Jump to content

Aisha Dahiru Ahmad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Aishatu Dahiru Ahmed)
Aisha Dahiru Ahmad
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 - 11 ga Yuni, 2023
Abdul-Aziz Nyako - Abbas Aminu Iya
District: Adamawa Central
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: Yola North/Yola South/Girei
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
Rayuwa
Cikakken suna Aishatu Dahiru Ahmed
Haihuwa Jahar Kaduna, 11 ga Augusta, 1971 (54 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Southampton (en) Fassara
Jami'ar Jihar Nasarawa
Harsuna Turanci
Fillanci
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da injiniyan lantarki
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress
Aishatu Binani

Aishatu Dahiru Ahmed, ( An haife ta a watan Augusta shekarata alif 1971) wacce aka fi sani da Binani, ‘yar siyasa ce kuma ‘yar kasuwa. Tsohuwar Sanata ce data wakilci Adamawa ta tsakiya a majalisar wakilai ta tarayya a ƙarƙashin Tutar jam'iyyar APC mai alamar tsintsiya. Sa'annan tayi takarar gwamna a shekarar 2023 ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC.

Farkon Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]
An haifi Aisha a ranar 11 ga watan Agusta, shekara ta alif ɗari tara da saba'in da  ɗaya 1971A.c. Ta taɓa zama ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a matsayin mamba a jam’iyyar People’s Democratic Party tsakanin shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.

Aisha Binani ta yi karatun firamare da sakandare a jihar Kaduna kafin ta wuce Jami’ar Southampton, inda ta samu digiri na uku a fannin Eleteical Engineering.[1]


Binani ta kafa kamfanin Binani Nigeria Limited, ƙungiyar Binani Group of Companies da nufin bunƙasa da inganta tattalin arziƙin yankin Arewa maso Gabasa a ƙasar Najeriya.

Ta shiga harkar siyasa ne a shekarar 2011 lokacin da aka zaɓe ta a matsayin ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya Daga jihar, Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Girei a a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Daga baya ta sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ta tsaya takarar Sanata inda ta lashe zaɓen kujerar a matsayin  sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya.
A matsayinta na yar majalisar dattijai, Binani ta yi aiki a matsayin shugabar kwamitin majalisar dattawa kan manufofin ci gaba mai dorewa (SDGs).[2]

Takarar Gwamna

[gyara sashe | gyara masomin]

Sanata Aisha Dahiru Ahmed Binani ta lashe tikitin takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Adamawa inda ta doke maza shida da kuma jiga-jigan siyasar Jihar Adamawa.

A zaɓen fidda gwanin dai, Binani ta samu kuri’u 430, wanda ya zama mafi rinjaye a zaɓen, inda ta doke Nuhu Ribadu,[3] tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Action Congress kuma Tsohon shugaban hukumar Yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC na farko, wanda ya samu ƙuri’u 288.
Muhammadu Jibrilla Bindow, gwamna mai barin gado ya zo na uku da ƙuri’u 103, Abdurrazaq Namda ya zo na biyu da ƙuri’u 94 sai Wafari Theman da 39.
Wafarniyi Theman da Umar Mustapha Madawaki ne suka samu matsayi na biyar da shida a zaɓen fidda gwanin.[4]
A ranar 14 ga Oktoban shekara ta 2022, wata babbar kotun tarayya da ke Yola ta soke takarar Binani a matsayin yar  takarar gwamnan Jihar Adamawa ta jam’iyyar APC.[5]

Hukuncin da kotun ta yanke, ta bayyana cewa babu Ɗan takarar jam’iyyar APC a jihar a zaɓen 2023 amma ta ce masu kara da waɗanda ake kara suna da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin.[6] Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa.

Mista Fintiri ya lashe zaɓen cike gurbin da ƙuri'u 9,337.  Ya kayar da babbar abokiyar hamayyar sa, Aisha Dahiru, wanda aka fi sani da Binani, ta jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ta zo ta biyu a zaɓen da ƙuri'’u 6,513.[7]

A babban zaɓen da aka gudanar da kuma zaɓen da aka sake Fintiri na Jam'iyyar PDP ya samu kuri’u 430,861 yayin da yar takarar APC ta samu kuri’u 398,788.

  1. https://www.shineyoureye.org/person/aishatu-dahiru-binnan
  2. https://hausa.leadership.ng/tikitin-tsayawa-takarar-aisha-binani-ya-karfafa-siyasar-matan-arewa/
  3. https://www.thecable.ng/history-as-aishatu-binani-beats-ribadu-bindow-to-adamawa-apc-guber-ticket/
  4. https://dailytrust.com/seven-things-to-know-about-aisha-binani/
  5. https://www.bbc.com/hausa/articles/cndrdjgegj8o
  6. https://www.bbc.com/pidgin/articles/czq3dg723ewo
  7. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/594019-updated-inec-declares-pdps-fintiri-winner-of-adamawa-governorship-election.html