta Kwamishina a Jihar Kaduna, Ci gaban Al'umma, Matasa da Wasanni a shekarar 1988, Kwamishina a Ilimi a shekarar 1989 da Mataimakiyar Gwamnan Kaduna daga shekarar 1990 zuwa 1992.

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Aisha Pamela Sadauki ta auri tsohon ministan Najeriya David Ahmed Sadauki wanda ya rasu a shekara ta 2008.[4]

Kyaututtuka

[gyara sashe | gyara masomin]

Ƙungiyar Manoman Dabbobi ta Najeriya ta ba ta lambar yabo ta Medal of Honor a shekarar 1999. Ta sami lambar yabo ta National Honorary Medal of Officer of the Order of Nigeria (OON) a shekarar 2000.

  1. https://dailytrust.com/reminiscences-with-aisha-pamela-sadauki/
  2. https://dailytrust.com/reminiscences-with-aisha-pamela-sadauki/
  3. https://www.vanguardngr.com/2018/11/issues-from-the-muslim-muslim-strategy-in-kaduna/
  4. https://allafrica.com/stories/200806160628.html